Askarawan Zamfara sun kama mota ɗauke da ababan fashewa

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar tsaro ta Asakarawan Zamfara ta ce ta kama wata mota da direbanta da ke ɗauke da wasu abubuwan fashewa da take zargin za a kai wa yanbindiga.
Rundunar Askarawan ta ce ta kuma samu kuɗi sama da naira miliyan 13 a motar da ta kama a ƙauyen Bindin da ke ƙaramar hukumar Maru.
Jihar Zamfara dai na fama da matsalar tsaro ta ƴanbindiga wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, inda rahotanni masu karo da juna ke nuna rasuwar dubban mutane da kuma ɗaiɗaita miliyoyi.








