Ko farin jinin Buhari zai yi tasiri a siyasar ɗansa?

Asalin hoton, Gwamnatin Najeriya
Bayanai na ci gaba da fitowa game da batun tsayawar ɗan tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari, takarar majalisar wakilan Najeriya.
Tun bayan saukar mahaifinsa daga mulki, ƴansiyasa da dama ke alaƙanta Yusuf Buhari da shiga siyasa, to sai dai ya riƙa noƙewa tare da nuna rashin muradin yin hakan.
Kiraye-kirayen da ake yi wa matashin sun ƙara tsananta tun bayan mutuwar mahaifin nasa.
Yanzu haka ana alaƙanta matashin - wanda shi kaɗai ne ɗa namiji ga marigayi Muhammadu Buhari - da takarar majalisar wakilai ta tarayya.
Mene ne gaskiyar batun?
Jaridun Najeriya sun riƙa ambato wata wasiƙa da suka ce daga Yusuf Buhari take game da wannan aniya.
To sai dai BBC ta tuntuɓi, Bashir Ahmad tsohon mataimaki na musamman kan kafofin sadarwa na zamani ga mahaifin Yusuf, wato marigayi Muhammadu Buhari, wanda kuma ya tabbatar da gaskiya al'amarin.
Bashir Ahmad ya ce ''haka ne Yusuf zai tsaya takarar ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Sandamu/Daura/Mai'Adua a zaɓen 2027 mai zuwa''.
Tsohon hadimin Buharin ya ce Yusuf ya ɗauki matakin ne bayan kwashe makonni yana tuntuɓar masu ruwa da tsaki da abokan shawara.
Wasiƙar da ke waɗari a shafukan sada zumunta ta ambata cewa Yusuf Buhari zi yi takarar ne a jam'iyyar APC da mahaifinsa ya zama shugabanta ƙarƙashin inuwarta.
Wane tasiri farin jinin Buhari zai yi wa Yusuf?
Galibi masu kiran matashin ya yi takara, suna yi ne la'akari da irin farin jinin da mahaifinsa ya samu a fagen siyasar Najeriya.
Dr Kabiru Sa'id Sufi malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasar ƙasar, ya ce Yusuf ka iya samun goyon baya da tausayawa daga al'ummar, la'akari da farin jinin mahaifinsa.
''Mahaifinsa ya yi farin jinin da wataƙila zai iya shafarsa a siyasance, kuma yadda aka yi tururuwa a lokacin jana'izar mahaifinsa na nuna tausayawa da mutane suka nuna wa iyalan nasa'', in ji shi.
Dangane da ko Yusuf zai iya taka rawa gani a siyasance, Dr Sufi ya ce duba da yadda wasu yaƴan manyan ƴansiyasa suka yi nasara, kuma suka taka rawar gani, za a iya cewa shi ma Yusuf ana kyautata masa zaton yin ƙoƙarin gaske.
''Idan ka duba mutum ne mai kamun kai da kawaici, wanda bai fiya shiga yahaniya ba'', in ji Dr Sufi.
Wane ne Yusuf Buhari?

Asalin hoton, others
Yusuf Buhari shi ne kaɗai na namiji ga tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shi ne ɗa na biyu a wajen mahaifiyarsa Hajiya Aisha Buhari, matar da tsohon shugaban ƙasar ta biyu.
Matashin mai shekara 34 na auren ƴar gidan tsohon sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero.
Ya karanta fannin tattalin arziki a jami'ar Surrey da ke Birtaniya.
Ba kasafai ake ganin fuskarsa a harkokin siyasa ko mulki ba a zamanin gwamnatin mahaifinsa.
Yusuf Buhari bai taɓa riƙe wani muƙamin siyasa ba a Najeriya ba.










