Me ya kamata ku sani kan babban taron jam'iyyun siyasa na Ƙasa
Asalin hoton, INEC
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya zayyana tanade-tanade masu yawa domin gudanar da tsarin shugabanci tun daga tafarkin ƙasa zuwa sama.
Cikin tanade-tanadensa har da na jam'iyyun siyasa da kuma yadda za su riƙa tafiyar da lamuransu da shugabancinsu.
Ya wajabta gudanar da babban taro ga jam'iyyun siyasa domin gabanin ɗaukar wasu manya-manyan hukunce-hukunce na baiɗaya.
Akwai dalilai da ke sa a yi babban taron kasa a jam'iyyance kamar haka:
- Zaɓar waɗanda za su jagorance su, kamar shugaban jam'iyya, sakatare, shugaban matasa, ma'aji da dai sauransu.
- Fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa da zai fafata da sauran 'yan takara daga sauran jam'iyyu.
- Zaɓar mambobin kwamitin gudanarwa, da na kwamitin ƙoli.
- Sauya wani matakin baiɗaya, ko ƙirƙirar wata doka, ko maye gurbin wanda aka rasa a jam'iyya.
Wakilai da mambobin jam'iyya daga faɗin Najeriya ne kawai kundin tsarin mullkin ya baiwa damar zuwa taron tare da jin ra'ayoyinsu.
A lokuta da dama akan fafata tsakanin 'yan takarar cikin jam'iyya, waɗanda suke neman matsayi guda, kamar shugabancin jam'iyya ko kuma takarar shugaban ƙasa.
Wakilan jam'iyya ne ke yin zaɓe har a kai ga fitar da gwani. A wani lokacin kuma ba sai an fafata ba, akan yi maslaha tsakanin 'yan takarar cikin gida wasu su kan janyewa wasu idan aka samu fahimtar juna.
Yaushe ya kamata a yi babban taron jam'iyya?
Asalin hoton, Abba Hikima X
Kwararren masanin doka kuma lauya a Najeriya Abba Hikima ya bayyana cewa dokokin da aka gindaya ba zaɓi ba ne ga jam'iyyu wajibi ne su yi aiki da su shi yasa wasu lokutan idan ba su cika su ba ake watsi da 'yan takararsu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Sashe na 84 na dokar zaɓen Najeriya ya sanya wa'adin kwana 180, kimanin wata shida kenan gabanin zaɓe, a matsayin lokacin da jam'iyyu za su aika da sunan 'yan takararsu na shugaban ƙasa.
"Tsarin mulkin Najeriya dimokradiyyar jam'iyya muke yi, jam'iyya ake zaɓa, komai na gudana ne ƙarƙashin jam'iyya, ɗantakara baya tsayawa a ƙashin kansa ya nemi mulki dole sai ta hanyar jam'iyya, shi yasa ba a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na du gari ba har sai jam'iyyu sun yi babban taronsu na ƙasa", in ji Lauyan.
Lauya Abba Hikima ya ce gabanin rashin fahimtar siyasa da aka samu tsakanin Honourable P.C. Onuoha da R.B.K Okafor na jam'iyyar N.P.P. a 1983, jam'iyyun siyasa na cin karensu babu babbaka, kuma kotuna ba su da hurumin yi musu katsalandan, amma daga baya aka bayar da damar kotuna ka iya shiga cikin lamarin musamman idan matakin da aka ɗauka ya ci karo da dokokin da suka kafa jam'iyyar.
Wannan ya sa ake buƙatar Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta riƙa halartar wajen tarukan jam'iyyun, kazalika aka buɗe ƙofa ga ƙungiyoyin da ke sanya idanu kan harkokin zaɓe da su ma su riƙa halarta domin tabbatar da ingancin zaɓukansu.
Me jam'iyyu ke yi bayan gudanar da babban zaɓe na ƙasa?
Masananin Shari'ar ya ci gaba da cewa bayan kammala zaɓuka ko tarukan, jam'iyyun suna tattara bayanai su tura ga hukumar INEC domin ta zuba bayanan a kundinta, ta kuma samu cikakkun bayanai da sunayen shugabannin da 'yan takarar da aka fitar a jam'iyyance da murya ɗaya.
Ana gudanar da tarukan ƙasa ne a lokacin da bukata ta taso, ma'ana babu wai tsayayyen lokaci da aka ce dole sai cikinsa ne aka amince a yi tarukan.
Kuma ana gudanar da tarukan jam'iyya a matakai daban-daban kama daga matakin ƙananan hukumomi zuwa na jihohi zuwa na ƙasa.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai