BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Wace illa matakin INEC zai yi ga ADC?
''Tun daga lokacin da aka ga mutane suna tururuwa suna shiga wannan jam'iyya tamu ta ADC, hankalin gwamnatin Tinubu ya tashi, ta san cewa ƴan Najeriya ba za su bari ta tsallake shekarar 2027 ba...," in ji ADC.
Arsenal da Man City da PSG na neman Olmo, Salah zai koma Saudiyya
RB Leipzig ta sanya farashin Yan Diomande fam miliyan 87 , Saudiyya na ƙara matsa lamba kan Mohamed Salah, Everton na ƙara kwarin gwiwa kan Jack Grealish.
Yadda Boko Haram ta yi wa mutane 20 yankan rago a Borno
Ƙungiyar Boko Haram dai ta kwashe shekaru tana ƙaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Shin muna tunkarar yaƙin duniya na uku ne ko ana razana mu ne kawai?
A wata hira da BBC a watan Fabrairu, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce ya yi amanna cewa shugaban Rasha Vladimir Putin ya riga ya fara yaƙin duniya na 3, kuma mafita ɗaya ce a matsa lamba domin tilastawa Rasha ta dakata.
'Yadda aka kama ni bayan sayen layin waya da ƴan bindiga suka taɓa amfani da shi'
A baya-bayan nan ne ƴansanda suka tsare wata matashiya mai suna Tititlayo Ibrahim, ƴar jihar Ondo kan laifin da ba ta san komai a kai ba bayan sayan layin waya da aka taɓa amfani da shi.
Falle Ɗaya: Me take nufi kuma daga ina ta samo asali?
Idan akwai wata kalma da za ta samu karɓuwa a wurin ƴan siyasa musamman a arewacin Najeriya to ita ce kalmar Falle Ɗaya wadda a yanzu haka amonta kawai ake ji na tashi a cikin wake da waƙoƙin siyasa.
Iran ta ce za ta faɗaɗa hare-harenta bayan barazanar Trump
Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 02 ga watan Afrilun 2026.
Ko Iran ta yi wa Amurka da Isra'ila ba-zata?
Lokacin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-haren haɗin gwiwa kan Iran ranar 28 ga Fabrairun 2026, tambayar ita ce tsawon wani lokaci yaƙin zai ɗauka?
Ƴan sama-jannati sun kama hanyar zuwa duniyar wata
Tafiyar, wadda aka yi wa laƙabi da Artemis II a turance, za ta ɗauki kimanin kwana 10, inda ƴan sama-jannatin za su je wuri mafi nisa fiye da kowane bil'adama a tarihi.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 3 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 2 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 2 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 2 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
Fitattun ƙasashen da ba za su buga kofin duniya ba a 2026
Fitattun ƙasashe da ke taka rawar gani a nahiyar turai da dama da na Afirka sun kasa samun damar buga gasar kofin duniya a wannan karon.
Wakilan Tonali sun tuntuɓi Real Madrid, Liverpool da Man U na zawarcin Diomande
Everton na bibiyar halin kwantiragin John Stones, wakilan Sandro Tonali sun tuntubi Real Madrid, Barcelona na kan gaba wajen neman Bernardo Silva.
Ƴan wasan gaba da suka fi ƙwazo da zura ƙwallo a wannan ƙarni
Wannan maƙala ta yi duba da nazari ne dangane da ƴan wasan ƙwallon ƙafa da ke gaba da suka fi ƙwazo da yawan zura ƙwallo a tarihin ƙwallo a ƙarni na 21.
City na son Anderson, United na harin Tonali, Liverpool za ta ɗauko Conceicao
Man City ta shiga gaban United kan ɗaukar Elliot Anderson, United ta kara matsa ƙaimi wajen siyen Sandro Tonali, yayin da Liverpool ke son Francisco Conceicao don maye gurbin Salah.
Ina Salah zai koma idan ya bar Liverpool?
A tsawon shekarun da ya shafe a Anfield, Salah ya ci kwallaye 255 a wasanni 435, inda ya taimaka wa kungiyar lashe kofuna da dama ciki har da gasar Firimiya biyu da kofin Zakarun Nahiyar Turai.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Me ke faruwa a Jos?
Ana zaman ɗarɗar a birnin Jos na jihar Filato bayan wasu rahotanni da ke cewa an samu hargitis bayan sassauta dokar hana zirga-zirga ta kwana biyu da aka ƙaƙaba sanadiyyar wani mummunan hari da wasu ƴan bindiga suka kai
Dabarun yin barci cikin minti biyu irin na sojoji
Yanayin yadda mutane suke fama da matsalar ya bambanta, amma bincike ya nuna cewa tsakanin kashi 5 zuwa kashi 50 na mutanen duniya suna fama da cutar.
Abin da ya sa yunƙurin ƙwace uranium ɗin Iran zai zamo mai haɗarin gaske
Abin da kamar wuya sojojin Amurka su kutsa wurin adana makamashin nukiliyar Iran wanda yake a ƙarƙashin ƙasa domin ƙwace shi, amma kuma wannan yana daga cikin abubuwan da Donald Trump rahotanni ke cewa yana duba yiwuwarsa domin cimma burinsa na yaƙi: wato hana Iran cimma makamin nukiliya.
Gwamnatin APC ke kunna wutar rikici a jam'iyyun adawa - ADC
Rikicin shugabancin jam'iyyar ADC ya kunno kai ne a watan Yulin 2025 lokacin da shugabannin jam'iyyar suka yi murabus, kuma David Mark ya zamo sabon shugaba na riƙon ƙwarya, inda aka zaɓi sauran ƴan kwamitin zartarwa babu hamayya.
Me dokar Najeriya ta ce kan masu son tsayawa takara idan ba su ajiye muƙaminsu ba?
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umurci duk masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara a zaɓen 2027 su yi murabus kafin ko a ranar 31 ga Maris, 2026.
Ministocin Bola Tinubu da suka ajiye aiki 'don tsayawa takara'
Sai dai har yanzu akwai wasu ministocin da aka yi tsammanin za su ajiye muƙaman nasu, amma ba a ga sun yi hakan ba, duk kuwa da cewa an ga alamun suna da sha'awar yin takara a babban zaɓen ƙasar na 2027.
Wane ne Alex Babir, Ba'amurken da ake zargi da 'ingiza ƴan Najeriya su ɗauki makami'?
Tun bayan bayyanar wani matashi ɗan Amurka mai suna Alex Babir yana sukar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu bisa gazawarsa wajen daƙile kai wa al'ummar jihohin Benue da Plateau, ƴan Najeriya ke son sanin haƙiƙanin wane ne wannan matashi.
Haɗakar ADC : Wane tasiri shigar manyan ƴan'adawa za ta yi a zaɓen 2027
''Waɗannan jiga-jigan uku, haɗuwarsu wuri guda lalle wani babban ƙalubale ne ga jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu. Abu ne da za mu iya cewa ƙila ba su yi lissafin aukuwarsa ba zuwa yanzu''
Iran ta musanta iƙrarin Trump cewa ta nemi a tsagaita wuta
Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 01 ga watan Afrilun 2026.
Yadda adawa ke ƙara ƙazancewa tsakanin Boko Haram da Iswap
Masu sharhi a Najeriya da kuma kafofin sada zumunta da ke da alaƙa da masu iƙirarin jihadi sun yaɗa wani sabon bidiyo da aka danganta da mayaƙan Boko Haram. Bidiyon ya yi alawadai da aƙidun ƙungiyar ISWAP'
Abin da ya sa Trump ya bar Pakistan ta zamo mai shiga tsakani a yaƙin Iran
A baya-bayan nan shugaban na Amurka na bayyana shi a matsayin ''wanda ya fi jin daɗinsa'' inda a baya ya riƙa magana kan yadda Munir ya san Iran ''fiye da mafi yawan mutane''.
Mece ce mashigar Bab al-Mandab da Iran ke barazanar sake rufewa?
Barzanar da Iran ta yi na rufe wata hanyar ruwa mai muhimmanci a Tekun Maliya ya janyo fargabar, kan yadda hakan zai ƙara kawo tsaiko ga kasuwanci a duniya.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.





























































