Shin muna tunkarar yaƙin duniya na uku ne ko ana razana mu ne kawai?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ahmen Khawaja, Global Journalism team
- Marubuci, The Global Story podcast
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Watanni uku kenan tun bayan fara yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran, ana ta nuna fargaba kan yiwuwar yaƙin na Gabas ta Tsakiya na iya girmama.
Ba iya Iran yaƙin ya shafa ba, har wasu ƙasashe da dama a yankin irinsu, Haɗaɗɗiyar Daular Larabarawa, Iraƙi, Bahrain, Kuwait, Saudiyya, Oman, Azerbaijan, West Bank, Cyprus, Siriya, Qatar daLebanon.
Ana ta nuna damuwa kan cewa rikin na iya zama ɓarkewar yaƙin duniya na uku.
Yaushe ne yaƙi yake zama yaƙin duniya?
"Mutane suna tunanin cewa ana shirya yaƙe-yaƙe ne a tsanake kuma duk waɗanda suka fara yaƙi sun san abin da suke yi," in ji Margaret MacMillan, farfesa a fannin tarihin ƙasa da kasa a Jami'ar Oxford da ke Birtaniya, a hirarta da BBC.
"A zahirin gaskiya, idan kuka kalli yaƙe-yaƙe da suka gabata… Yaƙin Duniya na farko… yawancin abin da ya haifar da shi, ya faru ne bisa kuskure, kuma mutane suna yin wuce gona da iri kan abokan hamayya," in ji Farfesa MacMillan.
Kisan ɗan uwan Sarkin Ostiriya-Hungary Franz Joseph, Archduke Franz Ferdinand ne ya jawo jerin abubuwan da suka tayar da yaƙin duniya na ɗaya a 1914, in ji MacMillan.
A cikin makonni, ƙungiyar ƙawance ta jawo Turai cikin rikicin: ƙasashen Austria, da Hungary suka far wa Serbia, Jamus ta goyi bayan Austria, ita kuma Rasha ta goyi bayan Serbia, Faransa kuma ta goyi bayan Rasha, yayin da ita kuma Biritaniya, ta shiga yaƙin da sunan daidaita lamura.
Abin da ya biyo baya kuwa sai ya zama bala'i a duniya, in ji ta.

Asalin hoton, Stringer/Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Joe Maiolo, wanda farfesa ne a fannin tarihin ƙasa da ƙasa a King's College da ke Landan, ya bayyana yaƙin duniya a matsayin ruwan dare wanda ya shafi dukkan manyan ƙasashe.
Ya shaida wa BBC cewa "A yaƙin duniya na farko, ya shafi ƙasashen turai ne ke daular mulkin mallaka. A yaƙin duniya na biyu, ya haɗa da Amurka da Japan da China."
Mutane da dama za su kwatanta tashin hankalin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya a matsayin gagarumin yaƙi na yanki. Amma shin ya cancani a faɗaɗa shi?
A wata hira da BBC a watan Fabrairu, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce ya yi amanna cewa shugaban Rasha Vladimir Putin ya riga ya fara yaƙin duniya na 3, kuma mafita ɗaya ce a matsa lamba domin tilastawa Rasha ta dakata.
"Na yi imanin cewa Putin ya riga ya fara. Tambayar ita ce har faɗin yanki nawa ne zai iya ƙwacewa da kuma yadda za a hana shi... Rasha na son ƙaƙaba wa duniya wata salon rayuwa ta daban da kuma canza mutane abin da suka zaɓa wa kansu," in ji shi.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
To yanzu mene ne yiwuwar fara yaƙin duniya na uku?
"Ina ganin ƙasar da ka iya ta'azzara ita ce Iran, ko ƙawayenta, kamar irinsu mayaƙan Houthi a Yemen," in ji MacMillan.
Abubuwan da Iran za ta iya yi - irin su kai hari kan hanyoyin jigilar kayayyaki ko rufe mashigin Hormuz - na iya haifar da illa ga duniya, da kawo cikas ga samar da makamashi da kuma jawo hankalin manyan kasashe, a cewar MacMillan.
Har ila yau, shigar Amurka yaƙin ya ƙara rikita lamarin; Ta ƙara da cewa, wasu ƙasashen, ko da ba su shiga kai tsaye ba, tattalin arzikinsu ya taɓu.
Akwai kuma wani ƙalubalen, in ji ta. Rikice-rikice a wani yanki na iya haifar da damammaki a wasu wurare.
Alal misali, kasar Sin na iya karkatar da hankalin yammacin duniya domin ta samu damar ƙarbe iko da Tiwan, ko kuma Rasha na iya ƙara tsananta farmakinta a Ukraine yayin da hankalin duniya ke wasu wurare.
"A ko wane irin lokaci, akwai yuwuwar rikicin ya bazu fiye da wannan yanki, saboda wasu da ke wajen yankin za su ga cewa ga dama ta samu sakamakon rikicin, saboda ya ɗauke hankalin mutanen da za su iya hana su yin abin da suke so," in ji MacMillan.
Farfesa Maiolo ya yi imanin cewa za a ci gaba da wannan rikicin a yankin Gabas ta Tsakiya, kuma zai yi tasiri a ƙasashen kungiyar haɗin kan yankin Gulf, da suka hada da Saudiyya. Sai dai ya ce ba ya tunanin China da Rasha za su shiga yaƙin.
"Tunanin cewa idan wani abu yana faruwa a duniya, China za ta mamaye Taiwan... tunani mara kan gado ne."
"Amma idan muna magana ne game da yaƙin duniya, yaƙin duniya na uku, ba na jin China ko Rasha za su yi sha'awar shiga kai tsaye ko kaɗan, ballantana ma nahiyar Turai."
Ya yi imanin cewa, ƙasar China na da wasu tsare-tsare na diflomasiyya da shugaba Trump: "Lokacin da abokin hamayyar ku yake aikata wani babban kuskure, kawai ku bar su, su ci gaba," in ji shi.
Maiolo ya ce "A cikin manyan tsare-tsare na muradun manyan ƙasashe, ɗauke hankalin Amurka a Gabas ta Tsakiya ya fi muhimmanci fiye da albarkatun mai a China."
Rawar da shugabanni ke takawa

Asalin hoton, Getty Images
MacMillan ta ce tarihi ya nuna cewa yawancin dalilin fara yaƙi saboda yana samo asali ne daga izza daga ƙasashe, ko kare martaba, ko kuma tsoron abokan hamayya.
Ta kuma ce tarihi ya nuna cewa ɗaiɗaikun shugabanni na iya tsara yadda al'amura za su gudana.
"Firaministan Faransa, [Georges] Clémenceau, a lokacin yaƙin duniya na farko ya ce wanzar da zaman lafiya ya fi yin yaƙin wahala."
A cewar MacMillan, sau da yawa akan nace cewa idan har aka samu manyan asarori ko sadaukarwa da rayuwa da mutane suka yi, wasu shugabannin suna yanke shawarar cewa dole ne su "ci gaba da yaƙin har sai sun ci nasara".
Ta ce girman kai na iya zama abin da ke ingiza shugabanni - inda ta ba da misali da Putin: "Ya yi babban kuskure wajen yunƙurin mamaye Ukraine."
Bayan kaɗɗamar da farmakin da aka yi bayan shekaru huɗu da suka gabata, Putin ya ce manufarsa ita ce "karya lagon sojinta da kuma wargaza" Ukraine, amma duk da haka Rasha ta ce har yanzu ba a cimma manufarta na soji a Ukraine ba, in ji ta.
Ma'aikatar tsaron Burtaniya ta yi ƙiyasin cewa Rasha ta yi haifar da asarar rayuka miliyan 1.25, wanda ake ganin ya zarta asarar da Amurka ta yi a lokacin yaƙin duniya na biyu, a cewar ministan tsaron ƙasar.
MacMillan ta ƙara da cewa shugabannin da suka ƙi amincewa da faɗuwa ko gazawa a yaƙi na iya tsawaita rikici.
Ta ƙara da cewa a baya, mutane irin su Adolf Hitler sun ci gaba da fafatawa a yaƙi duk kuwa da cewa an yi galaba a kansu amma suka ƙi ja da baya saboda akida da alfahari.
Irin waɗannan tunane-tunanen za su iya faɗaɗa rikici zuwa munanan yaƙe-yaƙe.
Hanyoyin daƙile yaɗuwar rikicin

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Domin cimma wannan burin na rage faɗaɗar yaƙin, bin hanyoyin diflomasiyya na da matukar muhimmanci, in ji MacMillan: "Akwai buƙatar ji daga ɗaya bangaren"
Ta bayyana cewa an samu ci gaba game da tattaunawa daga kowane ɓangare a cacar bakan da ake yi da kuma shigar da kungiyar tsaro ta Nato.
"Akwai misalai da yawa inda mutane suke ganin, wannan lamarin yana ƙara ƙazancewa. Sun fahimci cewa lamarin akwai sarƙaƙiya kuma akwai buƙatar tsagaitawa."
Kasancewar akwai makaman nukiliya, yana daga cikin abubuwan lura wajen daƙile bazuwar yaƙin musamman idan manya ƙasashe suka shigo ciki.
Farfesa Maiolo ya ce: "Dole ne sai kowa ya amince… a Tel Aviv, Washington da Tehran… cewa sun kai matakin abin da suke son cimma."
Ya bayyana cewa ci gaba da yaƙi ba zai "samar da ɗa mai ido ba" ga kowane ɓangare ba."
"Akwai buƙatar a samar da wasu tsare-tsare game da janye takunkumi, da wasu tsare-tsare na tsaro, da fahimtar matsayin Iran a siyasar duniya."
Maiolo ya ce ta hanyar sasantawa ne kawai hukumomin da abin ya shafa za su iya kawo karshen yaƙin, sannan su samu mafita mai ɗorewa.








