Ƙasashen Afirka 5 da Dangote zai riƙa sayar wa man fetur

Asalin hoton, NNPCL
Katafariyar matatar mai ta Ɗangote da ke Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara sayar da tataccen man fetur ga wasu ƙasashen Afrika biyar.
Matakin na zuwa ne yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar matsalar tsada da ƙarancin man fetur sakamakon yaƙin Iran, wanda ya haddasa toshe mashigar Hormuz da ake safarar man fetur.
A baya-bayan nan Matatar - wadda ta fi kowacce girma a Afirka - ta sayar wa wasu ƙasaahen Afirka biyar jiragen mai 12 da nauyinsu ya kai tan 456,000.
Matatar na taimaka wa ƙasashen Afirka ta dama rage dogaro da saro mai daga wuri mai nisa, wani abu da ke tsadarsa a ƙasashen.
A baya-bayan nan Ɗangote ya kammala faɗaɗa matatar, wadda a yanzu za ta iya tace ganga 650,000 a kowace rana.
Kuma ingancin tace man da matatar ke yi ya sa man ke samun tagomashi a nahiyar Afirka.
Ƙasashen Afirkan biyar da za su fara sayen mai daga matatar sun haɗa:
Ivory Coast
Ƙasar Ivory Coast, da ke yammacin Afirka ta jima ta na sayo mai daga ƙasashen Gabas ta Tsakiya.
Ivory Coast - wadda ta fi kowace ƙasa samar da cocoa a duniya - kan shigo da kaso mafi yawa na man da take amfani sa shi a cikin ƙasa.
Masana na ganin ƙulla hulɗar ciniki da Ɗangote zai kawo wa ƙasar sauƙin kashe kuɗaɗe masu yawa wajen shigo da mai daga yankin Gabas ta Tsakiya.
Kamaru

Asalin hoton, NNPCL
Kamaru - wadda ta yi iyaka da Najeriya na daga cikin ƙasashen duniya Afirka da ke sayen mai daga ƙetare.
Jaridar Business a Kamaru ta ruwaito cewa bayan da duniya tya fuskanci tashin farashin man fetur sakamakon matsalar jigilarsa, gwamnatin Kamaru ta ɗauki muhimman matakan magance matsalar.
Hukumomin ƙasar sun amince da ɓullo da wani sabon tsari da ƴankasuwa na duniya za su riƙa shigar da man ƙasar ta jirage domin sayar wa dillalai, waɗanda su kuma za su riƙa sayar da shi a ƙasar.
Tanzania
Ƙasar, wadda ke yankin gabashin Afirka, na dogara ne kan yawon buɗe ido da noma da gine-gine wajen samun kuɗaɗen shigarta.
A shekarar 2024, ƙasar ta shigar da man fetur da kudinsa ya kai dala biliyan biyar daga ƙasashen Indiya da UAE da kuma Kuwait.
A baya-bayan nan ƙasar na ƙara yawan man da tsake shigowa da shi sakamakon ƙaruwar buƙatarsa a ƙasar.
Ghana

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Ghana na daga cikin ƙasashen da Dangote ya ƙulla huldar sayar musu da man fetur daga matatarsa.
Yayin da yake jawabi a taron duniya kan makamashi da aka yi a Najeriya, cikin watan Fabrairun wannan shekara, shugaban hukumar kula da man fetur na Ghana, Godwin Kudzo Tameklo, ya ce ƙananan matatun ƙasar Ghana biyu ba sa iya samar wa ƙasar yawan man da take buƙata a cikin gida.
A cewar Mista Tameklo, Ghana za ta ci gaba da shigar da man fetur ɗanye da tatacce daga Najeriya.
Togo
Kamar sauran maƙwabtanta, Ivory Coast da Ghana a Afirka ta Yamma ƙasar Togo ta ƙulla yarjejeniyar sayen mai daga matatar Dangote, domin amfanin cikin gida.
Matakin ƙasar na daga cikin sabbin matakai da take ɗauka na rage kashe kuɗaɗen shigo da kaya daga ƙetare.
Masana na ganin cewa kusancin da ke tsakanin Najeriya da Togo zai rage lokacin da ake ɓata wa kafin man da ƙasar ta sayo ya isa cikinta.
Wane sauƙi ƙasashen za su samu?
Masana na ganin cewa wannan mataki zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka.
Haka kuma zai taimaka wa ƙasashen waje rage yawan kuɗaɗen da suke kashewa wajen sayo man daga yankuna masu nisa.
Galibi dai waɗannan ƙasashe kan sayo man fetur da suke amfani da shi daga yankin Gabas ta Tsakiya, don haka suka ɗauki lokaci mai tsawo kafin man ya iso cikin kasar, sannan suna biyan kuɗaɗe masu yawa domin shigar da man.
Ta ɓangaren Najeriya, matakin ya sauya mata matsayi daga mai sayo mai zuwa mai fitar da mai a Afirka, wani abu da zai bunƙasa tattalin arzikin ƙasar, da kara mata matsayin a idon duniya, a daidai lokacin da duniya ke fuskantar matsalar man fetur.
Bayani kan matatar mai ta Dangote

Asalin hoton, Getty Images
Matatar -wadda hamshaƙin attajirin Afirka, Aliko Dangite ya gina - ta fara aiuki a watan Janairun 2024 bayan ƙaddamar da ita a 2023.
Tun daga wancan lokacin, an ci gaba da faɗaɗa aikinta, inda a yanzu take iya tace ganga 650,000 a kowace rana, adadin da ya fi ƙarfin amfanin Najeriya.
Matatar na sarrafa nau'ika daban-daban na ɗanyen mai da take sayowa daga Najeriya da wasu ƙasashen Afirka da na Gabas ta tsakiya da kuma yankin Amurka.
Matatar na da manyan tankuna 177 waɗanda za su iya ɗaukar mai da yawansa ya kai lita biliyan 4.742.
An ƙaddamar da matatar a 2023, kimanin shekaru 67 bayan da Najeriya ta fara samar da ɗanyen man fetur a 1957.











