Yadda ƴan Kenya ke rige-rigen ramewa - ko akwai illa?

Asalin hoton, Naomi Kuria/Facebook
A can baya, ana ganin duk wani mutum mai ƙiba a ƙasar Kenya a matsayin wanda ya tara hamshaƙan kuɗaɗe da samun kwanciyar hankali. Amma yanzu ƴanƙasar na rige-rigen nemo duk wata hanyar da za ta sa su rame.
Yawanci an fi amfani da tsarin yin tiyata ko shan magungunan rage kiɓa a ƴan tsakankanin nan, inda da yawancin fitattun mutane a ƙasar ke bayyana yadda suka samu nasarar rage kiɓa a shafukan sada zumunta.
Wasu na yabawa wasu kuma na kushewa.
Wata likita a ƙasar Kenya, Dr Lyudmila Shchukina, ta ce a ko da yaushe mutane na tururuwa zuwa wani ƙaramin asibitin ta a cikin gari don yin tiyatar rage kiɓa.
Sai dai ba haka lamarin yake a cibiyar ta da ke Nairobi ba, wadda suka kafa ita da marigayin mijinta shekaru 40 da suka gabata.
A lokacin da suka kafa cibiyar, ba su da kwatomomi duk da ita ce ta farko da ta fara tiyatar rage ƙiba a ƙasar, in ji Shchukina.
Amma a yanzu suna samun aƙalla mutum 10 zuwa 15 a kowace rana.
"Wannan babban ci gaba ne," kamar yadda likitar ta shaida wa BBC. Ana ganin matsin lamba daga al'umma mutane ke daukar wannan matakin.
Ba a san ƴan Kenya da nuƙu-nuƙu ba, inda ake yawan cin fuska ga maza da matan da suka ɗora hotunansu a shafukan sada zumunta. Wasu lokutan ana ce musu "ba ka yi ƙiba ba" a duk lokacin da suka ɗora hotunansu, abin da ke nufin "ka yi ƙiba" a kaikaice.
Wani ɗan gwagwarmayar siyasa Francis Gaitho, ya taɓa yin ƙorafin ana cin zarafina a shafukan sada zumunta saboda ƙibarsa, inda yawancin mutane ke tsokanarsa da cewa "ba ka yi ƙiba ba".
Shchukina ta ce damuwa da cin fuskar da ake yi wa masu ƙiba ce take sa mutanen ke zuwa cibiyarta.
Tana duba marasa lafiya da ke fama da hawan jini, rashin haihuwa, ciwon suga da masu ciwo baya, yayin da wasu ke zuwa saboda yanayin lafiyarsu.
Shchukina ta ce ƴan Kenya sun fara gane cewa ƙiba ba alamar kuɗi ba ce, rashin lafiya ce.
Ma'aikatan lafiya na ci gaba da nuna damuwa kan lamarin. A shekarar 2022, an yi ƙiyasin cewa yawancin mata da wasu maza suna fama da nauyin jiki ko ƙiba. A yankunan karkara ma, kaso 39 na mata da kaso 14 na maza na fama da lalurar.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai, wasu mutanen da ke zuwa wajen Shchukina, suna son inganta lafiyarsu ne da kuma gyara yadda surarsu ta ke.
Ta ce, a baya ana ganin yin ƙiba abin burgewa ce, amma yanzu kuma abin da ake yayi shi ne mutum ya zama siriri... Abubuwa na canzawa.
Wata ƙwararriya a fannin gyaran jiki da ado, Yvonne Kanyi, ta ce mata na shan matsin lamba domin su gyara surarsu da kuma rashin yin tumbi, duk da yake a baya ma ana samun hakan amma ba abu ne mai sauki ba
Kanyi, wadda ta ke da wajen kwalliya ne da gyaran jiki a Kenya, ta ce yanzu yanayin rayuwar fitattun mutane ta sauya, "inda suke neman magunguna da za su daidaita musu surar jikinsu."
Ta ƙara da cewa, yawancin mata a yanzu suna samun ƙwarin gwiwa kan yadda suke son surarsu ta kasance "ba tare wasu ƙorafe-ƙorafe ba," kamar yadda ta shaida wa BBC.
Ɗaya daga cikin irin waɗannan matan akwai Naomi Kuria, shahararriyar mai amfani da soshiyal midiya, wadda ta bi hanyar likitoci domin rage kiɓa da daidaita surarta, kuma tana alfahari da hakan.
Naomi mai shekaru 27 a duniya ta fara yunƙurin rage ƙiba ne tun a shekarar 2024.
Ta ce ta fara ne da zuwa wajen motsa jiki, ama bayan watanni biyar, ba ta samu abin da take so ba. A madadin rage ƙiba, sai ta ƙara ƙiba kuma gwiwoyin ta suka fara ciwo.
An kuma ba ta shawarar fara iyo, da kuma sauya tsarin cin abinci zuwa ganyayyaki, amma ta fi son abin da zai yi aiki cikin sauri.
"Sau nawa zan je wajen iyo domin ya rage ƙiba?" Shi ya sa ne nemo hanya mafi sauri, inda a nan ne na gano amfani da maganin Ozempic," in ji ta.
Ozempic na ɗaya daga cikin magungunan da ke taimaka wa mutane wajen rage ƙiba, kamar su Mounjaro da Wegovy.
Ana ba da allura a wasu lokutan da kuma wasu sinadaran daidaita tsarin cin abinci.

Asalin hoton, Naomi Kuria
Kuria ta ce allurar da aka yi mata, ta taimaka sosai wajen cika mafarkinta, inda ta rage kilo 11 a cikin wata ɗaya da rabi.
A Kenya dai, ana ba da maganin Ozempic a hukumance. Ta ce ta kashe kuɗin da ya kai shilling 80,000, kimanin dala $620 a kan magunguna.
Duk a yake ta fuskanci ƙalubalen "rikicewar ciki", amma ta jin daɗin abin da ya faru da ita, "saboda dukkanin surar jiki na ta bayyana".
Sai dai duk da haka, Kuria ta ce tana da burin ƙara rage ƙibar, ta hanyar wani tsarin tiyata, inda za a yanke wani sashe na tumbin ta a mayar da shi ƙafar ta da ba ta da ƙiba.
Ta ce ta sha shuka daga masoyanta saboda yadda ta koma, waɗanda ta ce ba su fahimci dalilinta na yin hakan ba.
An sha tambayar ta dalilin yin hakan, inda ta ce "surar jikinta ta yi kyau".
Sai dai Dr. Alvin Mondoh, wani ƙwararre a fannin rage ƙiba, ya ce "har yanzu mutane na buƙatar taimako" ta hanyar likitoci, saboda ƙiba zai iya wuce matakin da za a iya magancewa idan ba a ɗauki mataki ba.
Amma ya yi gargaɗi game da ƙaruwar masu amfani da allurar rage ƙiba.
"A ƴan tsakankanin nan, mutane na yawaan amfani da allura saboda wasu dalilai," in ji ta.
Akwai haɗari game da tsarin, saboda mutane ba sa neman shawarar ƙwararru da kuma amfani da abubuwa masu arha.
A cibiyar da ake yin wannan tiyatar a Nairobi, ana kuma ba da shawarwari ga waɗanda suke son rage ƙiba tun daga kan shilling 38,000, kimanin $300, har zuwa dubban daloli, lamarin da ya ke fin ƙarfin wasu ƴanƙasar.
A watan Agustan shekarar da ta gabata, hukumomin ƙasar sun gargaɗi al'umma su gujewa amfani da magungunan rage ƙiba.
An umurci wani fitaccen mai horaswa da motsa jiki a ƙasar ya daina tallata shafukan da mutane za su samu alluran rage ƙiba a farashi mai rahusa.
Sai dai yayin da yawan masu ƙiba ke ƙaruwa a Kenya, ba lallai a samu raguwar masu buƙatar rage ƙiba ba.











