Wace fa'ida Kannywood ta samu daga ƴaƴanta da suka samu muƙamai?

Kannywoo

Asalin hoton, Social Media

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

A daidai lokacin da ake ci gaba da tafka muhawara kan rabon shigafa a tsakanin jaruman masana'antar Kannywood, masu bibiyar masana'antar sun fara tattaunawa game da asalin abin da ya kamata masana'antar ta samu.

A cikin azumin watan Ramadan da ya wuce ne jarumin masana'antar, Nuhu Abdullahi ya raba wa wasu jaruman masana'antar shinkafa da kuɗin cefane, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce mai zafi.

Daga cikin masana'antar akwai waɗanda suka yi sam-barka da rabon, yayin da wasu kuma suka nuna rashin jin daɗinsu kan cewa ba rabon shinkafa suke buƙata ba, inda suka ce akwai abubuwa na gyara masana'antar ke buƙata.

Daga cikin waɗanda suka yi zafi kan rabon shinkafar akwai darakta Ahmad Bifa, wanda ya ce akwai jaruman da bai kamata su fito a kafofin sadarwa suna karɓar shinkafa.

Ya ce irin wannan zai kashe wa jaruman kasuwa sannan ya ce za su iya janyo wa forudusoshi asara, kamar yadda ya bayyana a zantawarsa da Ali Jita.

Sai dai wasu jaruman, irin su Garzali Miko, wanda ya bayyana cewa ya ji daɗin rabon shinkafar, kuma a shirye yake ya je ko'ina ya ji za a raba shinkafa.

Kannywood ta mori siyasa?

Tun bayan muhawarar da ta ɓarke a masana'antar, sai maganganu suka fara fitowa kan ko masana'antar ta amfana da muƙaman siyasa da ta rabauta da su a wa'adin mulkin da ake ciki.

Dr Muhsin Ibrahim, malami a jami'ar Cologne da ke Jamus, kuma mai sharhi kan harkokin fina-finai ya ce masana'antar ta samu tagomashi, domin a cewarsa, ana yi da kai ya fi ba a yi da kai.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Tabbas Kannywood ta ƙaru da siyasa saboda dalilai da yawa, musamman samun mukamai da dama da ƴan masaa'antar suka yi a gwamnati. Misali Ali Nuhu da Rahama Sadau a matakin tarayya da su Abba El-Mustapha da sauransu a jihohi," in ji shi.

A game da irin taimakon da masana'antar ke so, Muhsin ya ce akwai hanyoyi da yawa da gwamnati za ta cicciɗa masana'antar ta ƙara ƙarfi.

"Ka ga akwai misali akwai cibiyar fim ta "Film Village". Ni ina goyon baya a gina ta a jihar Kano ko a wasu jihohin domin hakan zai haɓaka harkokin fim baki ɗaya," in ji Dr Muhsin.

Masanin harkokin na fim ya ƙara da cewa gwamnati za ta iya taimakon ƴan masana'antar da bashi mara ruwa ko kuma bashi mai ruwa kaɗan domin su shirya fina-finai masu inganci.

Muhsin ya ce da ƴan masana'antar Kannywood za su samu bashi mara ruwa, abubuwa da yawa za su zo musu da sauƙi.

"Shuhurarsu ba ta kai girman da masu zuba jari daga ƙasashen waje za su shiga ba, ko kuma manyan kamfanoni su zuba kuɗi. Shi ya sa za su fi buƙatar tallafi ko bashi mara ruwa."

Muhsin ya kuma ƙara da cewa ƴan masana'antar na buƙatar horo na musamman domin ƙara sanin makamar aiki.

"A zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, an tura su Ali Nuhu da Hafizu Bello da Bello Muhammad Bello da Hadiza Gabon da sauransu zuwa Amurka, sannan aka tura su Iyantama da Mandawari da sauransu zuwa India domin samun horo na musamman."

Rigimar shinkafa

Wata rigima da ta yi tashe a bana ita ce rigimar shinkafa, wadda ta haifar da ce-ce-ku-ce sosai a masana'antar.

A game da wannan, Dr Muhsin ya ce Kannywood na fama da matsalolin rikice-rikice ne saboda abubuwa da yawa.

"Rigimar na da alaƙa da abubuwa da yawa. Masana'anta ce da ta haɗa mutane daban-daba masu fahimta iri-iri," in ji shi.

Sai dai ya ƙara da cewa masana'antar na fama da ƙyashi da hasada da ƙoƙarin cin dunduniyar juna da ya ce sun yi ƙamari a masana'antar.

"Amma ina ganin duk da cewa masana'antar ta cancanci taimako sama da rabon shinkafa, ina ganin idan aka kawo shinkafar, ban ga laifi idan masu buƙata sun karɓa, waɗanda kuma ba sa buƙata su bari," in ji shi.

Ya ce bai ga dalilin da a yi ta yamaɗiɗi da maganar ba, "kuma ko da ma akwai saɓanin fahimta, magana ce ta cikin gida. Kamata ya yi su zauna a tsakaninsu su daddale komai ba sai an fitar kafofin sadarwa ba," in ji Muhsin.

Muƙaman da ƴan Kannywood suka samu a gwamnati

Kusan za a iya cewa ba a taɓa zangon mulki da ƴan Kannywood da dama suka rabauta da muƙaman siyasa tun daga matakin tarayya da wasu jihohi kamar wannan ba.

An dai ga yadda ƴan masana'antar suka shiga aka dama da su dumu-dumu a harkokin yaƙin neman zaɓe a kowane ɓangare na siyasa, inda kusan kowane ɓangare na jam'iyya da ƴantakara suke da masu tallata su daga masana'antar.

Ga wasu waɗanda suka samu muƙaman gwamnati, duk da cewa zuwa yanzu wasu sun sauka daga muƙaman, amma sun daɗe suna riƙe da kujerun.

Ali Nuhu - Shugaban Hukumar Finafinai ta Najeriya

Gwamnatin Najeriya a ƙarƙashin Bola Tinubu ce ta naɗa fitaccen jarumi kuma darakta, Ali Nuhu a matsayin shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya.

Rahama Sadau - Kwamitin iDICE

Rahama Sadau kuma ta samu shiga cikin kwamitin bunƙasa zuba jari ta hanyar amfani da fasahar zamani wato Technical Committee of the Investment in Digital and Creative Enterprise programme (iDICE) wanda yake ƙarƙashin ofishin mataimakin shugaban ƙasa.

Bashir Datti - Kwamishina a jihar Filato

Bashir Lawandi Datti jarumi ne kuma furodusa a masana'antar Kannywood.

Ya yi takarar kujerar majalisar jihar Filato sau biyu a shekarar 2019 da 2024, amma bai samu nasara, yanzu shi ne kwamishinan albarkatun ruwa da makamashi.

Abba El-Mustapha - Hukumar Tace Fina-finai ta Kano

Abba El-Mutapha shi ne shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, matsayin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa shi bayan sun samu nasara.

Sunusi Oscar 44 - Mai ba gwamnan Kano shawara kan Kannywood

Shi ma fitaccen darakta a Kannywood, Sunusi Hafiz, wanda aka fi sani da Sanusi Oscar 442 ya rabauta da muƙamin bai ba gwamnan Kano shawara na musamman a kan harkokin Kannywood, amma ana tunanin ya sauka daga muƙamin ya koma ɓangaren Kwankwaso.

Tijjani Gandu - Mai ba gwamnan Kano shawara kan mawallafa

Shi ma fitaccen mawaƙin siyasa, wanda ya fi fice da waƙarsa ta Abba gida-gida wato Tijjani Hussaini Gandu ya samu muƙamin mai ba gwamnan Kano shawar na musamman kan harkokin mawallafa, amma shi ma ya sauka daga muƙamin.

Maryam Jankunne - Mai ba gwamnan Kano shawara kan matan karkara

Hakazalika an naɗa tsohuwar ƴar Kannywood, Maryam Abubakar Jankunne a matsayin babbar mai ba gwamnan Kano shawara kan matan karkara.

Rabiatu Sulaiman Kurfi - Mai taimaka wa gwamnan Katsina kan kafofin sadarwa na zamani

Rabiatu Sulaiman Kurfi ita ce mai ba gwamnan Katsina, Dokta Dikko Raɗɗa shawara a kan kafofin sadarwa na zamani.