Wurare 5 da suke nuna tarihin cinikin bayi a Afirka

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gagarumar ƙaurar da ta sauya al'adu da siyasa da tsarin mulkin masarautun Afirika.
    • Marubuci, Isidore Kouwonou
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
  • Lokacin karatu: Minti 8

Tsananin azabar da aka sha a baya da, wuraren da ke ɗauke da labarun al'umma musamman baƙar fata da suka ɗanɗana bauta, babu shakka bauta ta taka rawa sosai a tarihin nahiyar Afirka.

Hukumar Kula da Al'adu da Tarihi ta Majalisar Dinkin Duniya watau (UNESCO), ta ce an kwashe mutane tsakanin miliyan 15 zuwa 20 da ƙarfi daga ƙasarsu a cikin shekaru 400 da aka shafe ana cinikin bayi a tsakanin ƙasashen ƙetare. Daga cikin wannan adadi miliyan 10.5 ne suka isa Amurka da Caribbean.

Safarar mutanen ita ce ta haifar da rashin tsarin zamantakewa da siyasa da kuma rushewar masarautu waɗanda ke riƙe da ginshiƙan kwanciyar hankali a Afirka, kamar yadda Maryse Condé ta bayyana cikin littafinta mai suna "Segou," wanda ya bayyana yadda aka gudanar da cinikin bayi da kuma tasirinsa a yammacin Afirka.

Ko bayan kawo ƙarshen cinikin bayi tsakanin Afirika da ƙasashen Larabawa da Turai, tasirin bauta ya ci gaba da a Nahiyar da al'umar ta.

Wurare da dama cikin nahiyar Afirka sun zama cibiyar tunawa da wannan tarihin azaba, inda masu yawon buɗe ido ke ziyarta don tunawa da kuma fahimtar abubuwan da suka faru a baya.

Daga tsibirin Gorée a Senegal zuwa Cape Coast ko El Mina a Ghana, zuwa gidan bayi a Agbodrafo da ke Togo da wucewa da bayi a Ouidah cikin ƙasar Benin da tsibirin Janjanbureh a Gambiya, dubban mutane na kai ziyara waɗannan wurare a kowace shekara don gano yadda aka yiwa Afirka ƙwacen jama'a.

Za mu sake duba waɗannan wurare masu mahimmanci ga nahiyar, da abubuwan da suka faru da muhimmancin kulawa da waɗannan wuraren tarihi don mutanen da zasu zo nan gaba.

1. Tsibirin Gorée a Senegal

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Barrack Obama da Matarsa Michelle

A gidan bayi na tsibirin Gorée watau Gorée Island da ke gabar tekun Dakar babban birnin ƙasar Senegal. Wurin na ɗauke da yanayin alhini da nadama.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An gina shi a ƙarni na 18 kuma ya kasance gidan bayi na farko da turawan Portugal sika gina a shekara ta 1536, sune turawan da suka fara sauka a tsibirin a shekara ta 1444 .

Wannan gine-ginen da ke tsakiyar tsibirin Gorée an yi musu irin tsarin Turawan mulkin mallaka wanda ya ƙunshi benaye biyu tare da ɗakunan ajiyar bayi masu ɗauke da sashen Mata da sashen Maza la'akari da shekaru, ɗakunan na haɗe da kofar nana mai suna ''Door of No Return'' watau in an fita ba za a dawo ba wadda ta zarce zuwa bakin teku, daga bakin ƙofar ana hango gidajen ƴan kasuwa.

"Idan bayi sun isa ƙofa, sai su yiwa Senegal ƙasarsu ta asali kallon ƙarshe saboda zasu bar ta har abada kamar yadda wani jami'i ya shaidawa BBC.

Jami'in ya ƙara da cewa idan masu ziyara zo, su kan koma zuciyarsu cike da juyayi. "Mutane na zuwa nan, idan mun basu labarin yadda bayi mutane kamar mu suka zauna a matsattsun ɗakunan ajiye bayi da kuma yadda suka san idan sun fita ta wannan ƙofa ba zasu dawo ba, da dama daga cikin masu ziyara sai su sa fashe da kuka.

Ya yin wata ziyarar da Fafaroma John Paul ya kai a watan Fabrairun shekara ta 1992 ya bayyana cewa 'cinikin bayi baƙar fata Mata da Maza babban abin kunya ne, mutum ya cutar da mutum ɗan uwansa Allah muna neman gafara.'

Duk da cewar babu sahihin adadin, to amma gidan bayi na kaɓar baƙi da masu yawon buɗe ido 700,000 a tsibirin Gorée kowacce shekara. Hukumar Kula da Al'adu da Kayan tarihi ta Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta mallaki wurin kuma shi ne inda aka fi kaiwa ziyara a Senegal.

Mashahuran mutane irin su Nelson Mandela da François Mitterrand da Jimmy Carter da Bill Clinton da George Bush da Lula da Silva da Sarkin Baudouin da Iyalan Obama da James Brown da kuma Jimmy Cliff da dai sauransu ne suka ziyarci wurin.

2. Gidan bayi na Agbodrafo a Togo

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rijiyar da ake zura bayi bayan an ɗaure su da sarƙa

Ɗakuna 6 ne da babban zauren da aka keɓe don ƴan kasuwa a gidan bayi na Agbodrafo ko Gidan katako wanda aka sanyawa sunan wani ɗan kasuwa daga ƙasar Scotland John Henry Wood wanda ya gina gidan. Gidan na ɓoye a ɗaya daga cikin gaɓar tekun Togo kimanin 50 daga Lomé babban birnin ƙasar.

An gina shi a shekara ta 1835, iskar tekun da ta lalata gini ba ta kawar da shaidar irin azabar da aka ɗanɗanawa bayi ya yin cinikin bayi ba.

Ma'aikatar da ke kula da harkokin masu yawon buɗe Ido ta Togo, ta ce ginin shaida ce ta "rashin adalici da aka yiwa ɗan Adam da kuma irin juriyar da mutum ya ke da ita, sannan wata gada ce tsakanin lokacin da ya wuce da yanzu."

Agbodrafo wanda aka fi sani da Porto Seguro ya kasance tashar jiragen ruwa da an kasuwa daga Potugal ke hada-hadar bayi. Tsakanin ƙarni na 17 zuwa na 19 Sarki Assiakoley ya mayar da tashar jiragen ruwan wurin cinikin bayi .

Kamar Gorée da ke Senegal, babban sirrin gidan cinikin bayi na Agbodrafo da kr Togo na ƙarashin gidan, wani ɗaki mai duhu mai tsawo mita 20 wanda ake kira da ''rijiyar sarƙa''. Anan ɗaruruwan Maza da Ma ta da Yara ƙanana ke zaman jiran lokacin da za a tafi da su Amurka,

Har yanzu duhun ɗakin na ɗauke da wani irin yanayi mai tunawa mutane tsahin hankalin wancan lokacin.

Jami'ai su na baiwa ƴan yawon buɗe ido labarin azaba da fargaba. Ka na shiga zaka ga wata bishiyar Mangoro, ƙarƙashinta ne ake yiwa waɗanda aka kamo wanka kafin a tafi da su. A ciki akwai wata ƙofa da iska ke fitowa mai firgitar da waɗanda aka kama.

Ma'aikatar Yawon Bude Ido ta Togo ta ce ''wuri ne da ke koyar da darasin rayuwa, masu ziyara suna samun darussan rayuwa daban daban da suka haɗa da muhimmancin ajiye tarihi don masu zuwa a gaba''.

3. Hanyar bayi ta Ouidah zuwa Benin

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Ouida akwai wata kasuwar bayi, inda ake musayar bayi da kayan more rayuwa tsakanin Turawa da ƴan Afrika.

Hanyar bayi da birnin Ouidah wadda ke kilomita 30 daga Cotonou a Bebin na adaga cikin manyan yankunan tarihi a kasar. Yankin na tunawa da mutane miliyan biyu Maza da Mata da Yara da aka raba da iyalansu da ƙasar su aka sayarwa Turawa.

Masana tarihi a Benin sun bayyana yadda aka yi amfani da kogin Ouidah wajen fidda bayi daga Afrika ta Yamma zuwa ƙasashen Cuba da Haiti da kuma Brazil. Jirage zasu tashi daga Ouidah su dakata a Ghana da senegal kafin su ci gaba da tafiya cikkin mashigin Atlantic inda bayi da dama ke mutuwa kafin kammala tsallalke teku.

A hanyar kilomita 4 zuwa Ouidah, akwai wata kasuwar gwanjo, inda Ƴan Afrika da Turawa ke musayar bayi da kayayyakin more rayuwa.

A yanzu wani ƙaramin dandalin ne ya rage a wurin mai suna ''Place Chacha'' don tunawa da Don Francisco de Souza, wanda aka fi sani da Cha Cha, wani mai cinikin bayi ɗan a ƙasar Brazil kuma wakilin sarki a wajen Turawa.

A Ouidah akwai wani gida da aka yiwa ado da furanni, bayan an kammala cinikin bayi anan ake yi musu shaida da wani ƙarfe bayan an sanya shi a wuta ya yi Ja sai a ɗana musu tambarin wanda ya saye su. Sannan akwai wata bishiyar mantuwa wadda ake tilastawa bayi Maza su zagaya ta sau 9, Mata kuma ana sanya su su zagaya ta sau 7 don su manta da asalinsu da danginsu daga nan sai su koma sai abinda Ubangidansu ya ce.

Akwai kuma ɗakin Zomaï , wani ƙaramin ɗaki ne mai tsananin duhu inda ake ƙulle bayi tsawon watanni 3 zuwa 4 har sai jirgin da zai yi dakon su zuwa inda ba zasu dawo ba ya iso.

4. Cape Coast da El Mina a Ghana

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cibiyar cinikin bayi ta Elmina

Wani wuri da ya yi fice a tarihin cinikin bayi a Afrika ta Yamma shi ne Cape Coast kilomita 150 daga Accra babban birnin ƙasar Ghana.

Turawan Portugal ne suka gina birnin kafin ya koma sansain Turawan Sojin Burtaniya daga baya kuma ya koma cibiyar kasuwancin zinare da katako da kuma bayi.

A Cape Coast ko El Mina, akwai wasu manyan gidaje da shugabannin Turawan ke zama a saman bene gidajen na kallon teku, sojoji na zaune a ƙasan bene su kuma bayi an cusa su a wani ƙaramin ɗaki cikin mummunan yanayi.

Da zarar jirgin bayi ya iso sai bayi Maza da Mata da Yara ƙanana ɗauke da sarƙa su bi ta hanyar nan wadda idan aka bi ta ba a dawo wa don fara tafiyar su ta ƙarshe.

5. Tsibirin Janjanbureh a Gambia

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A birnin Zanzibar akwai irin waɗannan wuraren tarihi na ajiyar bayi, yanzu ƙarƙashin maja'imar Anglican .

Janjanbureh, wanda a baya ake kira da Tsibirin McCarthy tashar wucewa da ayarin bayi ce a kogin Gambia.

Bayin da aka sallama ne suka sauyawa masa suna zuwa Janjanbureh a shekara ta 1923 bayan an hana cinikin bayi.

IFili ne mai faɗin hekta 7 da Turawa da ƴan Portugal da kuma Faransawa suka lalata. An sanaya masa sunan fitaccen Kunta Kinteh na tauraron fim ɗin Amurkan nan ''ROOTS'', a shekara ta 2011 ne kuma aka sanya masa suna Tsibirin James watau James Island.

A Tsibirin Janjanbureh, inda kowanne gini ke dauke da labarin lokacin azaba da tsoro. Ana jibge bayi daga ko ina a tsibirin daga nan kuma sai a tafi da su Banjul babban birnin Gambia don doguwar tafiya

A shekara ta 2003, an sanya Tsibirin Janjanbureh cikin jadawalin kayan tarini na Hukumar UNESCO.

Ba zai yiwu a taɓo batun tarihin cinikin bayi a Afrika ba, ba tare da an ambaci Zanzibar ba, a ƙarni na 19 aka aika da bayi ƙasashen Larabawa da Indiya to amma matsin lambar Turawan Burtaniya ta sanya an dai na cinikin bayi a shekara ta 1873.

Hukumar UNESCO ta ce sama da mutane 700,000 aka yi ciniki a Tsibirin lokacin cinikin bayi tsakanin shaekara ta 1830 zuwa 1873.

A Zanzibar kowacce ranar 6 ga watan Yuni ana bukin tunawa da ranar da aka hana cinikin bayi.