Yadda sojojin Najeriya suka kashe ƴaƴan Ado Aleiro da ƴanbiniga 65
Asalin hoton, Others
Rahotonni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana cewa jami'an tsaron ƙasar sun yi nasarar kashe wasu manyan barayin daji 65 ciki har da ƴaƴan ƙsurgumin ɗan bindigar nan Ado Aleiro.
Bayanai sun ce ƴaƴan ƙasurgumin ɗanfashin dajin uku na daga cikin ɓarayin dajin da suka addabi yankin Tsafe.
Mannir Sani Fura Girke ɗanjarida ne mai binciken ayyukan ƴanbindiga a arewa maso yammcin Najeriya ya kuma shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne yayin wani artabu da aka kwashe awanni ana yi tsakanin ƴan bindigar da jami'an tsaro.
Ɗanjaridar ya ce ƴan bindigar ƙarƙashin jagorancin Ado Aleiro suka yi yunƙurin kai hari kan sabon sansanin jami'an tsaro da aka buɗe a garin ƙunshin Kalgo, inda kuma jami'an tsaron suka mayar da martani.
''Tun maraicen ranar Asabar ɓangarorin biyu suke musayar wuta tsakaninsu har zuwa wayewar garin Lahadi ake fafatawa'', in ji shi.
Ƴanbindiga da aka kashe
Asalin hoton, Others
Ya ci gaba da cewa fafatawar ta yi sanadin kisan ƴanbindigar kusan 65.
''Daga ciki akwai ƴaƴan Ado Aliero na cikinsa har guda uku, ciki har da babban ɗansa,
- Sarki Ado Aleiro
- Ahmadu Ado Aleiro
- Iliya Ado Aleiro
- Kacalla Hukuma
- Kacalla Dogo Burti
- Kacalla Baƙin Sifindi
- Kacalla Mani Mugu
- Kacalla Iliya mai Rasha.
''Duka waɗannan su ne manyan jagororin tawagar da suka jagoranci wannan faɗan'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Mai bincike kan ayyukan ƴanfashin dajin ya ce ba a jima da buɗe sabon sansanin sojin a garin Ƙuncin Kalgo, wanda ke kusa da dajin Munhaye, da ya yi ƙaurin suna a matsayin mafakar ƴanbindiga.
''Duk ɓarayin da suka fito daga dajin Munhaye ta Ƙuncin Kalgo suke bi domin su je yammacin tsafe, ko su bu hanyar Gusau ko su je Faskari ko su shiga yankuna Bakori da Kankara'', in ji shi.
Ya ce girka jami'an tsaro a wannan sabon sansanin ba ƙaramar nasara ba ce ga rundunar sojin Najeriya, musamman a wannan muri mai matuƙar muhimmanci ga ayyukan ƴanbindigar.
Wane ne Ado Aleiro?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sunansa Ado Aleru Ƴankuzo kuma haifaffen garin Tsafe ne da ke ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Alero shi ne shugaban ɗaya daga cikin kungiyoyin ƴan ta'adda da ke da alhakin kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a Kananan Hukumomin jihohin Zamfara da Katsina, da jami'an tsaron Najeriya suka fi nema ruwa a jallo.
A watan Yulin 2022 ne aka yi wa Ado Aleiro naɗin Sarkin Fulani al'amarin da ya janyo har ta kai ga gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin Ƴandoto bisa naɗin.
Rundunar ƴansandan jihar Katsina a lokacin ta ce tana neman ɗanbindigar ruwa a jallo bisa kashe-kashen al'umma ciki har da kisan mutum fiye da 100 a Katsina.
"Adamu Aliero na daga cikin masu kashe mutane da kama mutane su yi garkuwa da su, kuma muna nemansa a kan aikin ta'addanci da ya yi a garin Kadisau, inda ya kashe sama da mutum ɗari," in ji SP Gambo Isa, kakakin ƴansanda jihar Katsina.
Wannan ne ya sa gwamnan jihar Katsina na lokacin, Aminu Masari ya ayyana Aleiro a matsayin cikakken ɗan ta'adda kuma ya ce ba za su taɓa yafe masa ba.
A watan Mayun 2025 rahotanni suka nuna cewa an kama mahaifya da mai ɗakin Aleiro a birnin Madina da ke Saudiyya.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai