Arsenal za ta yi gogayya da Liverpool wajen neman Gordon, Chelsea na son Barco

Anthony Gordon

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Anthony Gordon
Lokacin karatu: Minti 1

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na sha'awar daukar dan bayan Argentina Valentín Barco mai shekara 21 daga Strasbourg (Talksport).

Kungiyar Inter Milan na son golan Tottenham Hotspur, Guglielmo Vicario mai shekaru 29, domin zama zabinsu na farko a raga (CalcioMercato).

Kungiyar Liverpool na shirin kara daukar dan baya, inda ake sa ran za ta maida hankali kan dan wasan Italiya Marco Palestra mai shekaru 21 daga Atalanta a wannan bazara (CaughtOffside).

Manchester United na daga cikin kungiyoyin Premier League da ke bibiyar dan bayan Arewacin Ireland Tom Atcheson mai shekaru 19 na Blackburn Rovers (Teamtalk).

Sunderland na iya yunkurin daukar dan wasan tsakiya mai kai hari Sergio Arribas mai shekaru 24 daga Almeria, idan daraktan wasanni Florent Ghisolfi ya ci gaba da nuna sha'awarsa (Sport Witness).

Arsenal na shirin gogayya da Liverpool wajen daukar dan gaban Newcastle United Anthony Gordon mai shekaru 25 (Football Transfers).