Manchester United da Real Madrid na zawarcin Emery,Arsenal da Chelsea na son Bergvall

Unai Emery

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Unai Emery
Lokacin karatu: Minti 2

Kungiyoyi da dama na bibiyar dan wasan Tottenham da Sweden Lucas Bergvall, mai shekara 20, ciki harda Arsenal da Chelsea . (Caught Offside), external

Mai bai wa Paris St-Germain shawara kan harkokin wasanni Luis Campos ya tattauna da wakilan dan wasan Arsenal da Brazil Gabriel Martinelli, mai shekara 24, da dan wasan RB Leipzig da Ivory Coast Yan Diomande mai shekaru 19.(L'Equipe - in French, subscription), external

Bournemouth ta shirya sayar da dan wasan Faransa Eli Junior Kroupi, mai shekara 19, wanda Manchester United ke zawarcinsa. An yi kiyasin darajarsa ta kai fam miliyan 50. (Football Insider), external

Hankalin Manchester United da Real Madrid ya koma kan Kocin Aston Villa Unai Emery, ko da yake Villa na da kwarin gwiwar cewa zai ci gaba da aiki a kungiyar .(Teamtalk), external

Leeds na sha'awar dan wasan Wolves' da Jamhuriyar Czech Ladislav Krejci, wanda ya cika shekara 27 a ranar Litinin. (Express & Star - subscription), external

Southampton na da kwarin gwiwar cewa za su iya rike dan wasan Brazil Leo Scienza mai shekara 27 duk da cewa Leeds na zawarcinsa .(Football Insider), external

Ana sa ran wakilin dan wasan Barcelona da Poland Robert Lewandowski, mai shekara 37, zai gana da Juventus a wannan makon, yayin da AC Milan ke zawarcinsa. (La Gazzetta dello Sport - in Italian), external

Dan wasan Denmark Andreas Christensen, mai shekara 30, ya ki amincewa da tayin sabon kwantaragi a Barcelona sai dai yana fatan ci gaba da taka leda a wurin.(Mundo Deportivo - in Spanish)