KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa na 7 zuwa 11 ga watan Afrilun 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Talata 7, zuwa Asabar 11 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Abdu, Haruna Kakangi

  1. AN TASHI WASA, Barcelona 0-2 Atletico Madrid

    Aikin gama ya gama!

    Atletico ta bi Barcelona ta doke har cikin tsakiyar gidanta Camp Nou, karon farko tun 2006.

    Sau biyu Atletico na yin waje da Barcelona a karawarsu biyu ta kifa ɗaya ƙwale a baya.

    Ga shi yanzu suna son su yi na uku.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  2. AN TASHI WASA, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Shi ke nan! PSG ta yi nasara a kan Liverpool hankali kwance.

    In ban da Allah ya kiyaye da ƙwallayen da za a ɗura wa Liverpool sai sun fi haka.

    Hari uku kacal Liverpool ta kai a yau, kuma cikin ukun babu wani mai kyau.

    Wannan ne karon farko da ta gaza kai farmakin cin ƙwallo a wasan Champions League tun bayan karawarta da Atalanta a Nuwamban 2020.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  3. VAR: BABU FENARITI, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Gaskiya yau Ibrahim Konate yana da sa'a.

    Duk da cewa Ibrahim Konate ya ɗan taɓa shi kaɗan amma bai kai a bayar da fenariti ba.

    Saboda haka babu fenariti.

  4. VAR na duba yiwuwar fenariti ga PSG, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Nuno Mendes ya sheƙo a guje da ƙwallo ta gefen hagu, ana tunanin Ibrahim Konate ya ture shi har ƙasa.

    Ana duba bidiyon VAR domin tantance gaskiya.

  5. An kusa tashi wasa!, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    An shiga minti uku na ƙarshe.

  6. , Barcelona 0-2 Atletico Madrid

    Yamal ya burge!

    Lamine Yamal ya shiga ya fita ta tsakankanin defendun Atletico amma a ƙarshe ƙwallon ta ƙwace masa.

    Kash!

  7. Ana ta canje-canjen ƴan wasa, Barcelona 0-2 Atletico Madrid

    Atletico Madris ta maye gurbi Guiliano Simeone da Nicolas Gonzalez, Thiago Almanda kuma ya maye gurbin Antoine Griezmann.

  8. ƘWALLO A RAGA: Barcelona 0-2 Atletico Madrid, Minti na 70

    Alexander Sorloth ya zura ƙwallo ta biyu a ragar Barca.

    Gaskiya Atletico sun shanye matsi sosai daga Barcelona bayan dawowa hutun rabin lokaci, amma lallai sun yi amfani da damarsu.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  9. VAR: BABU FENARITI, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Jose Maria Sanchez Martinez

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ibrahim Konate

    Lafari Jose Maria Sanchez Martinez ya soke fenaritin da ya bayar da kuma katin gargaɗi da ya bai wa Ibrahim Konate.

    Ko haka zai bai wa Liverpool ƙwarin gwiwa?

  10. VAR, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Lafari ya je duba bidiyo domin tantance gaskiya

  11. PSG TA SAMU FENARITI, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Ibrahim Konate ne ya yi sulu ya ɗebe Zaire-Emery ta baya, nan take lafari ya nuna fenariti.

    Da alamu abubuwa na ƙara dagule wa Liverpool.

  12. ƘWALLO A RAGA: Paris St-Germain 2-0 Liverpool, Minti na 65

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Khvicha Kvaratskhelia ya ja ƙwallo ta tsakiyar difendu ya jefa ƙwallo a raga.

    Wannan zai sa PSG ta numfasa!

  13. , Paris St-Germain 1-0 Liverpool

    A cikin minti biyu da suka wuce ana ta gwagwagwa tsakanin waɗannan ƙungiyoyi biyu.

    Ana kai ruwa rana.

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

  14. , Paris St-Germain 1-0 Liverpool

    PSG ta ɓaras da kyawawan damarmaki guda uku zuwa huɗu kuma tabbas za su ɗora wa kansu laifin rashin ƙara yawan ƙwallaye.

  15. Rashford ya ɓaras da dama mai kyau, Barcelona 0-1 Atletico Madrid

    Rashfaord ya samu wata ƙwallo amma sai ya buga ta a gefen raga.

    Da wuya Barcelona ta sake samun wata dama mai kyau kamar wannan.

  16. , Paris St-Germain 1-0 Liverpool

    Duk da cewa ƴan wasan Liverpool sun ɗan fara da kuzari amma ƴan PSG sun sake karɓe fozeshon inda suke shafa ƙwallo a ɓarayin Liverpool.

    Liverpool kan ɗan taɓa ƙwallo lokaci zuwa lokaci amma suna yin kuskure da yawa.

  17. AN DAWO WASA, Barcelona 0-1 Atletico Madrid

    A Camp Nou ma an take wasa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

    Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

  18. AN DAWO WASA, Paris St-Germain 1-0 Liverpool

    An sake take wasa tsakanin PSG da Liverpool bayan dawowa hutun rabin lokaci.

    Steven Gerrard: Ina ganin kamar Liverpool ta yi abin da za ta iya a farkon lokaci amma ya kamata su ƙara ƙokari.

  19. HUTUN RABIN LOKACI: Barcelona 0-1 Atletico Madrid, Barcelona 0-1 Atletico Madrid

    Barcelona ta yi wasa iyakar wasa amma ƙwallo ta ƙi shiga, daɗin-daɗawa kuma aka kori ɗan wasanta Pau Cubarsi, kuma Julian Alvarez ya zura mata ƙwallo,

    Kai, abin ya yi yawa!

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  20. HUTUN RABIN LOKACI: PSG 1-0 Liverpool, Paris St-Germain 1-0 Liverpool

    Liverpool za ta ji babu daɗi an tafi hutun rabin lokaci tana ƙasa, to amma ƙwallo ɗaya ce kawai, akwai sauran lokacin wasa.