Shin nasara Trump ya samu ko faɗuwa bayan amincewa da tsagaita wuta a yaƙin Iran?

Donald Trump at a podium, wearing an American flag pin, stares straight ahead.

Asalin hoton, EPA

    • Marubuci, Anthony Zurcher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 5

Daga ƙarshe dai za a samu kwanciyar hankali - aƙalla a wannan lokaci.

Da misalin ƙarfe 6:32 agogon Washington, shugaba Donald Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa Amurka da Iran sun yi "nisa" a ƙoƙarin cimma "cikakkiyar" yarjejeniyar zaman lafiya sannan kuma ya ce ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako biyu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage saura sa'o'i kaɗan wa'adin da Trump ya bai wa Iran ya ƙare a kan buɗe mashigar Hormuz ko kuma ya "shafe su" da kuma kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi da sufurinta.

Duk waɗnnan sun ta'allaƙa ne kan Iran wadda ita ma ta dakatar da yaƙin da kuma buɗe mashigar Hormuz gaba ɗaya domin ci gaba da zirga-zirgar jiragen ruwan dakon kaya, wanda gwamnatin ta ce za ta yi, yayin da ta nace har yanzu "ita ke da iko" da ruwan.

Yarjejeniyar da aka cimma ta sa Trump ya fita daga tsaka mai wuya, bayan shan alwashin "shafe" Iran a daren jiya, inda kuma yake ƙoƙarin kare ƙimarsa a idon duniya. Hakan wataƙila zai sa Trump ya samu salama na ɗan wani lokaci.

A yanzu za a fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a cikin waɗannan makonni biyun kan yadda za a sulhunta na dindindin. Bayan ɗaukar dogon lokaci ana ja-in-ja, farashin gangar mai ya sauka zuwa ƙasa da $100 a karon farko cikin kwanakin da aka yi ana yaƙin wanda ya sa su ma farasin hannayen jari suka tashi.

Wannan ci gaban da aka samu a ranar Talata ta sa an samu natsuwar cewa barazanar da Trump ya yi na "shafe" Iran ta kau kuma ba za a sake dawo da maganar ba.

Ba lallai barazanar da Trump ya yi ce ta sa Iran ta amince da tsagaita wutar da a baya ta yi watsi da ita ba. Amma dai dai abin da Trump ɗin ya yi da kalaman ashariya da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, babu wani wayayyen shugaban Amurka da ya taɓa yi.

Kuma ko da a ce tsagaita wutar ta makonni biyu ta kai ga dakatar da yaƙin gaba ɗaya, kalaman Trump kan yaƙin tsakanin Iran da Amurka, abu ne da za a daɗe ana kallon Amurka da shi.

Iranians, including men and women  wave the national flags as they gather in Tehran after the ceasefire was announced. On the right, a woman with a black hijab is tearful.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu Iraniyawa sun fantsama kan titunan Tehran bayan an sanar da tsagaita wutar.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙasar da ta ke kallon kanta a matsayin mai wanzar da zaman lafiya a faɗin duniya, amma yanzu ita ce ake ƙoƙarin maido da ita kan dokar ƙasa da ƙasa. Shugaban da ya ke caccakar yadda ake tafiyar da siyasar cikin gida, shi ne yanzu yake aikata hakan ga idon duniya.

Ƴan jam'iyyar Democrats, ba tare da ɓata lokaci ba suka yi alawadai da kalaman na Trump a ranar Talata, inda wasu suka buƙaci a tsige shi.

"A bayyane yake cewa shugaban ƙasa yana rasa ƙimarsa kuma ba shi da nagartar shugabanci," in ji ɗanmajalisa Joaquin Castro a wani saƙo da wallafa a shafin X.

Shi ma Chuck Schumer, ɗaya daga cikin manyan ƴan Democrats a majalisar dattawan Amurka, ya ce duk wani ɗan jam'iyar Republican da ya ƙi kaɗa ƙuri'ar dakatar da yaƙin, "duk wani abu na alawadai da ya faru har da su a ciki".

Duk da cewa wasu ƴan jam'iyar Trump sun mara masa baya, bai samu goyon bayan da ya saba ba.

Austin Scott, ɗanmajalisar wakilai na jam'iyyar Republican daga Georgia kuma jigo a kwamitin kula da ayyukan soji na majalisar, ya yi kakkausar suka ga barazanar Trump na shafe Iran.

Ya shaida wa BBC cewa, "Maganganun shugaban ba su dace ba, kuma ban yarda da su ba."

Sanatan Wisconsin Ron Johnson, wanda a yawancin lokuta mai biyayya ga Trump ne, ya ce Trump "zai tafka babban kuskure" idan ya biye wa son ran sa. Dan majalisa Nathaniel Moran daga Texas ma ya wallafa a shafukansa na sada zumunta cewa bai goyi bayan matakin da Trump ke son ɗauka ba.

Ya ce: "wannan ba ɗabi'ar mu ba ce, kuma ba ya cikin muradun Amurka da aka santa da shi."

Sanata Lisa Murkowski ta Alaska, wacce ba su jima ɓatawa da shugaban Trump ba, kai tsaye ta wallafa cewa barazanar shugaban "ba abin da za a iya yi mishi uzuri ba ne domin samun damar tattaunawa da Iran".

People wave Iranian flags and signs condemning the war on Iran during a protest in Washington, DC, on February 28, 2026. At the centre is a woman wearing a hijab and an Iranian flag is painted on her right cheek.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yawancin Amurkawa ba su san me ke tafiya game da yaƙin Iran ba.

Sai dai duk da haka, Fadar White House za ta iya cewa iƙirarin cewaa barazanar ta yi tasiri.

A wani saƙo da ya wallafa game da tsagaita wutar, Trump ya ce Amurka "ta cimma dukkan manufofinta" na soji

Duk da yake har yanzu Iran na da tsarin shugabanci, an kashe da dama daga cikin manyan shugabanninta a wasu hare-hare.

Har yanzu dai ana da shakku kan manufofin Amurka. Babu wasu cikakkun bayanai kan makamin nukiliyar Iran. Bugu da ƙari har yanzu ƙasar tana da tasiri kan wasu ƙungiyoyi a yankin irinsu ƴan tawayen Houthi a Yemen.

Ko da a ce Iran ta buɗe mashigar Hormuz, ba tare da karɓar wasu kuɗaɗen haraji ba, yanzu an gano ƙarfin ikon ta a kan yankin fiye da kowane lokaci.

A wani bayani da ministan harkokin wajen Iran Seyed Aragchi ya fitar, jim kaɗan bayan sanarwar Trump na tsagaita wuta, ya ce Iran za ta dakatar da kai hare-hare kuma za ta ba da damar wucewa ta Hormuz, amma tare da sanya idon rundunar sojinta. Ya ƙara da cewa Amurka ta amince da buƙatu 10 da suka gabatar.

Waɗannan yarjeniyoyin sun ƙunshi, janyewar sojojin Amurka a yankin, ɗage takunkuman da aka ƙaƙaba wa Iran, biyan diyyar ɓarnar da aka yi mata a yaƙin da kuma ba Iran iko da Hormuz. Akwai matuƙar mamaki mutum kamar Trump ya amince da waɗannan sharuɗɗan da Iran ta gabatar, amma alamu ne da ke nuna cewa za a iya cimma matsaya ta har abada a tattaunawar makonni biyun.

Duk da yake wannan wata nasara ce ta ɗan wani lokaci ga Trump. Ya yi barazana kuma ya samu abin da ya ke so. Amma tsagaita wutar na ɗan wani lokaci ne ba na dindin-din ba.