KAI TSAYE, Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da sauran batutuwan da ke faruwa a duniya 4/4/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da sauran batutuwan da ke faruwa a duniya 4/4/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Tarko INEC ke son naɗa mana kuma ba za mu kamu ba - ADC

    ADC

    Asalin hoton, ADC

    Jama'iyyar adawa ta ADC ta haɗakar ƴan adawar Najeriya ta zargi hukumar zaɓen ƙasae INEC ta naɗa mata tarko ta hanyar hanyar yunƙurin dakatar da ita daga gudanar tarukanta domin zaɓen shugabanninta.

    ADC - tsagin David Mark - ta jaddada aniyar ci gaba da tsare-tsarenta na gudanar da zaɓukan shugabanninta na jihohi da babban taron jam'iyyar na ƙasa, saɓanin gargaɗiin da hukumar zaɓen ƙasar ta yi, yayin da batun rikicin shugabanci ke ci gaba da munana a jam'iyyar

    A baya-bayan nan ne dai INEC ta gargaɗi jam'iyyar da kada ta gudanar da tarukan jam'iyyar da za su zaɓi shugabanninta don gudan Matsala.

    Cikin wata hira da gidan talbijin na Arise a ranar Juma'a shugaban hukumar Farfesa Joash Amupitan ya ce kotu ta riga ta dakatar da jam'iyyar daga gudanar da komai har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin jam'iyyar.

    Sai dai Kakakin jam'iyyar, Faisal Kabir ya shaida wa BBC cewa, mataki wata ƙualliya ce domin kafa wa jam'iyyar tarko a hana ta yin tarukan ta yadda daga baya za a ce ba ta da shugabanci, don haka ba za ta shiga zaɓen 2027 ba.

    ''Tarko aka kafa mana da wannan, ai su manyan tarukan jam'iyyu, wajibi ne a doka, kuma suna da lokacin yinsu, idan wannan lokacin ya ƙure shikenan'', in ji shi.

    Ya ƙara da cewa abin da dokokin Najeriya suka ce shi ne ka sanar da INEC taron jam'iyyarka kwana 21 kafin ranar taron, mu kuma mun sanar da ita.

  2. Amurka ta umarci babban hafsan sojin ƙasanta ya yi murabus

    Janar George

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren harkokin wajen Amurka, pete Hegseth ya umarci babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar, Janar Randy George ya sauka daga muƙaminsa, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CBS ƙawar hulɗar BBC a Amurka ta ruwaito.

    Kakakin ma'aikatar tsaron ƙasar, ta Pentagon Sean Parnell ya bayyana cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin sada zumunta cewa ''zai sauka daga matsayinnsa na babban hafsan sojin ƙasan Amurka na 41 ba tare da ɓata lokaci ba''.

    Kawo yanzu babu cikakken bayani kan dalilin da ya sa ake ce ya sauka daga muƙamin nasa ba.

    Matakin na na zuwa ne bayan da Shugaba Trump ya bayyana a wani jawabin da ya yi wa ƙasar cewa ana sa ran yaƙin Amurka da Isra'ila da kuma Iran a gefe guda ya kusa zuwa ƙarshe ''nan ba da jimawa ba''.

    A ƙa'ida babban hafsan sojin ƙasan Amurka kan yi wa'adin shekara huɗu.

    Toshon shugaban Amurka, Joe Biden ne ya naɗa George muƙamin a 2023.

    Janar George ya fara ya fara aiki da rundunar sojin Amurka ne bayan kammala karatu a makarantar horon manyan hafsoshin sojin ƙasar da ke West Point.

    Ya halarci yaƙin yankin Gulf na farko a matsayin kwamandan dakarun ƙasa, sannan a baya-bayan nan ya halraci yaƙe-yaƙen Afghanistan da Iraƙi.

    Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ce za a maye gurbinsa da mataimakinsa Janar Christopher LaNeve a matsayin riƙo.

  3. 'An raunata sojojin Amurka 365 da kisan 13 tun bayan fara yaƙin Iran'

    sojoji

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar tsaron Amurka tya Pentagon ta ce sojojin ƙasar 365 ne samu raunuka tun bayan fara yaƙin Amurka da Isra'iloa kan da kuma Iran a gefe guda.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce sojojin sun fito ne daga rundunoni daban-dban da suka haɗa da:

    • Sojojin kasa - 247
    • Sojojin ruwa - 63
    • Sojojin sama - 36
    • Dakarun ƙundunbala - 19

    Ma'aikatar ta kuma waɗanda suka mutu sakamakon yaƙin su 13 ne.

  4. Makaman rokar Iran sun faɗa tsakiyar Isra'ila

    makamai

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu makaman roka da Iran ta harba sun faɗa wasu yankuna masu cikowar jama'a a sassan tsakiyar Isra'ila da safiyar yau Asabar.

    Ma’aikatan agajin gaggawa sun garzaya zuwa wuraren da abin ya shafa a biranen Petah Tikva da Ramat Gan.

    Iran na ci gaba da kai hare-hare kan ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya, inda ma’aikatar harkokin cikin gida ta Bahrain ta buƙaci jama'a su nemi mafaka bayan na'urar gargadi ta yi kuwa a faɗin ƙasar.

    Tun da farko, wani wurin sarrafa iskar gas ya kama da wuta a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sakamakon tarkacen abubuwan da suka faɗo.

    Can ma a Kuwait, hare-haren da aka kai sun lalata tashoshin samar da lantarki da tace ruwan sha da kuma matatar mai.

  5. Amurka na neman mutum na biyu cikin matuƙan jirginta da Iran ta harbo

    jirgi

    Asalin hoton, ..

    Dakarun Amurka na can na ci gaba da neman mutum na biyu, cikin matukan jirgin yakin kasar na da Iran ta harbo jiya Juma'a.

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ƙi yin ƙarin bayani kan ƙoƙarin ceton, amma ya ce hakan ba zai shafi tattaunawar da ake yi da Iran ba.

    A nasu ɓangaren, hukumomi a Tehran sun buƙaci mazauna yankin da su taimaka wajen gano matuƙin jirgin, har ma suka yi alƙawarin bayar da lada mai tsoka ga duk wanda ya kai rahoton inda yake.

    A wani zama na sirri da ƴan majalisar dokokin Amurka, ma'aikatar tsaron ƙasar Pentagon ta ce an harbo jirgin yaƙin ƙirar F-15 ne a yankin kudu maso yammacin Iran, kuma an ceto ɗaya daga cikin matuƙansa, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman ɗayan.

    A wani ƙarin koma-bayan ga Amurka, Iran ta ce ta kakkaɓo mata jirgin yaƙi na biyu duk dai a wannan rana.

    Kafofin watsa labaran ƙasar sun ce Iran ɗin ta kakkaɓo jirgin ƙirar A-10, a kusa da mashigin Hormuz.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ta wayi gari.

    Ku biyu mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.