''Ya kamata jama'a su rungumi tubabbun 'yan tada kayar baya''

Yan tada kayar baya

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Yan tada kayar baya
Lokacin karatu: Minti 2

Yayin da mutane da dama ke nuna fargabata kan mu'amala da tubabbun yan tada kayar bayan nan sama da 700 da gwamnatin Najeriya ta saki, wasu masana halayyar dan adam sun yi gargadin rashin jan su a jiki, na iya janyo su sake komawa ruwa.

A baya bayan nan ne gwamnatin kasar ta saki mutanen su 744, bayan an gyara masu tunani, da kuma kyautata rayuwarsu, karkashin wani shirin gwamnatin kasar na ganin an cire musu tsatstsauran ra'ayin da suke da shi, da ke tunzura su wajen cutar da jama'a.

Ko da yake ba wannan ne karon farko da ake sakin tubabun yan tada kayar baya ba a Najeriya, lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce, musamman kan yadda mutane da dama ke ganin hakan a matsayin ganganci, domin watakila mutanen na iya sake komawa gidan jiya.

Sai dai Farfesa AbdulLahi Maikano Madaki, malami a sashen nazarin zamantakewar dan Adam na jami'ar Bayero ta Kano, ya ce wajibi ne gwamnati da jama'ar gari su tashi tsaye wajen rungumar wadannan tubabbu da aka yaye, don a tabbatar yanayin rayuwarsu ya inganta, kuma ba su koma ruwa ba.

Masanin ya shaida wa BBC Hausa cewa akwai tsare tsare da dama da ake sanya su a ciki don a nusar da su rayuwa da kuma yadda ya kamata su zama, don su tashi daga matsalolin da suke haifarwa, kana su zama masu amfani ga al'umma, don haka bai kamata mutane su daga hankalinsu ba.

Ya ce''Su jama'ar gari su karbe su, a rungume su, kada a tsangwame su ko a kyare su, mu'amala mai kyau za ta taimaka, duk lokacin da suka zo neman taimako ko wata shawara daga jama'a ya kamata a ba s.''

Ya kara da cewa ''A nasu bangaren hukumomi dole ne su samar masu abubuwan da za su yi, wadan da za a horar a horar, wadanda za a koyawa sana'oi a koya masu, kada a tilasta masu yin sana'ar da ba ita su ke son yi ba, a sanya su, su ji sun zama kamar kowa.

Tubabbun yan tada kayar bayan dai sun fito ne daga sassa daban-daban na Najeriya, biyu sun fito daga Jihar Abia, goma daga Jihar Adamawa, daya daga Jihar Akwa Ibom, biyu daga Jihar Anambra, goma sha biyu daga Jihar Bauchi, 597 daga Jihar Borno, uku daga Jihar Ebonyi, daya daga Jihar Enugu, goma sha biyar daga Jihar Kano, uku daga Jihar Katsina, daya daga Jihar Kebbi, biyar daga Jihar Kogi, hudu daga Jihar Nasarawa, biyu daga Jihar Niger, biyu daga Jihar Plateau, biyu daga Jihar Sokoto, sannan 58 daga Jihar Yobe.