Me ya janyo musayar yawu tsakanin Kwankwaso da Nafi'u Bala?

..

Asalin hoton, Kwankwaso/Nafi'u/Facebook

Lokacin karatu: Minti 2

Faɗi-in-faɗa ta kaure tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Nafi'u Bala wanda ake rigimar shugabancin jam'iyyar ADC da shi.

A makon da ya gabata ne dai Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar NNPP, inda ya koma jam'iyyar ADC.

To sai dai jim kaɗan bayan komawar Kwankwason sai hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC ta fitar da matsaya dangane da rikicin shugabanci da ke kotu a tsakanin ɓangarori biyu na jam'iyyar ADC.

INEC ta cire sunan David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar da Ra'uf Aregbesola da kuma sunan sauran membobin kwamitin ayyuka daga jadawalin sunayen da Inec ta amince da su a matsayin shugabannin a jam'iyyar saboda wani hukuncin Kotu.

Kalaman Kwankwaso

..

Asalin hoton, Kwankwaso/Facebook

A wata hira da kafar watsa labarai ta DCL, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana takaicinsa ga irin abubuwan da ke faruwa dangane da rikicin da ke ruruwa a jam'iyyar ADC.

A tattaunawar ya ce ya nemi Nafi'u Bala domin su zauna su tattauna matsalar da ke faruwa a jam'iyyar amma bai samu damar haɗuwa da shi ba.

"A halin da ƙasar nan ke ciki da jam'iyya tamu da dimokraɗiyya bai kamata shi ya zama ƙadangaren bakin tulu ba. Abin da ya ɗauko a halin yanzu ba zai taimake shi ba. Ba zai taimaki ADC da yake son ya shugabance ta ba. Ba za ta taimaki Najeriya ba ba kuma za ta taimaki dimokraɗiyya ba."

"A nan ne nake kira ga dukkannin al'umma waɗanda suka gan shi domin ni na kasa ganin sa da su ba shi sahawarar cewa ya cire hannunsa daga wannan tsari na kawo ƙalubale ga wannan tafiya tamu," in ji Rabi'u Musa Kwankwaso

Martanin Nafi'u Bala

..

Asalin hoton, nafi'u/Facebook

A nasa martanin da ya yi wa sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, a wata tattaunawa da wata kafar watsa labarai mai suna DC Hausa, Nafi'u Bala ya ce Kwankwaso ba shi da bakin magana domin bai shiga jam'iyyar ta halastacciyar hanya ba.

"Shi yaushe ma har ya shiga tafiyar wancan ɓangaren da har yake da bakin magana a kan jam'iyyar ADC. Lallai-lallai na tambatar ya kira ni a waya mun yi magana amma na ce masa ba ni da wani hurumin da zan je mu yi magana da shi a matsayinsa na jam'iyyar ADC.

"Ni ina zargin Kwankwaso da shigowa jam'iyyar ADC domin ya shigo ya lalata jam'iyyar domin Bola Tinubu ya koma mulki...domin mun ga yadda a baya ya ɗauke wata jam'iyyar da ya yi takarar shugaban ƙasa har dattawan arewa suka je suka same shi domin ya janye wa Atiku Abubakar amma ya ƙi. Wannan ya sa Bola Tinubu ya ci zaɓe," in ji Nafi'u.