Son yin takara ne a gaban 'yan ADC ba Najeriya ba - Shekarau

Asalin hoton, IBRAHIM SHEKARAU
Tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau, ya ce son yin takara ne a gaban jiga-jigan da ke jagorantar tafiyar ADC, ba wai bukatar ciyar da kasar gaba ba.
Yayin wata hira da sashen Hausa na BBC jim kadan bayan sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a ranar Lahadi, tsohon gwamnan ya ce rashin yarda da akidun 'yan ADC din ne ya sa ya zabi rungumar tsohuwar jama'iyyarsa ta APC, wadda ke kan mulki a yanzu.
A cewar Shekarau ''Na san da ADC tun wajen wata bakwai ko biyar da ake ta yin batunta, lokacin da su Atiku suka yi gangami har rubutu na yi na gaya musu cewa ni bana goyon bayan 'yan takara kadai su ce za su hadu wuri guda ba tare da jama'iyyunsu ba, idan ka kalle su dukkansu takara suke nema''
Ya ce ''Ko kwankwaso da ya shiga ADC a baya bayan nan ai bai boye ba, tun kafin ya shiga ma ya ce duk inda zai koma sai in za a ba shi takarar shugaban kasa ko mataimaki kafin ya koma, saboda haka duk abun da ya hada su kenan'' inji Shekarau.
Shekarau ya ce sakamakon haka ne bayan shawarwari da abokan tafiyarsa na siyasa suka yanke shawarar komawa APC.
Dama dai fitaccen dan siyasar ya taka rawa wajen samar da jama'iyyar ta APC mai mulki gabanin zaben shekarar 2015, wadda daga baya ta lashe zaben shugaban kasar sannan ta kafa gwamnati a jihohi da dama, ko da yake daga bisani ya fice ya bar ta, inda ya koma PDP, daga nan ya koma NNPP, ya sake komawa PDP, sannan a yanzu kuma ya tsunduma APC.
''Akida ce ta sa na rungumi APC''
Tuni Ibrahim Shekarau ya mayar da martani ga masu sukar matakin da ya dauke na sake komawa APC a yanzu, da ke zargin rashin akida ne ya sa shi daukar wannan mataki, inda ya ce akidar ce ma ta sa ya koma jama'iyyar.
''Mu akidarmu ita ce a samar da adalci da gaskiya da walwalar yan jama'iyya da za a ba wa kowa dama ko na zabe ko na mukami, duk inda muke muna duba inane za mu samu damar da za mu bayar da gudummawa'' inji shi.
Ya ce babu wani alkawari da aka yi masa hatta a lokacin da ya gana da shugaba Tinubu a baya bayan nan a fadar shugaban kasar da ke Abuja.
Ya ce sun tattauna ne kan rade radin da ake yi na yiwuwar komawarsa jama'iyyar a wannan lokaci, sannan ya yi amfani da wannan dama wajen ba shi shawarwari kan wasu batutuwa.











