Ina ce mashigar Malacca da ka iya haɗa Amurka da China yaƙi?

..

Asalin hoton, EPA

    • Marubuci, Luis Barrucho
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Kafin cimma yarjejeniyar da ta sa ƙasar Iran buɗe mashigar Hormuz, ɗaya daga cikin manyan hanyoyin ruwa a duniya, hankalin duniya ya koma kan wata muhimmiyar mashigar.

Mashigar Malacca, a kudu maso gabashin Asiya ce hankali ya karkata can bayan jami'an Indonesiya suka tabbatar da cewa Amurka ta gabatar da buƙatar tura sojojinta zuwa ƙasar, bayan cimma yarjejeniyar tsaro da aka sanya wa hannu a ranar Litinin.

Ma'aikatar harkokin wajen Indonesiya ta ce har yanzu ana nazari kan matakin.

Masana sun ce matakin zai iya haifar da ƙalubale a faɗin duniya.

Amma ina ne mashigar Malacca, kuma me ya sa take da muhimmanci?

Muhimmancin Malacca a duniya

..
Bayanan hoto, Mashigar Malacca tana da faɗin kusan kilomita 2.8, a kusa da Singapore

"Mashigar Malacca tana da muhimmanci saboda ita ce hanya mafi gajarta kuma mafi inganci wacce ta haɗa Tekun Indiya zuwa tekun Pacific, wanda ya sa ya zama dole a yi amfani da mashigar wajen kasuwanci tsakanin Gabas ta Tsakiya, Turai da Gabashin Asiya," in ji Azifah Astrina wata ɗalibar PhD a jami'ar Illinois Urbana‑Champaign a Amurka da ta ke nazari kan zirga-zirgar ta mashigar ruwa

Ta ce, "Ya haɗa tekun kudancin ƙasar Sin, inda kusan kashi ɗaya bisa uku na cinikayyar duniya ke tafiya."

Ita ce mashiga mafi siranta ta mashigar Phillips Channel da ke kusa da Singapore, inda ba ta wuce faɗin kilomita 2.8 ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar wani rahoto a baya-bayan nan da Hukumar Kula da Makamashi ta Amurka (EIA) ta fitar, ganga miliyan 23.2 na mai a rana suna wucewa ta Malacca a farkon rabin shekarar 2025 - kwatankwacin kusan kashi 29% na yawan man da ake fitawarwa a tekunan duniya. A daidai wannan lokacin, an kuma fitar da kimanin mita 260 na iskar gas (LNG).

Gokcay Balci, malami a fannin sufurin kaya da dabaru a Jami'ar Leeds ta Burtaniya, ya ce hanyar ruwar kuma babbar hanya ce ta fitar da kayan lantarki, kayan masarufi, kayayyakin masana'antu, injina da motoci.

"Kusan kashi 25% na cinikin motoci na duniya ne ke bi ta cikinsa. Kayan hatsi irin su waken soya, su ma suna wucewa ta mashigar," in ji shi.

Balci ya ƙara da cewa: "Ita ma Hormuz tana da mahimmanci ga kasuwancin duniya, amma bai kai kamar mashigar Malacca ba. Amfaninsa ya wuce na makamashi kawai, har da wasu nau'ikan kayayyaki da masarufi."

Astrina ta kara da cewa "Za a iya cewa Malacca na ɗaya daga cikin hanyoyin ruwa da ke taka rawa ga tattalin arzikin duniya."

Fashin jiragen ruwa ma abin damuwa ne. An sami rahotannin fashin teku guda 108 a mashigar Malacca da Singapore a 2025 - mafi yawa tun 2007 - a ewar Cibiyar Tattara Bayanai ReCAAP da ke Singapore.

Mahigar na kuma fuskantar ƙalubalen yanayi, da suka haɗa da ambaliyar tsunami ko aman dutse. Alal misali, ambaliyar tsunami da ta faru a watan Disambar 2004, ta haifar da babbar illa a tekun.

Me ya sa take da muhimmanci?

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Indonesiya ta ce har yanzu tana nazarin kan buƙatar da Amurka ta amfani da sojojinta a ƙasar bayan da kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro

Masana sun ce muhimmancin Malacca bai ta'allaƙa ne kan tattalin arzikin kaɗai ba, har ma da tasirinta ga yankuna.

"Ko yaya aka samu tashin hankali tsakanin China da Amurka ko Indiya game da mamaya a ruwa yankin na iya kawo cikas ga hanyoyin mashigar," in ji Balci.

Astrina ta ce hatta yiwuwar tura sojojin Amurka zuwa sararin samaniyar Indonesiya na iya yin tasiri na dogon lokaci.

Binciken nata ya nuna cewa tsarin samar da tsaro a yanzu a mashigar Malacca ba zai iya aiki idan akwai tankiya tsakanin manyan ƙasashe ba.

"An tsara shi ta yadda zai magance barazanar kan ruwa - irinsu fashin teku, fasa-kwauri da kuma laifukan ruwa, ba wai nuna ƙarfin iko ba" in ji ta.

"Saboda haka idan wata babbar ƙasa kamar Amurka ta ƙara faɗaɗa aikinta, hakan zai kawo wani tsarin tsaro da ba a san da shi ba."

A ƙarshe dai ta ce ba lallai a samu wani tsaiko ba.

Babbar bazaranar, lokaci ne kawai zai nuna.

"Damuwar it, idan China ta kalli hakan a matsayin ƙaruwar sa ido ko daga Amurka a kusa da wannan muhimmin tashar ruwar, za ta iya mayar da martani."

"A nan ne barazanar ta ke. Za fara ganin turjiya daga haɗin kan da ake da shi, da kuma amfani da soji"

Ko da ba a samu rikici ba, ta yi gargadin irin wannan canjin na iya yin tasiri sosai.

Ta kuma yi gargaɗin kada a raina ƙarfin Indonesiya.

"Bai kamata a ga Indonesiya ta karkata ga wani bangare ba," in ji ta.

"Da alama Indonesiya na bin dabarun daidaita lamura - zurfafa haɗin gwiwa da Amurka tare da kulla alaka mai karfi ta fuskar tattalin arziki da China da yin haɗaka da sauran ƙawayenta kamar Rasha."

'Tsaka mai wuya a Malacca'

A shekarar 2003, shugaban ƙasar China na wancan lokacin Hu Jintao ya ayyana wani laƙani kan mashigar Malacca da sunan "Tsaka Mai Wuya", domin nuna yadda China ta dogara sosai kan mashiwar ruwan.

Kimanin kashi uku cikin huɗu na da man da ake shiga da shi China - da kuma kusan kashi 60% na kasuwancin cinikin teku - suna ratsawa ne ta mashigar Malacca da tekun kudancin kasar China, kamar yadda bayanai daga EIA da CSIS ChinaPower Project suka nuna.

"Amma ba China kaɗai ba, Japan da Koriya ta Kudu ma sun dogara sosai kan mashigar kan makamashi, inda kusan kashi 90% na man da suke shigo da su ke bi ta cikinsa," in ji Balci.

Ya ƙara da cewa hanyar ruwan tana kuma da matuƙar muhimmanci ga ƙasar Singapore, wacce ke ɗauke da tashar jiragen ruwa ta biyu mafi hada-hadar a duniya, kuma ita ce babbar cibiyar shan mai ga jiragen.

Astrina ta ce rage dogaro kan mashigar da China za ta yi wani abu ne na gajeren lokaci.

"Ba na tunanin China tana da wasu hanyyoyin rage dogaro kan ruwan a nan kusa," in ji ta.

"Wasu hanyoyin ta bututu ko mashiga za su taimaka wajen rage ƙalubalen, amma ba za su iya maye gurbin Malacca ba," in ji Balci.

Ya ce akwai wasu hanyoyin masu muhimmanci - Mashigar Sunda da Lombok - da suke cikin ruwan Indonesiya.

Mashigar Torres da ke kusa da Papua New Guinea, mashiga ce amma ba ta da wani muhimmanci sosai kuma manyan jiragen ruwa ba za su iya bi ta wajen ba.

Balci ya kara da cewa tafiya ta kudancin Ostireliya, akwai kashe kuɗi da dogon lokaci.

Idan aka yi la'akari da wannan in ji Astrina, China za ta fi mayar da hankali ne wajen ganin ta ci gaba da kula wurin a madadin toshe shi.

Tsaka mai wuyar ba wai a kan rage dogaro kan ruwan ba ne. Ya danganta da yadda China ta ke amfani da damar."

Ta kara da cewa, "Don haka ne muke ganin China ta mai da hankali kan raba ƙafa, da faɗada tasirinta da kasancewarta a duk faɗin duniya, musamman a tekun kudancin kasar China da kuma wasu muhimman hanyoyin teku."