Yadda naɗin ɗan ƙabilar Igbo a Afirka ta Kudu ya janyo tashin rikici

Asalin hoton, SABC Screengrab
Hankula sun fara kwanciya bayan wani rikici ya ɓarke a Afirka ta Kudu sakamakon naɗin wani ɗan ƙabilar Igbo muƙamin wata sarauta a ƙasar.
Rahotonni sun ce batun naɗin sarauta ne ya janyo rikicin, inda aka yi yunƙurin naɗa Solomon Egbonna Eziko a matsayin jagoran ƴan ƙasashen waje.
Chief Solomon Ogbonna Eziko ya samu muƙamin mai suna ''Igwe Ndigbo Na East London'', mako biyu da suka gabata.
Ƙungiyoyin fararen hula da na siyasa ne suka shirya zanga-zangar.
Daga baya zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali, bayan ɗaya daga cikin masu yinta ya yi iƙirarin cewa wani ɗan ƙasar waje ya taɓa masa wuƙa a lokacin zanga-zangar.
Fusatattun masu zanga-zangar sun ƙona shagunan ƴan ƙasasashen waje da na ƴan Afirka ta Kudu tare da cinna wa motoci aƙalla 10 wuta.
Masu zanga-zangar sun tilasta dakatar d kasuwanci, yayin da ƴansanda suka yi amfani da harsasan riba wajen tarwatsa su.
Ƴansandan sun ce fara bincike kan lamarin, kodayke ba wanda suka kama.
Magajin garin Princess Faku ta yi Allah wadai da rikicin.
''Muna goyon bayan gangamin, saboda yana cikin yunƙurinmu na kare ƙasarmu, amma ba za mu lamunci tashin hankali ba, cikici ba zai magance matsalar ba...Abin baƙin ciki ne yadda wannan zanga-zanga ta koma tashin hankali'', in ji ta.
Hukumomin lardin da masana ala'ada sun yi alla wadai da naɗin a matsayin haramtacce da ya saɓa wa tsarin al'adun ƙasar.
An shirya wata ganawa tsakanin babban jami'in ofishin jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu da wakilan gwamnatin ƙasar ranar 8 ga watan Afrilu.
Abin da muka sani
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu bidiyoyi da suka yaɗu a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda rikicin ya yi ƙamari har ma da ƙona dunkiyoyi.
Bikin naɗin ya yaɗu a shafukan sada zumunta, yayin da wata ƙungiyar masu riƙe da sarautun gargajiya suka ce ya saɓa wa dokokin sarautar yankin, wanda tunin yake da jagora.
Shugaban ƙungiyar masu riƙe da sarautun gargajiya na gabashin Cape, Nkosi Mpumalanga Gwadiso ya faɗa jaridar ƙasar cewa yankin na ƙarƙashin gundumar amaRharbabe, wanda ke ƙarƙashin ikon Sarki Sandile.
Kafar yaɗa labaran ƙasar, SABC ta bayar da rahoton cewa ƙungiyoyin bayar da agaji na birnin KuGompo da mazauna gabashin Cape ne suka taru a kan titu don yin zanag-zanga kan abin, kuma sashen kula da ƙungiyoyi da masarautun gargajiya na gwamnatin ƙasar ya yi alla wadai da lamarin.
Duka wannan na faruwa ne yayin da ƙungiyar ƴan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu ke ƙokarin fayyace abin da naɗin Sarkin ƴan Najeriya a gabashin London ke nufi.
Sun ce naɗin na jeka-na-yi-ka ne wanda zai taimaka wajen kare al'adun ƴan Najeriya mazauna ƙetare, wanda ba zai shafi dokokin hukumomin Afirka ta Kudu ba, a cewar rahoton SABC.
Shugaban ƙungiyar, Nwobi Smart ya ce ''wannan mai kare al'adun zai yi aiki a matsayin ɗan tsakiya tsakanin hukumomin ƙasar da ƴan Najeriyar da ke zaune a wannan yankin''.
Ya ƙara da cewa ''irin waɗannan wakilan ne ke sanya baki idan aka samu hari a wuraren da ƴan Najeriya ke zaune.''
Martanin gwamnatin Najeriya
Ofishin jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu ya mayar da martani kan rikicin da ya ɓarke maia laƙa da naɗa wani ɗan ƙabilar Igbo muƙami a gabashin birnin Cape na Afirka ta Kudu a ranar Litinin.
A lokacin wata hira da kafar yaɗa laban SABC, lokacin da yake yi wa masu zanga-zanga a ofishin jakadancin jawabi, wakilin mataimakin babban jami'in ofishin jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu, ya ce ƴan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu masu bi dokokin ƙasar ne kuma ba sa nufin tayar da hankali a Afirka ta Kudu.
Ya ƙara da cewa ƴan Najeriya abokan Afirka ta kudu ne, kuma ko a lokacin yaƙi da mulkin wariyar launin fata ƴan Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen goyon bayan al'ummar Afirka ta Kudu.
Jami'in ofishin jakadancin ya nemi afuwar hukumomin Afirka ta Kudu, yayin da ya dage cewa Najeriya ba ta da nufin kawo cikas ko tashin hankali a Afirka ta Kudun.
"Najeriya ƙasa ce mai bin doka, mai biyayya ga dokokin kowace ƙasa, don haka Najeriya ba ta da nufin tayar da rikici a Afirka ta Kudu,,' in ji shi.
"Abin takaici ne yadda wanna al'amari ya faru, amma ina mai tabbatar muku Najeriya ba ta da niyyar tayar da hankali a Afirka ta Kudu.''
"Abin da zan nanata muku shi ne Najeriya ƙawar Afirkat Kudu ce, ku je ku bincika tarihi, duka muna da muradin ci gaban Afirka ta Kudu, don haka ba za mu goyin bayan duk abin da zai kawo nakasu ga wannan ba, da haka nake neman afuwar hukukomin Afirka ta Kudu.''
Tuni dai gwamnatain Najeriya ta shawarci ƴan ƙasarta mazauna Afirka ta Kudu su taƙaita zirga-zirga tare da kauce wa shiga taron jama'a yayin da har yanzu ake cikin zaman ɗarɗar.
Ofishin jakadancin ƙasar da ke birnin Pretoria, wanda ya bayar da shawarar a ranar Litinin da daddare ya gargaɗin ƴan Najeriya su kauce wa duk wani rikici da zai iya tayar da hankali a ƙasar.
gargaɗin na zuwa ne bayan samun zanga-zanga a gabashin birnin Cape na yankin KuGompo da a baya aka fi sani da Gabashin Landan.







