Abin da ya sa Trump ya bar Pakistan ta zamo mai shiga tsakani a yaƙin Iran

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Pakistan ya jima tana ƙoƙarin mayar d akanta mai shiga tsakani a yaƙin Iran
    • Marubuci, Caroline Davies
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Pakistan Correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 5

Matsayin da Pakistan ta samu na mai shiga tsakani a yaƙin Iran ya zo wa mutane da dama da mamaki.

Amma kuma bai kamata ya bayar da mamaki ba.

Shugaban rundunar sojin ƙasar, Field Marshall Asim Munir, na cikin ƴan lelen Shugaba Donald Trump na Amurka.

A baya-bayan nan shugaban na Amurka ya bayyana shi a matsayin ''wanda ya fi jin daɗinsa'' inda a baya ya riƙa magana kan yadda Munir ya san Iran ''fiye da mafi yawan mutane''.

Ba Iran ce kaɗai maƙwabciyar Pakistan ba, wadda suka hadu kan iyakar da ta kai tazarar kilomita 900, kuma suke da ''fahimtar juna'' da al'adu da addini iri guda.

Pakistan ba ta da sansanin sojin Amurka a cikinta.

Kuma ba kamar sauran masu shiga tsakani ba a yankin Gulf ba har yanzu ba ta shiga cikin rikicin ba.

Wani muhimmin abu shi ne ƙasar na son shiga tsakani ne don samar da zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran, kuma bisa ga dukkan alamu hakan zai yi wa ƙasar amfani.

Haka kuma har yanzu akwai tambayoyin da ake yi game da ta yaya ƙasar da ke faɗa da maƙwabtanta biyu - Afghanistan da Indiya - za ta zama mai shiga tsakani a rikicin wasu.

Yanzu haka ƙasar na faɗa da ƙungiyar Afghanistan sannan tana tana zaman doya da manja da Indiya, lamarin da a shekarar da ta gabata ya haifar da fargabar bazuwar makaman nukiliya.

Kawo yanzu Pakistan ta yi tayin shiga tsakani ga ƙasashen Amurka da Iran, inda ta aike musu da saƙonnin tayin a hukumance, sannan ta karɓi baƙuncin tattaunawar ministocin ƙasashen Musulmi tare da tattaunawar diplomasiyya da wasu ta wayar.

To sai daidaita ƙasashen biyu abun fargaba ne.

Asarar da za a yi

Pakistan ta dogara da shigo da man da take amfani da shi daga ƙetare, kuma mafi yawansa na zuwa ne ta mashigar Hormuz.

"Pakistan, kamar yadda na ke faɗa , fiye da kowace ƙasa da ke yankin Gabas ta Tsakiya na da rawar da za ta taka,'' a cewar Michael Kugelman, mai sharhi a majalisar yankin Kudancin Asiya da Atalantika.

"Ta na da muradin yin duk mai yiwuwa don kawo ƙarshen yaƙin.''

Gwamnatin Pakistan ta fara farashin man fetur da na disel da kusan kashi 20 a farko watan Maris kuma tuni ta gabatar da matakan rage raɗaɗi da suka haɗa da rage wa ma'aikatan gwamnati kwanakin zuwa aiki zuwa huɗu a mako, domin tattalin kuɗin mai.

"Idan yaƙin ya ci gaba, Matsin tattalin arziki a Pakistan zai ƙaru matuƙa,'' a cewar Farfesa Farhan Siddiqi, mai sharhi kan al'amuran siyasa a cibiyar huldar kasuwanci da ke Karachi.

.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Akwia kuma fargabar abin da ci gaba da yaƙin zai iya haifarwa.

A watan Satumban da ya gabata, Pakistan ta sanya hannu kan yarjejniyar tsaro da Saudiyya, wadda ta ƙunshi, duk wani hari kan ɗaya daga cikin ƙasashen , za a ɗauke shi kan hari ƙasashen biyu''.

Hakan ya san mutane tambayar ko Pakistan za ta shiga yaƙin idan Saudiyya ta shiga.

"Matsalarmu ita ce idan aka ce mun shiga yaƙin ta ɓangaren Saudiyya, gaba ɗaya kan iyakarmu ta yamma zai kasance ba ta da tsaro,'' a cewar Siddiqi.

Tuni dai Pakistan ta ''shiga yaƙin'' da Afghanistan, ta zargi ƙungiyar Taliban da ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ta'addanci a cikin ƙasarta, zargin da gwmanatin Taliban ta musanta.

Wani abu zai sake faruwa

A ranar da aka kashe jaogan addinin Iran a hare-haren Amurka da Isra'ila, magoya bayan Iran sun yi zanga-zangar a titunan biranen Pakistan, inda aka kashe da dama daga cikinsu, ciki har da waɗanda suka far wa ofishin jakadancin Amurka da ke Karachi.

Akwai kuma batun matsayar Pakistan a idanun duniya.

Kugelman ya ce "Pakistan na matuƙar kula da sukar da ake yi mata cewa ba ta da tasiri a duniya."

"Wannan muhimmin ci gaba ne ta fuskar diplomasiyya,'' a cewa Maleeha Lodhi, tsohuwar jakadiyar Pakistan a Amurka da Birtaniya da kuma MDD.

.

Asalin hoton, Turkish Foreign Ministry / Handout/Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif (tsakiya) ya karɓi baƙuncin ministocin harkokin wajen Masar da Turkiyya da kuma Saudiyya kan tattauna kawo ƙarshen yaƙin Iran.

"Za a kallai Pakistan a matsayin wadda ta yi wannan yunƙuri da kyakkyawar manufa, kuma ko da ba ta samu nasara ba, ba za a alaƙanta hakan da rashin ƙwarewarta ba, sai don rashin daidaitawar ɓangarorin biyu.''

Haka kuma, Kugelman na ganin cewa akwai ƙaranta ga Pakistan, idan har bayan duka wannan jita-jitar ɓangaroroin biyu suka koma yaƙin da karfinsu.

"Pakistan na iya gamuwa da zarge-zargen cewa ba da gaske take ba a wannan yunƙuri nata," in ji shi.

'Taka rawar diplomasiyya mai wahala'

Ba a san me zai faru ba, amma abin da yake ƙarara shi ne Pakistan na sauyin amfani da damar da take da ita na kyakkywar alaƙa da Trump.

Lodhi ya kafa hujja da naɗa Trump da Pakistan ta yi a matsayin ɗan takararta na gwarzon zaman lafiya na duniya domin samun kyautar 'Nobel Peace Prize'

Ta yi hakan ne domin nuna jin daɗinta game da yunƙurinsa na shiga tsakani lokacin rikicin Pakistan da Indiya a 2025.

"Pakistan ta sadaukar da nasarar ga Trump, inda hakan ya ƙara kyautata alakarsu'', in ji Lodhi.

.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Magoya bayan Iran sun gudanar da zanga-zanga a Pakistan bayan kisan jagoran addinin Iran
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai alaƙarta da Amurka, ba Pakistan kaɗai ke amfana ba.

Siddiqi ya ce, "Pakistan ta fahimci cewa martaba juna ce hanya mafi dacewa ta gudanar da harkokin diflomasiyya a yankin."

"Irin duniyar da muke fuskanta a yanzu ita ce duniyar da ƙasashe, musamman ma masu matsakaicin ƙarfi, ke amfani da manufofin manyan ƙasashe don ƙulla alaƙa da ƙasashe da yawa."

"Ina ganin dalilin da ya sa Pakistan ta fi dacewa ta yi magana da Iran shi ne saboda ba ta da ra'ayin kasancewa mai goyon bayan Isra'ila ko ma nuna goyon bayan Amurka sosai."

Yanzu haka dai ana ci gaba da tattaunawa.

A ranar talata, Ministan harkokin wajen Pakistan, Ishaq Dar ya yi tafiya zuwa China domin amsa gayyatar takwaransa na Chinan, Wang Yi.

Amma akwai manyan tambayoyi ga Pakistan, kuma samun damar ƙulla yarjejeniyar abu ne da ta jima tana so.

Kugelman ya ƙara da cewa, "Idan za mu fayyace abin a sarari, yiwuwar ƙulla yarjejeniyar na da wahala, idan aka yi la'akari da irin rashin amincewar da ke tsakanin Amurkawa da Iraniyawa da kuma irin girman buƙatun da Amurka da ɓangaren Iran suka yi."

"Ina tunanin da wahala Pakistan ta iya warware wannan rikicin ta hanyar, don haka yana da kyau ƙasar ta sake nazarin shirin da ta yi."