Gwamnatin APC ke kunna wutar rikici a jam'iyyun adawa - ADC

Jagororin ADC

Asalin hoton, Peter Obi/Facebook

Lokacin karatu: Minti 3

Jama'iyyar hamayya ta ADC a Najeriya ta yi watsi da matakin da hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗauka na cire sunan Sanata David Mark da sauran ƴan kwamitin zartarwar ta daga shafinta na yanar gizo.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, INEC ta ce ta ɗauki matakin hakan ne sakamakon hukuncin kotun ƙoli da kuma shari'ar da ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja dangane da rikicin da ake yi tsakanin ɓangarori biyu wato David Mark da na Nafi'u Gombe.

A wani hukunci da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar 12 ga watan Maris ɗin 2026, kotun ta nemi dukkannin ɓangarorin da su jira hukuncin babbar kotun tarayya.

Hukumar ta zaɓe ta ce sakamakon hukuncin na kotun ɗaukaka ƙarar ne ta karɓi ƙorafe-ƙorafe daga lauyoyin ɓangarorin biyu masu taƙaddama da juna a kotu, inda ɓangaren David Mark ya nemi ka da ta amince da ɓangaren Nafi'u Gombe sannan shi ma lauyoyin Gombe suka nemi a cire sunan David Mark daga na'urarta ta jerin shugabannin jam'iyyun da INEC ta amince da su.

Faisal Kabir, jami'i ne a ofishin watsa labarai na jama'iyyar ta ADC bangaren David Mark, ya kuma shaidawa BBC cewa dama tun a ranar Talata suka fitar da sanarwa cewa ''akwai wasu mutane a cikin wannan gwamnatin ta APC sun matsa wa shugaban hukumar zaɓe ka dolen dole sai ya kawo cikas a cikin shugabancin jam'iyyar ADC.''

Ya yi zargin cewa masu wannan matsin lamaba ga shugaban hukumar zaɓen sun yi nasarar shawo kansa bayan ɗaukar lokaci ana kai-komo, shiyasa har ya amince da cewa a yanzu ba zai yarda da shugabancin dukkan ɓangaroin biyu ba, har zuwa lokacin da za a kammala shari'a.

''tun daga lokacin da aka ga mutane suna tururuwa suna shiga wannan jam'iyya tamu ta ADC, hankalin gwamnatin Tinubu ya tashi, ta san cewa ƴan Najeriya ba za su bari ta tsallake shekarar 2027 ba, duba da halin da suka sa Najeriya a ciki. Don haka wannan firgici ne da tsoro ya sa gwamnati ke ƙoƙarin lallai sai shugaba Tinubu ya rasa wanda zai kara da shi a zaɓen 2027.'' In ji Faisal Kabir.

Rikicin shugabancin jam'iyyar ADC ya kunno kai ne a watan Yulin 2025 lokacin da shugabannin jam'iyyar suka yi murabus, kuma David Mark ya zamo sabon shugaba na riƙon ƙwarya, inda aka zaɓi sauran ƴan kwamitin zartarwa babu hamayya.

Sai dai kuma tsohon mataimakin jam'iyyar, Nafi'u Gombe ya ƙalubalanci zaɓen inda ya dage cewa dole ne a samar da shugabanci ta hanyar da kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tsara.

Ya kuma garzaya kotu yana neman ta ayyana shi a matsayin shugaban ADC saboda a lokacin da shugabanninta suka yi murabus shi kadai ya rage, kuma a matsayin mataimakin shugaba mai baring ado, shi kundin mulki ya bai wa damar ɗarewa shugabancin kai tsaye.

Wane mataki ADC za ta ɗauka?

Yanzu haka dai ɓangaren David Mark na jam'iyyar ADC ya yi kira ga magoya bayan shi su kwantar da hankali yayin da jagororin su ke tattaunawa domin neman mafita.

Faisal Kabir ya ce ''wannan nasara ce, wannan ƙarfin gwiwa zai ƙara mana, kuma zai ƙara haɗa kan jagororinmu, kuma muna aiki tuƙuru domin tattabatar da cewa nan da ɗan lokaci kaɗan za mu faɗa masu mataki na gaba,''

Ya ƙara da cewa a yanzu ƙofar su a buɗe take domin zaƙulo mafita kan wannan batu, da kuma tabbatar da cewa sun kawar da gwamnatin APC a 2027.

''Tun bayan zaɓen 202, wannan gwamnatin tun da ta zo kan mulki babu abin da ta mayar da hankali sai tabatar da cewa ta rusa jam'iyyun adawa. An rusa SDP, an rusa Labour an rusa jam'iyyar NNPP, an rusa PDP, yau kuma gashi jam'iyyar ADC wadda ita kaɗai ƴan Najeriya ke fatan ta ceto su, itama ana ƙoƙarin sai an rusa ta,'' in ji Faisal Kabir.