City na son Anderson, United na harin Tonali, Liverpool za ta ɗauko Conceicao

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta shiga gaban Manchester United a yuƙurin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Nottingham Forest Elliot Anderson, kafin fara buga gasar cin kofin duniya. (Mail - subscription required)
Manchester United ta sami ƙarfin guiwa ɗauko ɗan wasan tsakiyar Italiya Sandro Tonali, yayin da Newcastle ta buɗe ƙofar siyar da ƴan wasanta, a farashi mai kyau a wannan kakar. (Sun)
Liverpool na son siyen ɗan wasan Portugal da Juventus Francisco Conceicao, a mastyin wanda zai maye gurbin Mohamed Salah, idan ya bar ƙungiyar a ƙarshen kakar nan. (Gazzetta - in Italian)
Manchester United na cikin ƙungiyoyi da ke son ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Brazil Joao Gomes, da zai iya kasancewa a kasuwa kan fam miliyan 39 idan har Wolves ta faɗa a gasar Premier. (Caught Offside)
Manchester United na harin siyen ɗan wasan bayan Toulouse da Ingila Charlie Cresswell a wannan kaka. (Teamtalk)
Bayern Munich ba su da sha'awar siyen ɗan wasan tsakiyar Ingila Phil Foden daga Manchester City saboda basu da kuɗin da za su iya siyen sa a wannan kakar. (Bild - in German)
Ɗan wasan gaban Netherlands Joshua Zirkzee, na son ci gaba da zama a Manchester United a kaka mai zuwa, saboda fatan da yake na zai samu damaidan har Michael Carrick, ya kasancewa wanda zai ci gaba da horar da yan wasan ƙungiyar. (Mail - subscription required)
Arsenal da Manchester City ne wadan da suka fi nuna son ɗaukar ɗan wasan Igila da Newcastle Tino Livramento idan ya yaƙi sabunta kwantaraginsa da Newcastle. (Football Insider)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Villarrael na son ɗan wasan Crystal Palace Ismaila Sarr a wannan kaka. (Fichajes - in Spanish)
Nico Schlotterbeck ya musanta shiga kwantaragi da Borussia Dortmund, wanda hakan ya baiwa Real Madrid sabon fata na damar ɗaukar ɗan wasan. (AS - in Spanish)
Ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, da ke taka leda a matsayin ɗan wasan aro a Barcelona, na cikin ƴan wasa biyar da za su bar Manchester united a wannan kaka, inda United ɗin ke fatan samun fam miliyan ɗari idan ta siyar su. (Sky Sports)
Barcelona na son ɗan wasan Benfica Andreas Schjelderup a matsayin wadan zai maye Rashforda a mastayin ɗan wasan ƙungiyar na din-din-din, bayan Rashford ɗin ya kamala zama amatsayin ɗan wasan Aro daga Manchester United a wannan kaka. (Record - in Portuguese, subscription required)
Ɗan wasan gaban Faransa Hugo Ekitike ya shiga jerin ƴan wasan da ke gaba da Real Madrid ke son sauka ganin irin ƙwazon da dan wasan yayi a wannan kaka a Liverpool. (Teamtalk)










