Dangote zai gina kamfanin siminti a Nijar

Mutumin da yafi kowa arziki a Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya ce zai gina katafaren kamfanin simitin a Jamhuriyar Nijar.
A cewarsa, kamfanin zai samar da tan miliyan daya da rabi na siminti a kowacce shekara.
Dangote a wata hira da wakilinmu Baro Arzika a Yamai bayan ganawarsa da shugaban Nijar, Alhaji Muhammadou Issoufou, ya ce zai kashe kusan dalar Amurka miliyan 350 wajen ginan kamfanin.
Ana saran kamfanin wanda za a kamallashi cikin shekaru biyu masu zuwa, zai samar da dubban ayyukan ga 'yan Nijar.
Alhaji Aliko Dangote kuma ya yi alkawarin gina asibiti da makarantu a yankunan da zai gina kamfanin.







