Da gaske ne sha'awar ma'aurata na dakushewa?

.
Bayanan hoto, Mace da Namiji kwance kan gado sun juyawa juna baya
    • Marubuci, Ruth Clegg
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior health reporter
  • Lokacin karatu: Minti 5

A shekara ta 1990 Alan Reeves yakan yi rawa tsirara a gaban dubban mutane yayin da yake mamba a ƙungiyar Dreamboys. Ya yi farin jini sosai inda ake neman sa a lokuta da dama tare da abokansa masu rawa, sun taɓa fitowa a fim ɗin Spice Girls mai suna Spice World.

A wancan lokaci ya na da shekara 24 da haihuwa.

Amma da ya kai shekara 30, sai ya tsinci kansa a mawuyaci hali- sha'awarsa ta ragu ƙwarai.

"Ba na jin daɗin jikina," in ji shi.

Reeves mai shekaru 52 a yanzu ya ce rashin sha'awa ya zamar masa ƙalubale a alaƙarsa.

"Mu kan shafe watanni 3 ko 4 a wasu lokutan ba tare da jima'i ba. Ba na son yi," ya ce.

"Irin wannan yanayi zai iya raba Namiji da Mace."

.

Asalin hoton, Fragile Films/ Icon Entertainment International/ Polygram Filmed Entertainment

Bayanan hoto, Geri Halliwell da Alan Reeves a fim ɗin Spice Girls mai suna Spice World

Yanzu ya koma mai horas da masu motsa jiki a London, Reeves wanda ya fara shan magungunan da ke dawo da sinadarin testosterone watau testosterone replacement therapy (TRT). Ya bayyana cewar sha'awarsa ta dawo inda a yanzu ya na ji kamar shekarunsa 20.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mata ma ba a bar su a baya ba, sun fara komawa testosterone.

Rachel Mason ƴar shekaru 37 mai wallafa labarai game da shekarun da mata suke manyanta watau menopause, ta bayyana cewar magungunan TRT sun ƙara mata kuzari da sha'awa.

An samu ƙaruwar masu amfani da magungunan, bayanai na baya-bayan nan da hukumar NHS ta bayar sun ce an samu ƙaruwar masu buƙatar da kashi 135 tsakanin shaekara ta 2021 da shekara ta 2024.

An samu ƙarin ne ya yin da sha'awar ta ragu tsakani sosai a Birtaniya kamar yadda wata hukumar ƙididdiga ta bayyana (Natsal), lamarin da ya haifar da tambayar sama da mutane 10,000 game da sha'awar su.

A shekara ta 1990. mutane masu shekara 16 zuwa 44 sun bayar da rahoton yin jima'i aƙalla sau 5 a wata ɗaya. Amma a shekara ta 2000 an samu raguwa da kashi 4 ya yin da a shekara ta 2010 aka kuma samun raguwa da kashi 3. A halin yanzu a ana dakon sabon sakamakon binciken cikin wannan shekara, masu bincike na sa rai za a kuma samun raguwar duk da cewar ba su faɗi wani dalili da ke haifar da raguwar sha'awa stakanin mutanen ba.

Ana tafka muhawara sakamakon wannan komabata da ake samu, Shin ko ƙarawa sinadarin testosterone ƙarfi a jikin mutane zai ƙara sha'awar jima'i ko kuwa batu ne kawai don neman suna da kuɗi?

Dakushewar sha'awa

Matsalar dakushewar sha'awa da Alan Reeves ke fuskanta, ɗaya daga cikin misalai ne da masu bincike suka ce yana ƙara yawaita.

"A tsawon shekaru, mun ga raguwar sha'awa tsakanin mutane," in ji Soazig Clifton.

"Akwai ma'aurata a cikin wannan lamari ba kamar a can baya ba, wanda kuma hakan ne ke nuna raguwar sha'awa matuka."

An fi samun raguwar sha'awar tsakanin tsofaffi, ma'aurata ko kuma masu soyayya.

Clifton ta ce akwai wahala a iya bayyana me ya sa ƙarfin sha'awa ke raguwa.

"Babu alkaluma da za su iya faɗa mana dalilin da ya sa ake samun raguwar yin jima'i a matsayin al'umma," in ji ta.

Akwai bincike da yawa waɗanda ke ƙoƙarin fahimtar dalilin da ya sa ake samun haka, suna nuna cewa tsarin zamani na iya zama babban dalili, saboda mutane na ƙarin abubuwa da za su yi.

Gajiyar da muke yi yanzu ta fi ta shekaru 30 da suka wuce, wanda hakan na iya zama dalili, in ji Dakta Ben Davis, masanin ilimin jima'i.

"Mutane na fama da abubuwa da yawa," in ji shi, "Akwai fasaha, amma akwai ƙaruwa gajiya, damuwa da kuma kaɗaici... duka waɗannan za su iya zama abin da ya sa ake samun dakushewar sha'awa.

Akwai kuma hasashen cewa wata ƙarancin sinadarin halitta na namiji wanda ke ƙara ƙarfin jima'i na cikin dalilai na dakushewar jima'i.

"Sindarin halittar namiji na raguwa," in ji Farfesa Geoffrey Hackett.

"Ƙaruwar masu ƙiba, na'ui na biyu na cutar suga, ƙaruwar mutanen da ke zama ko kwanciya na tsawon lokaci - duka waɗannan na rage sinadarin halittar namiji wato testosterone. Kuma hakan zai iya zama dalili na raguwar son yin jima'i.

Sinadarin halitta ya dawo min da jin daɗin rayuwa

Melissa Green ta kasance tana na abin da zai ƙara mata sinadarin halitta kusan shekara guda. Ta ce ba ya ga dawowar jin daɗin rayuwarta - abin ya ceci har aurenta.

Ƴar shekaru 43 da haihuwa ta ce ƙarancin sha'awa ya yi tasiri sosai a dangantakarsu.

"Rayuwata ta koma sabuwa. A wani lokaci, ina jin tamkar ƴar shekara 20," in ji ta.

"Na ƙara samun ƙarfi, ina da kuzari, kuma ƙarfin sha'awata ta dawo."

Melissa Green da mijinta.

Asalin hoton, Melissa Green

Bayanan hoto, Melissa Green da mijinta, Marcus

Ga maza, sinadarin halitta na raguwa ne da kashi ɗaya daga shekara 30 zuwa 40.

Hukumar lafiya ta Birtaniya ta ce wannan ba abin damuwa bane saboda yana cikin ɓangare na tsufa kuma da wuya ya shafi ƙarfin sha'awa.

Alan Reeves ya ce an yi masa allurai huɗu domin mayar da sinadarin halittarsa yadda ya kamata daga NHS. Sai dai, bayan yi masa magani, an faɗa masa cewa abin ba zai ci gaba da aiki ba, "ba tare da an yi masa bayani ba."

"Na koma gidan jiya," in ji shi. "Lokacin ne na yanke shawarar yin shiru."

Hotunan Alan

Asalin hoton, Alan Reeves @coachalreeves

Bayanan hoto, A yanzu Alan Reeves yana horar da masu motsa jiki

Don haka, wane mataki ake son sinadarin halittar namiji ya kai? a

Hukumar lafiya ta Birtaniya ta ce idan sinadarin halittar najimi ya yi kasa da mataki shida zuwa takwas, to za a iya cewa suna da matsala.

Ga mata kuwa, sinadarin halittarsu na raguwa ne tsakanin shekaru 20 zuwa 40, kafin su shiga shekarun ɗaukewar al'ada. Ba matsala bace idan sinadarin ya yi kasa a loakcin, sai dai wani tasiri hakan zai yi ga sha'awar mace baki ɗaya.

Yana da wahala a gane haka, saboda yayin da sinadarin yake da muhimmanci ga mata, wanda ake buƙata ba shi da yawa.

Alan Reeves, ya kasance yana kan magani na daidaita sinadarin halitta na tsawon shekara bakwai, don ƙarfin sha'awarsa ta dawo. Ya ce rayuwarsa ta yi matukar sauya wa.

"Ƙarfin sha'awata ya dawo, akwai lokacin da na riƙa jin son yin jima'i a kowane dare har sau goma.

"Amma hakan ya ragu yanzu kuma komai ya daidaita."

Get in touch

Are you personally affected by the issues raised in this story?