Yadda aka gicciye Yesu Almasihu a mahangar Kirista

Bayanan bidiyo, Muhimmancin ranar Good Friday a addinin Kirista
Lokacin karatu: Minti 5

Mabiya addinin Kirisita a fadin duniya kan gudanar da bukukuwan Easter duk shekara domin tunawa da gicciyewa da kuma tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu.

Bikin dai a kan fara shi ne tun daga dare irin na Alhamis zuwa wayewar garin Juma'a a kuma kammala a ranar Litinin ta gaba.

A tattaunawarsa da BBC, Rabaran Murtala Mati Dangora, mataimakin shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kano ya ce bukukuwan Easter sun kasu kashi biyu; akwai wanda ake kira Juma'a mai Tsarki wato ''Good Friday'', da kuma Easter Monday.

..

Asalin hoton, Getty Images

Rabaran Dangora ya kara da cewa "Juma'a mai Tsarki ko kuma ''Good Friday'' rana ce ta saduda, rana ce ta komawa ga Allah, rana ce ta tunani domin wahala da Yesu Almasihu ya sha a ranar."

"A ranar ne aka zartar masa da hukuncin kisa a bisa umarnin sarkin Pontius Bilatus a wancan zamani, a ranar ne sojojin Romawa suka gicciye shi, a ranar ne kuma ya mutu, a ranar ne kuma aka saka shi a kabari bayan da aka yi jana'izarsa," in ji shi.

Ya kuma ce: "Abin da aka bayyana a cikin littafin tsohon alkawari, cewa ya auku ne a rana ta uku da binne shi, bayan da Romawan suka gicciye shi a wani waje da ake kira Calvary ko kuma Golgotha da ke wajen birnin Kudus.''

Don haka in ji Reverend Dangora wannan rana ba ta shagali ba ce kawai, rana ce da ake son duk mabiya addinin Kirsita su yi wannan biki cikin neman salama.

"Duk lokacin da ranar Juma'a mai Tsarki ta kewayo mukan yi kira ga jama'a da su kasance cikin saduda, da komawa ga Allah, su zama ga tunanin cewa rai mai mutuwa ne, ko wane mai rai zai dandana mutuwa, don idan har Almasihu ya mutu ba wani mahaluki da ba zai mutu ba."

Yadda Yahuza ya ci amanar Yesu Almasihu

..

Asalin hoton, Getty Images

Rabaran Dangora ya dada yi wa BBC ƙarin bayani game da tarihin yadda aka gicciye Yesu Almasihu da cewa ɗaya daga cikin almajiransa da ake kira Yahuza shi ne ya ci amanarsa ya bayar da shi ga abokan gabansa.

"An fara wannan tun ranar Laraba zuwa Alhamis, har ya zuwa ranar Juma'a da aka zartar masa da hukunci, irin yadda Romawa ke yi wa wadanda suka aikata laifi," a cewarsa.

Ya kara da cewa "kodayake Yesu Almasihu ba wai ya aikata laifi ba ne amma ya dauki zunubanmu ne shi ya sa ya zama kamar laifi a gare shi, don haka sai aka saka ita ce a kafa masa kusa a hannuwa da kafa aka daga shi sama."

Wannan gicciyewar da aka yi masa a cewar malamin na Kirista, sai da ya shafe sa'oi uku zuwa hudu a kan gicciyen sannan aka bayyana cewa ya mutu, daga nan ne a cikin almajiransa akwai wani da ake kira Yusuf ya je ya roki alfarma wurin sarki cewa yana bukatar gangar jikin Yesu Almasihu zai yi masa jana'iza.

Yaya aka yi jana'izar Yesu?

..

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Yadda Yahudawa suke jana'iza ya bambanta da yadda mu muke yi, yayin da muke haka rami mu saka mutum, su kuma ko wane magidanci kan tanadi rami na saka duk wanda ya rasu, don haka dama Yesu Almasihu ya riga ya tanadi wannan rami da aka saka shi aka rufe, sannna aka saka masa hatimin hukuma.''

Malam Dangora ya ce saboda farkon kafa addinin Kirista ne don haka mabiya addinin ba su dauke shi da sauki ba, sun shiga damuwa sosai don lokacin da aka zo za a kama Yesu Almasihu daya daga cikin almajiransa Bitrus ya zaro takobi ya sari wani har ya cire masa kunne.

A cewarsa: "Yesu Almasihu ya ce, masa a'a Bitrus idan ina so zan iya umartar rundunar mala'iku su je su hallaka su amma yaki ba na nama da jini ba ne, don haka ka mayar da takobinka, don haka kashe shi ya zama cikar annabci ne."

Rabaran din ya kuma bayyana yadda mabiyan ke muhimmantar da wannan rana wajen yanka rago da zubar da jini wanda ke misalta Yesu don tunawa da 'yanci daga zunubi.

Ya kuma ce mabiyan kan bayar da kyaututtuka lokacin bikin Easter, in da ya ce kamar yadda aka saba a ko wane lokaci irin wannan yana yin kira ga mabiya addinin Kirista da su koma ga Allah su kuma rika yin azumi da neman tuba tare da yin la'akari da gudanar da harkokin rayuwa a kan tafarkin da Yesu Almasihu ya bar musu.

Me ya sa ake kiran ranar da aka gicciye Yesu 'Good Friday'?

..

Asalin hoton, Getty Images

''Good Friday'' ita ce ranar da mabiya addinin kirista ke tunawa da ranar da aka gicciye Yesu Almasihu.

To me ya sa ake kiran ta Juma'a mai kyau ko kuma Juma'a mai tsarki?

Littafin Injila ya ce an zane Yesu, aka tursasa masa daukar katakon da aka yi amfani da shi wajen gicciye shi, sannan aka kashe shi.

Babu wani abu mai kyau a cikin haka wanda zai sa a kira ranar a matsayin mai kyau, wato "good".

Wani bayanin na cewa rana ce mai kyau kasancewar ta rana mai tsarki. Wasu kuma na cewa an baddala kalmar "God's Friday" ne zuwa "Good Friday", wato daga "Ranar Allah" zuwa "Rana mai kyawu".

Sai dai babbar edita a wajen tsara kamusun turanci na Oxford English Dictionary, Fiona MacPherson, ta ce a al'adance Good Friday na nufin "wata rana ko lokaci da ake yin ayyuka na ibada".

Kamusun harshen Ingilishi na Oxford ya ce "abu mai kyau a nan na nufin lokacin da masu zuwa coci ke ayyukan addininsu", inda suke yi wa juna gaisuwar samun alkhairai, wato "good tide".

Baya ga Good Friday, akwai kuma ranar ''Good Wednesday'' wadda ba a cika magana a kanta ba, wadda ita ma ke nufin Larabar da ke zuwa gabanin ranar Easter.

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokaci na farko da aka san an fara amfani "goude friday" shi ne a wani littafi da ake kira 'The South English Legendary", wanda aka rubuta a wajajen shekarar 1290, kamar yadda kamusun ya nuna.

Shi kuwa littafin Baltimore Catechism - na mabiya Katolika a Amurka wanda ya samo asali daga shekarun 1885 zuwa 1960, ya ce ranar gicciye Yesu rana ce mai kyau kasancewar Yesu "ya bayyana matukar kaunarsa ga dan'adam tare da nemar masa dukkanin alhairai".

Babban kamusun mabiya Katolika, wanda aka fara wallafawa a shekarar 1907 ya bayyana cewa babu tabbas kan asalin sunan 'Good Friday.

Amma ya ce wasu majiyoyi sun ce sunan ya samo asali ne daga "God's Friday" ko kuma 'Gottes Freitag', sai dai wasu sun tsaya kan cewa ya samo asali ne daga 'Gute Freitag' na harshen Jamusanci.

Ya kuma bayyana cewa mutanen Anglo-Saxons sukan kira ta da 'Long Friday' wato doguwar rana.

Har wa yau babban kamusun ya ce ana kuma kiran ranar "rana mai tsarki kuma kasaitacciyar Juma'a" a harshen Girka.

Akan kira ta da "Juma'a mai tsarki" a harsunan Romance Languages. Akan kuma kira ta da Karfreitag (Ranar Alhini) a harshen Jamusanci.