'Abin da ya sa na yanke shawarar ƙin yin aure' - Yadda wasu matan Najeriya suka 'boƙare'

Hoton wata mata mai suna Susan.
    • Marubuci, Helen Oyibo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin
  • Lokacin karatu: Minti 5

Susan Imaibehe Ekpoh na ɗaya daga cikin matan Najeriya kalilan da ke aikin tuka jirgin sama. Tana zaune a Abuja, babban birnin Najeriya.

Ta fara sha'awar jiragen sama ne tun tana karama, lokacin da ita da mahaifiyarta suka shiga jirgi tana da shekara takwas. Akwai abin da ta gani wanda ya kasa fita cikin ranta.

Daba baya burin Susan ya cika na zama matukin jirgin sama. A matsayinta na mai tuka jirgin sama, aikinta na buƙatarta na tsawon sa'a 27 lokacin da take aiki, idan kuma jirgi ya tashi dole duka hankalinta ya koma kan abin da take yi.

Susan ta bayyana abin da ta fuskanta lokacin da ta fara tuka jirgi: "Tuka jirgin sama a matsayina na mace shi ne wani abu mafi farin ciki da ya taɓa samu na, ina son aikin sosai, yana da kalubale ga kuma gajiya."

Shiga harkar da maza suka fi mamaya shi ma wani abu ne na daban a gare ta, sai kuma ta yanke shawarar cewa ba za ta haihu ba.

A al'ummomin Najeriya, ana cewa mace ta kai cikakkiyar mace ne lokacin da ta yi aure ta haihu, sai dai a yanzu ana ƙara samun mata a faɗin Najeriya waɗanda ke zaɓar kin haihuwa, ba wai saboda ba sa haihuwa ba, kawai saboda ba su son yara.

Susan mai shekara 30 na cikin irin waɗannan mata. Ta ce zama uwa shi ne aikin da ya fi wahala a duniya kuma mutum ba zai iya yin aikin da ya dace ba idan ba wanda ya tsara yi ba, ko kuma wanda kake mutuwar so.

Ta ƙara da cewa ba ta yanke shawarar kin haihuwa saboda irin yanayin aikin da take yi ba, inda ta ce akwai mata masu tuka jirgin sama waɗanda suka haihu - sai dalilinta daban ne.

"Ba abu ɗaya bane ya faru ya sa na ce ba zan haihu ba. Yanayin rayuwata ne, zaɓuka da na yi wa kaina, da irin rayuwar da nake son yi, su ne suka saka na ga babu ta inda batun haihuwa zai shigo."

Susan Ekpoh.

Asalin hoton, Susan Ekpoh

Bayanan hoto, Susan Ekpoh ta ce aikinta na tuka jirgin sama shi ya fi cin lokacinta amma ba shi ne dalilin da ya sa ta ce ba za ta haihu ba.

Duk da cewa Susan na samun goyon bayan iyalanta, ta ce matakin da ta ɗauka ya shafi rayuwar soyayyarta

"Na yi imanin cewa ba ka isa ka tilasta mutum yin abin da ba ya so ba, saboda ta haka ne ɓacin-rai ke fara wa. Ba zan bi wanda ke son yaro ba in ce zan canza masa ra'ayi, ni ma kada wani ya ce zai min katsalanda. Abu mafi muhimmanci shi ne za mu daidaita."

"Kofa ta a buɗe take wajen yin soyayya da kuma aure, amma ba zan bar rayuwata haka kawai in ce sai hakan ya faru ba. Idan Allah ya kaddara hakan abu mai kyau ne. Idan kuma ban samu wanda ra'ayin ya zo ɗaya ba, ba zan damu ba.

"Ƙulla alaƙa ba sai tsakanin miji da mata ba, na gina rayuwatan ta yadda ina da ɗimbin mutane, abokai da kuma ƴan uwan waɗanda ra'ayinmu ya zo ɗaya. Muna son ingantaccen rayuwa. Muna son gina rayuwarmu."

Susan.
Bayanan hoto, Susan ta ce farin cikinta shi ne damar zaɓar abin da take so

Jennifer na aiki da ɗaya daga cikin kamfanonin fasaha da ke birnin Lagos.

Ita kuwa, matakin da ta ɗauka na kin haihuwa shi ne saboda abin da ta fuskanta lokacin girmanta a matsayinta na ƴar fari, da kuma yanayin zamantakewa da tsadar rayuwa.

"Na tashi a gidan da akwai matsaloli nan da can. Ina ganin ƴar uwata da kuma mahaifiyata da irin ɗawainiyar da ke kaina matsayin ƴar fari. Hakan da na gani ne ya sa na ce ba zan haihu ba, ba ni da wannan ƙarfi."

Jennifer ta ce mahaifiyarta na ci gaba da ba ta shawara ta sauya tunaninta.

"Mahaifiyata tana faɗan cewa waye zai kula da ke idan kin tsufa, maganar gaskiya ina tuna hakan amma idan na hau shafukan sada zumunta, na zo na ci karo da irin matan da ke da ra'yi irin nawa waɗanda suka kai shekara 50 kuma suke rayuwa lafiya, sai in ce ni ma rayuwata za ta yi kyau muddin na tsara ta yadda ya dace."

Jennifer.
Bayanan hoto, Jennifer ta ce tana shakkun matakin da ta ɗauka wasu lokuta amma tana ganin matan da suka girme ta kuma suka yi irin zaɓinta suna rayuwa cikin farin ciki.

'Babu da na-sani'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ga Destiny Udey ƴar shekara 41 wadda ta yi aure, ta ce rayuwarta daban take.

Ta ce ta kasance tana tambaya a asirce na tsawon lokaci me ya sa za ta haihu, amma bayan aurenta da ta fuskanci ɓarin ciki daga nan ne ta samu ƙwarin gwiwar fitowa ta yi maganar cewa ba ta son yara.

"Na ɗauki ciki a 2021, ina tuna cewa lokacin da na gano ina da cikin mutane sun yi ta ba ni shawarar cewa in bar cikin, amma lokacin da yaron bai zo da rai ba, shi ne na fito na faɗa wa ƙawayena, ƴan uwana da kuma surukaina."

Destiny ta ce mijinta, mahaifiyarta da kuma surukanta sun goyi bayan matakin da ta ɗauka duk da cewa wasu ƴan uwa da kuma ƙawayenta sun ki amincewa da haka.

"Mun amince tsakaninmu kafin mu yi aure cewa ba dole bane sai mun haihu. Don haka lokacin da na yanke shawarar cewa ba zan haihu ba, mijina ya tambaye ni ko da gaske nake yi. Ya ce hakan ba matsala bane a wajensa."

Destiny ta ce ba ta jin ƙunyar magana kan zaɓin da ta yi wa kanta a shafukan sada zumunta.

"Ina farin ciki cewa ina rayuwa yadda na zaɓa wa kaina. Ina nunawa wasu mata cewa za su iya zaɓan abin da suke so kuma su yi rayuwa cikin farin ciki, hakan yana saka ni jin daɗi."

Destiny.

Asalin hoton, Destiny Udeh

Bayanan hoto, Destiny ta ce mijinta ya goyi bayan matakinta na kin haihuwa.

'Babu hanyar zama mace da ta fi wannan'

Ga Abiola Akiyode-Afolabi wadda ta kasance cikin waɗanda suka assasa cibiyar mata ta Women Advocates Research and Doc Center (WARDC), ta ce suna jin labarai da yawa irin waɗannan saboda lokaci na sauyawa kuma al'amura ba su yadda suke irin na zamanin baya.

"Muna ganin ƙaruwar matan da ke yin fice a ayyukan da maza suka fi yawa, wanda abu ne da ba za a iya yi shekaru da yawa da suka wuce. Muna cikin zamani na mata masu ilimi waɗanda ke dogaro da kansu, kuma waɗanda aka sani a duniya. A wajensu, aure da haihuwa sun zama wani zaɓi ne, ba dole ba kuma kafofin sada zumunta sun taka rawa wajen tabbatuwar hakan."

Akiyode-Afolabi ta ce sauyin ba zai haka kawai saboda akwai mata da yawa da suka fuskanci kalubale kafin cimma abin da suke so, musamman waɗanda ke da iyalai da yawa.

Duk da cewa matan da ba son samun yara su suka fi ƙaranci, ɗaya daga cikin rashin fahimta da al'umma ta yi musu shi ne cewa sun fi son kansu, ba su cika mata ba kuma su raunana.

A cewar asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, Unicef, kusan jarirai miliyan bakwai ne ake haihuwa a Najeriya a kowace shekara, abin da ya saka zajeriya cikin sahun masu ba da gudummawar ƙaruwar al'umma a duniya.