KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 03/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 03/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Iran ta ci gaba da kai hare-hare kan Isra'ila ta yankin Gulf

    Hri

    Asalin hoton, ..

    Iran ta ci gaba da kai hare-hare kan Isra'ila da sauran ƙasashen yankin Gulf.

    A Kuwait babban kamfanin na ƙasar ya ce an kai wa matatar mai ta Mina al- Ahmadi hari da jirage marasa matuƙa, yayin da ma'aikatan agaji ke ƙoƙarin kashe gobarar da ta tashi bayan hare-haren.

    Can a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa hukumomin ƙasar sun bayar da rahoton kai hare-hare.

    A Isra'ila sojojin ƙasar sun ce na'urorin tsaron samniyarta na aikin kakkaɓo makaman linzami da Iran ta harba cikin ƙasar.

  2. Dimokraɗiyya ba ta dace da Burkina Faso ba - Traore

    Kyaftin Ibrahim Traore

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban mulkin sojin Burkina Faso ya shaida wa al’ummarsa su daina sa rai da dimokuraɗiyya.

    A wata hira da aka watsa a gidan talabijin na ƙasa, Kyaftin Ibrahim Traore ya ce ba shi da wani shiri na gudanar da zaɓe, duk da cewa ya yi alƙawarin mayar da mulki ga farar hula lokacin da ya karɓi iko shekaru huɗu da suka gabata.

    Sai dai a ranar Alhamis, ya bayyana a fili cewa dimokuraɗiyya ba ta dace da al’ummar Burkina Faso ba.

    Gwamnatinsa ta soja ta gaza shawo kan rikicin tashe-tashen hankulan masu iƙirarin jihadi da suka addabi ƙasar.

    Haka kuma, ƙungiyoyin kare hakkin ɗanadam na ci gaba da suka kan kamun ludayin gwamnatinsa ta fuskar ƴancin ɗan'adam.

  3. Kiristoci na bukuwan Ranar Easter

    Mahalarta taron addu'o'in Easter

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban limamin Katolika na Latin a Birnin Ƙudus ya jagoranci wani taron ibada kwanaki bayan da ƴansandan Isra’ila suka hana shi shiga cocin da ake girmamawa a matsayin wurin da aka gicciye Yesu Almasihu.

    A daren Alhamis, Kardinal Pier-battista Pizza-balla ya wanke ƙafafun fastocinsa a wani ɓangare na al’adar ibadar Kirista.

    Ana sa ran zai jagoranci wasu ibadu a yau, ciki har da ranar Good Friday da kuma Easter Sunday, sai dai za a takaita yawan masu halarta saboda matsalolin tsaro da suka shafi yaƙin da ake yi da Iran.

    A sauran majami’u kuwa, za a bai wa mutane kusan hamsin damar halartar tarukan ibadar.

    Duk da haka, yawancin wuraren ibada a tsohon Birnin Ƙudus na ci gaba da kasancewa a rufe, ciki har da masallacin Al-Aqsa da kuma Western Wall.

  4. Za mu tsananta hare-hare kan Iran idan ba ta ba da kai ba - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ƙara tsananta hare-hare kan Iran, matsawar shugabanninta ba su ba da kai ga buƙatunsa ba.

    Wannan gargaɗi na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan wasu ƙwararru a fannin dokokin duniya sun fitar da wata wasiƙa, inda suka yi gargaɗi kan manyan take dokoki da ake zargin Amurka, da Isra’ila da Iran da aikatawa.

    Ƙwararrun sun nuna damuwa kan kalaman barazanar da Mista Trump ke yi a tsawon yaƙin.

    Shugaban ya sake yin barazanar kai hari kan kayayyakin more rayuwa na Iran, kamar lalata gadoji da cibiyoyin wutar lantarki, abun da za a iya ɗauka a matsayin laifukan yaƙi.

    A ranar Alhamis, Amurka da Isra’ila sun kai hari kan wata gada da ake ginawa, da kuma wata daɗaɗɗiyar cibiya mai tarihi da ke samar da riga-kafin cututtuka.

  5. Assalam alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a da Hausawa ke yi wa kirari da Hajji babbar rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki, musamman yakin Iran da siyasar Najeriya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafa.