Hanyoyi uku da suka rage wa Arsenal na lashe kofin Premier

Wasu ƴanwasan Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Har yanzu magoya bayan Arsenal na ci gaba da alhinin rashin nasarar da ƙungiyar ta yi a wasanta da Man City na ranar Lahadi.

Rashin nasarar da ƙungiyar ta yi da ci 2-1 ya sake jefa ta cikin babbar barazanar gaza lashe Kofin Premier da ta shafe fiye da shekara 20 tana ƙishirwarsa.

A shekarun baya-bayan nan ƙungiyar kan nuna alamun lashe kofin ta hanyar hawa teburin gasar tare da bayar da tazara mai yawa, amma ana zuwa ƙarshen kakar sai komai ya sukurkuce mata.

Hakan ce ma ta sa masu bibiyar ƙwallon ƙafa, musamman masu hammaya da ita ke yi mata kirari da ''Kofi Haram''.

A wannan kaka ƙungiyar ta yi yunƙurin goge wannan kirari, musamman ganin yadda ta jima a kan teburin gasar ta tazara mai yawa da ta bai wa City ta biyu.

To sai dai da alama da wuya haƙar ƙungiyar ta cimma ruwa, bayan shan kaye da 2-1 a hannun AFC Bournemouth da kuma 2-1 a hannun City, lamarin da ya rage tazarar makin da ke tsakaninsu zuwa uku, yayin da City ke da kwantan wasa.

A yanzu da ya rage wasa biyar a ƙarƙare gasar tambayar da mafi yawan masu bibiyar ƙwallon ƙafa ke yi ita ce ko Arsenal za ta iya karya baƙin kirarin da ake yi mata na Kofi Haram? ko kuwa dai tarihi zai ci gaba da maimaita kansa?

Afrilu - wata mai tsanani ga Arteta

s

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kocin Arsenal, Mikel Arteta

Ga Mikel Arteta, Afrilu ya ci gaba da kasancewa wata mafi tsanani gare shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Alƙaluma sun nuna cewa a wannan watan ne Arteta ke yawan rashin nasara a wasannin Premier, wani abu da alamu ke nuna cewa zai maimaita kansa a wannan shekarar ma, kasancewar ta yi rashin nasara biyu zuwa yanzu a cikin watan.

Afrilun 2021, Arsenal ƙarƙashin Arteta ta yi wasa huɗu, inda ta ci ɗaya kawai, ta yi rashin nasara biyu tare da kunnen doki ɗaya.

Haka ma a Afrilun 2022, ƙungiyar ta buga wasa 5, ta ci biyu daga ciki ta kuma yi rashin nasara uku.

A Afrilun 2023 ma, Arsnela ta buga wasa 5, inda ta ci guda ɗaya tare da yin kunnen doki a uku da kuma rashin nasara ɗaya.

To amma a 2024, abubuwa sun sauya, inda ta buga wasa 6, ta ci 5 daga ciki da rashin nasara ɗaya.

Amma a Afrilun 2025 da ya gabata sai aka sake komawa gidan jiya, inda ta buga wasa 5, ta ci 2 da kunnen doki 3.

Sai dai duk da haka Arteta na da ƙwarin gwiwa, kamar yadda ya bayyana a taron manema labarai da ya gabatar bayan wasan na jiya.

"Mun yi rashin nasara a wasa mai muhimmanci, amma har yanzu akwai sauran maki uku, kodayake suna da kwantan wasa, amma har yanzu akwai sauran dama'', in ji shi.

Hanyoyin da suka rage wa Arsenal na lashe kofin

s

Asalin hoton, a Getty Images

Anas Sani Tukuntawa ɗanjarida mai bibiyar wasanni a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ya ce halin da Arsenal ke ciki na buƙatar jajircewa da ƙarin ƙoƙarin ƴanwasa da koci.

Ɗanjaridar ya ce ƙungiyar na da matuƙar ƙishirwar kofin Premier, kuma akwai yiwuwar a kori kocinta idan har ba ta ci kofin na bana ba.

Masanin wasannin ya kuma ce hanyoyi biyu ne kawai zuwa uku suka rage wa Arsenal domin ɗaukar kofin na bana.

''Hanya ta farko ita ce su tabbatar sun ci duka ragowar wasanninsu biyar da suka yi saura, kada ta sake ta yi rashin nasara ko kunnen doki'', in ji shi.

Anas Tukuntawa ya ce su kuma yi fatan Manchester City ta yi rashin nasara a wasu daga cikin wasanninta koda guda ɗaya ne.

''Sannan a wasannin nasu su yi ƙoƙari su riƙa zura ƙwallaye masu yawa, ta yadda koda City ta ci duka wasanninta, Arsenal ɗin ta tsere mata da yawan ƙwallaye'', in ji shi.

Ɗanjaridar ya ce waɗannan su ne kawai hanyoyi uku da suka rage wa Arsenal na lashe kofin Premier na bana.

Ya kuma ƙara da cewa domin cimma hakan akwai buƙatar ƴanwasan Arsenal da kocinta su sake dabara, su ƙara ƙoƙari da saka ƙaimi, domin tabbatar da wannan buri.

Wasannin da suka rage wa Arsenal da City

a

Asalin hoton, Getty Images

Wasanni 5 da suka rage wa Arsenal

  • Newcastle United (Gida)
  • Fulham (Gida)
  • West Ham United
  • West Ham United (Waje)
  • Burnley (Gida)
  • Crystal Palace (Waje)

Wasanni 6 da suka rage wa City

  • Burnley (Waje)
  • Everton (Waje)
  • Brentford (Gida)
  • AFC Bournemouth (Waje)
  • Crystal Palace (Gida)
  • Aston Villa (Gida)