Dalilan da ke nuna haɗarin ƙwace sindarin uranium na Iran

Ƙwararru sun ce kai farmaki a rumbun sindaran makamashin nukiliyar Iran na ɗauke da ƙalubale da dama.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daniel Bush
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Washington correspondent
    • Marubuci, Bernd Debusmann Jr
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, White House reporter
  • Lokacin karatu: Minti 5

Abin da kamar wuya sojojin Amurka su kutsa wurin adana makamashin nukiliyar Iran wanda yake a ƙarƙashin ƙasa domin ƙwace shi, amma kuma wannan yana daga cikin abubuwan da Donald Trump rahotanni ke cewa yana duba yiwuwarsa domin cimma burinsa na yaƙi: wato hana Iran cimma makamin nukiliya.

Aiwatar da wannan shiri abu ne mai cike da ƙalubale da kuma haɗari, kamar yadda masana harkar soji suke faɗi da kuma tsoffin jami'an tsaro na Amurka da suka tattauna da BBC. Sun akwai buƙatar aikewa da dakarun soji kuma hakan ka iya ɗaukar kwanaki ko ma makonni masu dama kafin cimma hakan.

Kwashe sindaren na nukiliya daga rumbunsa "zai zama wani farmaki mafi jimirɗa a tarihi, " in Mick Mulroy, tsohon mataimatin sakataren tsaro a Gabas ta Tsakiya.

Farmakin ɗaya ne daga cikin ayyukan soji da Trump ka iya ɗauka a Iran.

Sauran matakan sun haɗa da ƙwace iko da tsibirin Kharj a wani yunƙuri na matsa wa Iran lamba domin ta buɗe mashigar Hormuz. Gwamnatin ta Trump ka iya amfani da barazanar wani sabon nau'in ayyukan soji domin matsa wa Iran lamba ta hau teburin tattaunawa.

A wata hira ta waya da kafar watsa labarai ta CBS a ranar Talata, shugaba Trump ya ƙi ya ce ko akwai yiwuwar ayyana samun nasara a kan Iran a yaƙin ba tare da ƙwace ko kuma lalata sindaren makamashin nukiliya.

Sai dai kuma da alama yana rage muhimmancin rumbun makamashin nukiliyar na Iran, inda yake nuni da irin lalata makamashin da aka yi a lokacin yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran a watan Yuni. "Yana can ƙarƙashin ƙasa saboda haka zai yi wa wuya ga wani ya lalata shi," in ji Trump. "Yana can ƙarƙas. Saboda haka... a killace yake tsaf. Amma kun san, za mu shirya."

Bayanan nasa na zuwa ne bayan wani rahoto na mujallar Wall Street Journal ta rawaito cewa Trump na duba yiwuwar kwashe sindarin na makamashin nukiliya. Fadar White House ta ce har yanzu Trump bai gama yanke shawara ba.

..

Asalin hoton, BBC VISUAL JOURNALISM

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙwararru sun ce kai farmaki a rumbun sindaran makamashin nukiliyar Iran na ɗauke da ƙalubale da dama.

A farkon yaƙi, Iran tana da sindarin uranium 440kg wanda aka bunƙasa shi zuwa kaso 60 kamar yadda manyan jami'an Amurka suka sanar. Za a iya bunƙasa shi cikin gaggawa zuwa mataki na 90 da ake buƙata domin samar da makamin nukiliya.

A hannun ɗaya kuma Iran na da kusan sinadarin na Uranium da aka bunƙasa zuwa mataki na 20 tare da kuma mai yawan kilogiram 8,500 da aka bunƙasa zuwa mataki 3.6 da ake buƙata wajen binciken magunguna.

An yi imanin cewa akwai sindarin uranium ɗin da aka alkilta wanda za a iya gina makaman nukiliya ko kuma makamai masu linzami, a rumbun da ke Isfahan. Isfahana na ɗaya daga cikin rumbuna uku na nukiliya a Iran da hare-haren Amurka da Isra'ila suka yi ƙoƙarin lalatawa a bara.

Sai dai babu tabbacin yawan sindarin uranium ɗin da aka bunƙasa da ke rumbunan

Yin amfani da ƙarfin soji wajen ƙwace sinadarin zai fi zama abu mai sauƙi ga Amurka idan da a ce sun san haƙiƙanin wurin da aka ɓoye su, in ji Jason Campbell, tsohon babban jami'in tsaron Amurka a gwamnatin Obama da kuma ta Trump.

"Abun shi ne sai ka san a wane wuri sinadarin yake," in ji Campbell. "idan a warwatse sinadarin yake a rumbunan huɗu da ke sassa daban-daban to wannan ana magana ne na wani batu mai sarƙaƙiya.

Hotunan tauraron ɗan'adam

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Baya ga Isfahan, akwai kuma rumbun da ke Fordo da Natanz wani wurin da a yaƙin Amurka da Isra'ila na bara suka hara.

Baya ga Isfahan, akwai kuma rumbun da ke Fordo da Natanz wani wurin da a yaƙin Amurka da Isra'ila na bara suka hara.

Rafael Grossi, darekta a hukumar da ke sa ido kan makamashin nukiliya, IAEA ya ce a watan da ya gabata mafi yawan sindaran uranium ɗin da aka alkilta na Iran na ma'adanar da ke Isfahan, sannan kuma akwai ƙari a Natanz. Amma Grossi ya ce babu cikakken bayani saboda masu sanya ido kan sindarin ba su ziyarci wuraren ba tun bayan da akwa kashe daga Iran a lokacin ƴakin Amurka da Isra'ila a kan Iran a 2025.

"Akwai tambayoyi da za mu iya amsa su ne kawai idan muka samu damar komawa," in ji Grossi.

Samun kaiwa ga sindarin na uranium da aka bunƙasa na da matuƙar ƙalubale ko da kuwa alal misali Amurka ta san wurin da suke.

Akwai alamu da ke nuna cewa Iran ta sanya sulke a ɗaya daga cikin rumbunan nata na ƙrƙashin ƙasa wanda ke kusa da ma'adanar sinadarin na nukiliya kafin wannan yaƙin na wannan shekarar.

Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna yadda aka yi amfani da ƙasa aka rufe ƙofofin hanyoyin ƙarƙashin kasa wanda hakan ke nufin duk wani farmaki da za a kai wa wurin yana da wahalar gaske.

Tun bayan farar wannan yaƙi, Amurka da Isra'ila na amfani ne da hare-hare ta sama kaɗai wajen kai wa sojojin ruwa da makamai masu linzami da masana'antu na Iran hari. To amma kuma idan dai ana son cimma maradun yaƙin da Amurka da Isra'ila suka sanya ciki har da ƙwace sindarin uranium na Iran to dole ne sai an aike da sojoji.

Amurka ka iya amfani da dakarunta na sama na runduna ta 82 waɗanda aka aike da su Gabas ta Tsakiya - za su iya mamaye yankunan da ke kewayen Isfahan da Natanz. Daga nan kuma sai a aike da runduna ta musamman da ke da horo yadda za su taɓa abubuwan da ke da alaƙa da nukiliya. Shi kansa sindarin na uranium kamar iska yake kuma an haƙiƙance cewa an adana shi ne a cikin rufaffun tukwane.

Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna yadda aka lalata ƙofofin shiga rumbun Isfahan da Natanz a yakin watan Yunin 2025. Dakarun Amurka ka iya amfani da manyan na'urori wajen tone ɓuraguzan domin gano uranium ɗin da aka bunƙasa wanda aka haƙƙaƙe cewa yana cikin wasu hanyoyin ƙarƙashin ƙasa - to amma fa duka wannan zai faru ne a daidai lokacin da jami'an za su fuskanci hare-hare daga Iran.

"Dole ne sai ka fara tone wurin domin gano uranium ɗin a daidai lokacin da kake fuskantar barazana," in ji Campbell.

ƙwararrun sun ce ɗauke sinadarin daga Iran zuwa wani wurin ya fi sauƙi a kan narka shi saboda hakan na da haɗarin gaske duk ma ta yadda aka shirya aiwatarwa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A 2025 satellite imagery of the Natanz nuclear enrichment facility

Idan har za a kai farmakin to zai zama dakarun Amurka da za su yi wannan aiki an ware su a Isfahan mai nisan kusan kilomita 300 daga birni mafi girma na uku na Iran. "Kwashe sojojin da suka ji rauni zuwa asibiti zai yi wuya saboda nisan. Sannan hakan zai sa sojojin Amurka su zama ababan kaiwa hari cikin sauƙi," in ji Plitsas.

Bugu da ƙari, ƙwararru na cewa dole ne wannan shiri ya ƙunshi ƙwace wani filin da sojojin Amurka za su rinƙa sauka suna tashi domin kwashe sindarin daga Iran idan har sun iya samun damar yin hakan sannan kuma sai Amurkar ta yi tunanin me za ta yi da sinadarin. Ko dai a fitar da shi daga Iran ko kuma a narkar da shi.

Ƙwararrun sun ce ɗauke sinadarin daga Iran zuwa wani wurin ya fi sauƙi a kan narka shi saboda hakan na da haɗarin gaske duk ma ta yadda aka shirya aiwatarwa.