Wane tasiri komawar Malam Shekarau APC zai yi a siyasar Kano?

Shekarau

Asalin hoton, Shekarau New Media Facebook

Lokacin karatu: Minti 4

A ƙarshen makon nan ne tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam'iyyar hamayya ta PDP inda ya koma jam'iyya mai mulki ta APC.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar APC mai mulki ke ta faɗin tashin zawarcin fitattun ƴan siyasa a faɗin jihar Kano.

A watan da ya gabata ne gwamnan jihar ta Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya sheƙa daga jam'iyyar NNPP zuwa jam'iyyar mai mulki ta APC.

To wane tasiri komawar ta malam Ibrahim Shekarau za ta yi zuwa jam'iyyar mai mulki ta APC a zaɓen 2027?

Wannan ne ya sa BBC ta yi duba dangane da irin tasirin da komawar jigon ɗan siyasar jam'iyya mai mulki zai yi.

Me ya sa Shekarau ya koma APC ba ADC ba?

A wata hira da ya yi BBC Hausa, tsohon gwamnan na Kano ya ce ya zaɓi sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ta APC ne bayan shawarwari da abokan tafiyarsa na siyasa suka yanke cewa jam'iyyar ce ta fi dacewa da su.

Dangane da masu sukar malamin da rashin aƙida kan komawarsa APC, Ibrahim Shekarau ya ce aƙidar ce ta sa shi daukar wannan mataki na komawa jama'iyyar.

''Mu akidarmu ita ce a samar da adalci da gaskiya da walwalar yan jama'iyya da za a ba wa kowa dama ko na zabe ko na mukami, duk inda muke muna duba inane za mu samu damar da za mu bayar da gudummawa'' inji shi.

Dangane kuma dalilin da ya sa sanata Malam Ibrahim Shekarau ya ƙi komawa jam'iyyar ADC, malamin ya ce rashin yarda da aƙidun 'yan ADC din ne ya sa ya zaɓi rungumar tsohuwar jama'iyyarsa ta APC, wadda ke kan mulki a yanzu.

''Na san da ADC tun wajen wata bakwai ko biyar da ake ta yin batunta, lokacin da su Atiku suka yi gangami har rubutu na yi na gaya musu cewa ni bana goyon bayan 'yan takara kaɗai su ce za su haɗu wuri guda ba tare da jama'iyyunsu ba, idan ka kalle su dukkansu takara suke nema'," in ji Shekarau.

Abu uku da ke nuna tasirin Malam Shekarau

Malam Kabiru Sufi wanda masanin kimiyyar siyasa ne kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano, CAS, ya lissafa wasu dalilai da ya ce suna nuna sanata Shekarau yana da tasiri a siyasar Kano.

  • Gidan Shekarau: Duba da yadda ake da gida-gidan a siyasa a Kano kamar yadda ake da gidan Kwankwaso to akwai gidan Malam Shekarau to wannan zai ba shi damar zama mai tasiri a siyasar jihar.
  • Yawan Mabiya: Duba da ɗimbin magoya baya musamman waɗanda suka hallara a lokacin sauya sheƙar tasa.
  • Ɗaukar hankali: Duba da irin ɗaukar hankalin da komawar Shekarau zuwa jam'iyyar APC ya ɗauki hankali a jihar Kano abin da ke nuna cewa yana da tasiri a siyasar Kano kuma kowane ɓangare zai yi murnar zawarcinsa.

Abu 3 da ka iya shafar tasirin Shekarau

To sai dai kuma masanin kimiyyar siyasar, Malam Kabiru Sufi ya ce duk da tasirin tsohon gwamnan da ake ganin zai yi amma akwai wasu abubuwan da ya lissafa da ya ce ka iya zama naƙasu ga tasirin malamin.

  • Rashin yin takara: Ana ganin rashin takara da bai yi ba a 2023 a matsayinsa na jagora ka iya dakushe tasirin Malam Ibrahim Shekarau a siyasar jihar.
  • Ƙuri'un PDP a 2023: Duba da ƙuri'un da jam'iyyarsa ta PDP ta samu musamman a zaɓen da ya gabata (jam'iyyar PDP wadda ta tsayar da Sadiq Wali ta samu ƙuri'a 15,000), abin da ke sa ake ganin tasirin da ake sa ran malam Shekarau zai yi ba lallai ya yi shi ba.
  • Rasa mabiya: Ana ganin a yanzu tsohon gwamnan na Kano ba shi da yawan mabiya kamar a baya, inda da dama wasu mabiyan nasa suka fashe suka bar shi. Misali, Nasiru Yusuf Gawuna wanda a baya yake tare da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje yanzu ya koma jam'iyyar adawa ta ADC.

Wane ne Malam Shekarau?

Malam Ibrahim Shekarau ya kasance gwamnan Kano na farko da fara yin tazarce ko kuma wa'adi biyu a kan kujerar gwamna inda ya yi mulki a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011, a ƙarƙashin jam'iyyar ANPP.

Shi ne gwamnan da ya kayar da Rabi'u Musa Kwankwaso a 2003 a lokacin da yake neman wa'adi na biyu, sai dai kuma shi ne dai gwamnan da ya miƙa mulki ga Kwankwason a 2011 lokacin dawo-dawo, bayan Kwankwason ya kayar da Salihu Sagir Takai wanda Shekarau ya tsayar domin ya gaje shi.

Malam Shekarau ya yi takarar neman shugaban ƙasa a jam'iyyar ANPP.

Daga bisani Malam Ibrahim Shekarau ya koma jam'iyyar PDP inda shugaban lokacin Goodluck Ebele Jonathan ya naɗa shi ministan Ilimi.

A 2019, malamin ya zama ɗan majalisar dattawa bayan komawa jam'iyyar APC a zamanin mulkin Abdullahi Umar Ganduje.