Harin Amurka da Isra'ila ya kashe shugaban sashen leƙen asirin IRGC

Asalin hoton, Iranian state media
Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta tabbatar da mutuwar shugaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar, Majid Khademi.
Cikin wata sanarwa da rundunar IRGC ta fitar da safiyar yau Litinin ta zargi Isra'ila da Amurka da kai masa hari.
BBC ta tuntuɓi rundunar sojin Isra'ila, wadda ta ce za ta ''duba'' rahoton.
Khademi ne ya maye gurbin Mohammad Kazemi, wanda ya mutu a hare-haren Isra'ila ranar 15 ga watan Yunin 2025, lokacin yaƙin kwana 12 tsakanin Isra'ila da Iran.
A watan Fabrairun da ya wuce lokacin zanga-zangar ƙasar, Khademi ya zargi Shugaba Trump na Amurka da tunzura abinda jami'an Iran suka bayyana da kitsa dabarar ''kashe mutane'', da nufin kafa hujjar far wa ƙasar daga ƙetare.
A lokacin Khademi ya yi iƙirarin cewa fiye da jami'an leƙen asiri 10 daga ƙasashen waje, ciki har da sashen yaƙin Intanet na Isra'ila ne suka taka raw a kitsa zanga-zangar.
Wani kamfanin dillancin labarai na Amurka da ke gwagwarmayar kare haƙƙin bil'adama, ya ce aƙalla mutum 7,000 ne aka kashe a lokacin zanga-zangar ta watan Janairu.




