Diomande zai maye gurbin Salah a Liverpool,Newcastle za ta sayar da Gordon

Yan Diomande

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yan Diomande
Lokacin karatu: Minti 2

Newcastle za ta sayar da Anthony Gordon, mai shekara 25, ga Bayern Munich,idan zakarun na Jamus sun iya biyan fam miliyan 75 a kan dan wasan gaban Ingila.(Times - subscription required), external

Manchester United, wacce ke neman siyan akalla 'yan wasan tsakiya biyu a kakar wasa ta bana, ta sanya ido sosai kan halin da dan wasan Faransa Aurelien Tchouameni, mai shekara 26 ke ciki, a Real Madrid.(Telegraph - subscription required), external

Dan wasan RB Leipzig da Ivory Coast Yan Diomande, mai shekara 19, shi ne wanda Liverpool ta ke son ta dauka domin maye gurbin dan wasan Masar Mohamed Salah, mai shekara 33, kuma shugabannin kungiyar sun amince da haka . (Florian Plettenberg - Sky Germany), external

Dan wasan Argentina Cristian Romero ya ja hankalin Atletico Madrid yayin da babu tabbas game da makomar dan wasan mai shekara 27 a Tottenham. (Caught Offside), external

Dan wasan Ingila Curtis Jones, mai shekara 25, bai ji dadin yadda yake taka leda a Liverpool ba kuma zai iya barin kungiyar a wannan bazara . (Football Insider), external

Manchester City da Liverpool na gab da rasa dan wasan bayan Italiya Alessandro Bastoni, saboda dan wasan mai shekara 27 ya shirya barin Inter Milan don zuwa Barcelona . (Mundo Deportivo - in Spanish), external

Liverpool na cikin kungiyoyin da ke sha'awar dan wasan Sunderland dan kasar Faransa Enzo le Fee, mai shekara 26.(Teamtalk), external

Chelsea ta tuntubi wakilin dan wasan Borussia Dortmund da Jamus Karim Adeyemi, mai shekara 24, kan yiwuwar kulla yarjejeniya da kungiyar.Fussballdaten - in German), external

Everton ce a kan gaba a kungiyoyin da ke son siyan dan wasan Middlesbrough Hayden Hackney mai shekara 23 a bazara.(Teamtalk), external

Ana sa ran dan wasan Ingila John Stones, mai shekara 31, zai bar Manchester City a bazara a matsayin dan wasan da ba shi da kwantaragi (Fabrizio Romano), external