Yaƙin Iran ya illata ƙasashen yankin Gulf, wane sauyi za a samu?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Luis Barrucho
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
An daɗe ana kallon yankin Gulf a matsayin wuri mai kwanciyar hankali da kuma burin jawo hankalin masu zuba jari daga manyan kamfanoni da kuma ƙwararrun ma'aikata zuwa cikinsu.
Yankin na Gulf - wanda ya ƙunshi ƙasashe irinsu Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Kuwait da Qatar da Oman da kuma Bahrain - ya zamanantar da filayen jiragen sama da kuma mayar da birane zuwa cibiyoyin yawon buɗe ido domin samun kuɗi.
Sai dai yaƙin Iran ya girgiza ƙasashen wannan yanki, yayin da Iran ɗin ke ci gaba da kai hare-haren makaman linzami da jirage marasa matuki kan sansanonin sojin Amurka a yankin, sai dai sun shafi fararen hula da kuma cibiyoyin makamashi.
Ƙasashe sun yi kokarin ganin al'amura sun lafa cikin gaggawa: alal misali, gwamantin Qatar ta kawo karshen batun aiki daga gida sannan ta sake buɗe jami'o'i. Sai dai wasu masana na ganin cewa, yayin da ƙasashen Gulf za su iya jure yaƙin, amma ya tilasta musu sake fasalin tsare-tsare.
'Ba za ka iya dakatar da hare-hare daga Iran ba saboda yanayin wurin da suke," in ji Alex Vatanka, jami'i a wata cibiya a Washigton. "Wannan ƙasashe sun faɗa cikin rikicin yanzu, suna ma sahun gaba-gaba a yaƙin da ba nasu ba kuma suna asara mai yawa ta ɓangaren tattalin arziki."
Ya ƙara da cewa "Ko da za su karar da kuɗinsu wajen fannin tsaro, Iran za ta iya kai hari cikin sauki saboda abubuwan da muka gani a cikin waɗannan ƙasashe - jarin biliyoyi da suka zuba na cikin haɗari a hannun Iran."

Ci gaba da riƙe iko
Yayin da ƙasashen Gulf ke cikin mawuyacin hali kan yaƙin da ake yi, ɗaya daga cikin sakamakon shi ne sabunta batun tsaro da Washington, in ji Dakta Ebtesam Al Ketbi, shugabar cibiyar tsare-tsare na UAE.
Ta ce ana tura ƙasashen Gulf zuwa "kusa da Amurka" - a gefe kuma kusa da Isra'ila - saboda buƙatar tsaro da suke nema cikin gaggawa". Sai dai ta jaddada cewa wannan na haɗin kai ne ba na aƙidu ba. "Suna cikin tsaka mai wuyar cewa ana son jefa su cikin yaƙin, waɗanda za a yi ta kai wa hari har su rasa ikonsu."
Vatanka ya yi gargaɗin cewa alaƙa ta tsaro na da iyaƙa - musamman game da yiwuwar kare Gulf daga wajen Amurka. Ya ce gwamnatocin ƙasashen Gulf sun gargaɗi Washington tun kafin fara rikicin kan barazanar yaɗuwarsa, amma yanzu su aka jefa cikin matsala.
"Trump ya shiga saboda Netanyahu sannan ya bijirewa ƙasashen Gulf," in ji shi "Sun san ba za a taɓa ba su kulawa irin wadda ake bai wa Isra'ila."
Ya ce siyasar cikin gida a Amurka na da cikas wajen irin iyaƙar da ta bai wa Washington na son kare ƙawayenta na Gulf a tsawon lokaci. "Shin Amurkawa na son ninƙa sansanonin sojinsu a yankin Gulf... ta ya za a yi hakan?
""Hakan ya saɓa wa ainihin hujjar gwagwarmayar Maga cewa irin waɗannan yaƙe-yaƙe da Amurka ke shiga a duniya na jefa ƙasar cikin yanayi mara kyau."
Mafita ta hanyar diflomasiyya

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ɓangarenta, Iran na matsa lamba kan ƙasashen Gulf wajen ganin sun zama ƴan ba-ruwan mu, in ji Vatanka. "Ministan harkokin wajen Iran na ƙorafin cewa babu ƙasa ɗaya daga yankin da ta yi Alla-wadai da hare-haren Amurka da Isra'ila kan Iran... Iran na faɗa musu cewa: 'Ku fita daga cikin wannan faɗa."
Ya ce gwamnatocin yankin Gulf na "fushi da Iran" suna kuma son kauce wa kai musu hari. Ya ce Ya ce dabararsu ita ce ta samar da wata kafa tare da kauce wa shiga ayyukan Amurka ko Isra'ila.
"Iran za ta saka rayuwa a waɗannan kasashe ya zama mai wahala ga mutane. Ɗaukacin zuri'arku za ta kasance cikin barazana," in jin shi.
Samar da mafita ta tsawon lokaci za ta kasance ta hanyar diflomasiyya, a cewar tsohon jami'in gwamnatin Kuwait Dr Bader Mousa Al Saif wanda yanzu malami ne a jami'ar Kuwait.
"Muna buƙatar sasanci da makwabtanmu," in ji shi. "Muna son tattaunawa da Iran kai-tsaye. Muna son samar da tsari na yadda za a tafiyar komai yadda ya dace."
Gurgunta ɓangaren tattalin arziki

Asalin hoton, Getty Images
Sauyin da yankin Gulf ya yi daga tattalin arzikin da ake samu a ɓangaren mai zuwa cibiyar yawon buɗe ido a duniya na daya daga cikin labaran da suka fi ɗaukar hankali a cikin shekaru goma da suka gaba ta.
Kwararru sun yi gargaɗin cewa ko da yaƙin ba zai ƙawar irin cigabar da aka samu ba, amma dai ta nuna irin raunin da ƙasashen ke da shi.
Al Ketbi ta ce tana sa ran ƙasashen Gulf za su ci gaba da zama "matsayin masu yawon buɗe" - amma za a samu ƙaruwar abubuwa", ciki har da hauhawar farashin abubuwa, inshora da kuma haɗari.
Ta ce sauyin zai fi dogaro ga gwamnatoci fiye da kamfanoni masu zaman kansu, kuma 'yan kasuwa na amfani da wasu dabaru na daban, kamar aiki daga cibiyoyi da yawa.
Ketbi ta ce a tsawon lokaci, waɗannan kasashe za su faɗaɗa waɗanda suke yin kasuwanci da su, musamman komawa ga China da kuma ƙawayen yankin "don kauce wa dogaro" da Amurka.
Shi ma Al Saif ya amince cewa ƙarfin arzikin yankin zai rage musu raɗaɗi, duk da cewa za a samu tsadar abubuwa.
Ya ƙara da cewa "A farkon shekara ta 2010, 2011, idan za a iya tunawa mun fuskanci zanga-zangar ƙasashen Larabawa, ta faru a yankin Gulf, kuma mun yi nasarar fita daga cikinta lafiya".
Ingantaccen tsaro
Wani sakamako mai ɗorewa bayan rikicin shi ne ƙarin haɗin kai da kuma ingantaccen tsaro na yankin Gulf, in ji masana.
Al Ketbi ta ce za a zuba jari wajen kariyar makaman linzami ta hanyar amfani da na'urorin ankararwa, jirage masara matuki da sauransu.
Shi kuma Al Saif ya ce "Muna buƙatar daidaita sayayyar mu, samun tsarin samar da abubuwa a yankin Gulf…Bugu da kari, tare da samar da makamaia cikin gida, wani tsari da zai kara inganta mu," in ji shi.
Sai dai batun gasa tsakanin kasashen zai janyo tsarkakiya kan wannan buri.
Vatanka ya ce "A zahiri wasu ƙasashen Gulf na gaba da juna kamar yadda suke yi da Iran".
Makoma mai taka tsantsan

Asalin hoton, EPA
Masana sun yi imanin cewa makomar yankin Gulf ba zai dogara kan Iran kadai ba, sai dai har ma da sauran harkokin yankin - ciki har da irin zaman tankiya tsakanin ƙasashen yankin Gulf da kansu.
"Kuskure ne cewa Iran ita ce ƙasa kaɗai da za ta janyo ruɗani a yankin," in ji Vatanka. "Waɗannan ƙasashe na da tarihin rashin haɗin kai maimakon haɗa-kai."
Sai dai masana sun ce yankin Gulf zai ci gaba da zama cibiyar buɗe ido a duniya, amma mai ingantaccen tsaro da taka tsantsan.
"Ba za a kawar da su ba - amma za a sake gyara su," in ji Al Ketbi. Ta kara da cewa, "Gulf zai zama mai juriya - amma mai taka tsantsan da kuma karfin soji," in ji ta.











