Matar Jega tsohon shugaban INEC ta rasu

Asalin hoton, Jega X
Matar tsohon shugaban hukumar zaɓen Najeriya INEC, Farfesa Attahiru Jega ta rasu.
Cikin wata sanarwa da iyalanta suka fitar a yau Lahadi, sun tabbatar da mutuwar ta ta, kuma tuni aka yi jana'izarta a babban masallacin ƙasa da ke Abuja.
Gabanin mutuwarta Hajiya Hadiza Jega ta yi fice wajen taimakawa harkokin ilimi da ci gaban al'uma musamman a arewacin Najeriya.
Farfesa Jega wanda ya taɓa zama shugaban Jami'ar Bayero da ke Kano ya ce ya kaɗu da mutuwar mai ɗakin tasa tare da yi mata adduar dacewa da aljanna.











