United za ta siyar da Ugarte, Vinicius na son komawa Ingila

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na duba yiwuwar saiyar da Manuel Ugarte, a wannan kaka, yayin da Newcastle, da Aston Villa da Juventus ke cikin jerin ƙungiyoyin da ke nuna sha'awar ɗaukarsa. (Caught Offside)
United, da Manchester City, da Chelsea da kuma Arsenal, na cikin ƙungiyoyin da aka tuntuɓa wajen ganin sun siyi ɗan wasan gaban Real Madrid Vinicius Junior. (Teamtalk)
Liverpool na iya cinikin ɗan wasan Al-Ahaly Marcus Leonardo da Mo Salah. (Give Me Sport)
Ɗan wasan tsakiyar Aston Villa Amadou Onana, zai iya samun babban tayi idan har ya bar kungiyar da ya ke taka leda, inda Manchester United ke cikin ƙungiyoyin da ke son ɗaukarsa. (Football Insider)
Ɗan wasan Tottenham Luka Vuskovic da ke Hamburg a mastyin dan wasan aro, na iya komawa ƙungiyar tasa duk kuwa da irin tayin da yake samun daga wasu mayan ƙungiyoyi da ke Turai. (The Standard)
Chelsea na iya siyen mai tsaron ragar Sunderland Robin Roefs, don maye gurbin mai tsaron ragar ta Robert Sanchez. (Teamtalk)
Bayer Leverkusen na iya tsawaita zaman ɗan wasan gabanta Yan Diomande, zuwa shekara mai zuwa, duk da ƙungiyoyin da ke ci gaba da nuna sha'awarsu na ɗaukar ɗan wasan. (Fabrizio Romano)







