Manyan ƴansiyasar Amurka da suka buƙaci a tsige Trump saboda yaƙin Iran

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- Lokacin karatu: Minti 6
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ƙasar za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Iran bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ake yi.
Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa Iran ba za ta ci gaba da bunƙasa uranium ba, kuma Amurka za ta yi aiki tare da Tehran domin kwashe ɓaraguzan makaman da jirgin Amurka na B-2 ya jefa a Iran a shekarar da ta gabata.
"Babu wani abu da aka taɓa tun ranar harin. Muna, kuma za mu ci gaba da tattaunawa kan sassauta haraji da takunkumi tare da Iran," in ji shi.
Da misalin ƙarfe 6:32 agogon Washington, shugaba Donald Trump ya sanar da cewa Amurka da Iran sun yi "nisa" a ƙoƙarin cimma "cikakkiyar" yarjejeniyar zaman lafiya sannan kuma ya ce ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako biyu.
An cimma matsayar ce adaidai lokacin da ya rage saura sa'o'i kaɗan wa'adin da Trump ya bai wa Iran ya ƙare a kan buɗe mashigar Hormuz ko kuma ya "shafe su" da kuma kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi da sufurinta.
Yarjejeniyar da aka cimma ta sa Trump ya fita daga tsaka mai wuya, bayan shan alwashin "shafe" Iran a daren jiya, inda kuma yake ƙoƙarin kare ƙimarsa a idon duniya. Trump ya sha suka da alawadai kan kalaman na sa.
Abin da ya sa ƴansiyasar Amurka suka buƙaci a tsige Trump
Kiraye-kirayen tsige Trump ta hanyar amfani da sashe na 25 ya samu karɓuwa a tsakanin ƴan jam'iyyar Democrat waɗanda suka yi tir da kalaman na shugaban Amurka da cewa "ba su da kan gado" kuma "laifukan yaki" ne.
Ƙasar da ta ke kallon kanta a matsayin mai wanzar da zaman lafiya a faɗin duniya, amma yanzu ita ce ake ƙoƙarin maido da ita kan dokar ƙasa da ƙasa. Bugu da ƙari , shugaban da ya ke caccakar yadda ake tafiyar da siyasar cikin gida, shi ne yanzu yake aikata ba daidai ba a idon duniya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Manyan ƴansiyasa musamman ƴan jam'iyyar Democrats, da dama sun yi alawadai da kalaman na Trump a ranar Talata, inda wasu suka buƙaci a tsige shi daga shugabancin ƙasar.
Kamala Harris: Tsohuwar mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta ce Trump yana barazanar aikata laifukan yaƙi da kuma "shafe Iran" saboda ya fara mummunan yaƙin da ba shi da wani shiri kuma ba shi da dabarar yadda zai kawo ƙarshensa.
"Wannan abin ƙyama ne, kuma jama'ar Amurka ba sa goyon bayan hakan," in ji Harris, wadda ta yi rashin nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2024 da ta fafata da Trump.
"Sakacin Trump yana jefa jajirtattun ma'aikatanmu cikin haɗari."
Ilhan Omar: 'Yar majalisar dokokin jihar Minnesota Ilhan Omar ta yi kira da a tsige Shugaba Trump a ranar Talata bayan da ya yi wa Iran barazanar kisan kiyashi muddin kasar ta cimma yarjejeniyar sake bude mashigar Hormuz.
A wani saƙo da ta wallafa a shafin X, Omar ta kira barazanar Trump da "tsantsar mugunta."
"Dole ne a tsige Donald Trump," in ji ta. "Sai yaushe ƴan Republican za su yi jan wuya su cire shi?"
Wannan dai shi ne karo na biyu a mako guda da Omar ta yi kira da a tsige shugaban.

Asalin hoton, Getty Images
Bernie Sanders: Sanatan Amurka Bernie Sanders ma ya caccaki barazanar da Trump ya yi ta kai wa Iran hari game da Hormuz, inda ya ce kalaman shugaban"abin takaici ne".
Sanata Bernie Sanders ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta inda ya ce, "Yanzu ne lokacin da ya dace ƴan jam'iyyar Republican su yi magana, dole ne a dakatar da Trump, dole ne a kawo karshen yaƙin."
Gwamnan Minnesota: Sa'o'i kaɗan bayan wannan barazanar, gwamnan Minnesota Tim Walz ya wallafa a shafukansa na sada zumunta cewa, "Shugaban ba shi da hankali."
Hakeem Jeffries: Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dokokin Amurka Hakeem Jeffries da ya tsaya tsayin daka da yin kira a tsige Mista Trump, ya yi kira ga takwarorinsa na Republican da su taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin Iran.
"Dole ne majalisa ta gaggauta kawo ƙarshen wannan yaƙin kan Iran kafin Donald Trump ya jefa mu cikin yaƙin duniya na uku," in ji Jeffries.
"Lokaci ya yi da kowane ɗan jam'iyyar Republican ya sanya kishin ƙasa a kan jam'iyya kuma mu dakatar da wannan haukar. Ya isa."
Sauran ƴansiyasar da suka yi kiran tsige Trump
Austin Scott, ɗanmajalisar wakilai na jam'iyyar Republican daga Georgia kuma jigo a kwamitin kula da ayyukan soji na majalisar, ya yi kakkausar suka ga barazanar Trump na shafe Iran.
Ya shaida wa BBC cewa, "Maganganun shugaban ba su dace ba, kuma ban yarda da su ba."
Sanatan Wisconsin Ron Johnson, wanda a yawancin lokuta mai biyayya ga Trump ne, ya ce Trump "zai tafka babban kuskure" idan ya biye wa son ran sa. Dan majalisa Nathaniel Moran daga Texas ma ya wallafa a shafukansa na sada zumunta cewa bai goyi bayan matakin da Trump ke son ɗauka ba.
Ya ce: "wannan ba ɗabi'ar mu ba ce, kuma ba ya cikin muradun Amurka da aka santa da shi."
Sanata Amy Klobuchar ta kira barazanar Mr. Trump a matsayin "rashin hankali."
"Ya fito fili yana yin barazana ta haifar da gagarumin tashin hankali a Iran. Akwai buƙatar majalisa ta yi gaggawar kaɗa ƙuri'a don dakatar da hakan," in ji ta.
Dan majalisar wakilai Angie Craig ya ce barazanar ya yi "ya wuce hankali" har ga shi Mista Trump ɗin.
"A bayyane yake cewa shugaban ƙasa yana rasa ƙimarsa kuma ba shi da nagartar shugabanci," in ji ɗanmajalisa Joaquin Castro a wani saƙo da wallafa a shafin X.
Shi ma Chuck Schumer, ɗaya daga cikin manyan ƴan Democrats a majalisar dattawan Amurka, ya ce duk wani ɗan jam'iyar Republican da ya ƙi kaɗa ƙuri'ar dakatar da yaƙin, "duk wani abu na alawadai da ya faru har da su a ciki".
Duk da cewa wasu ƴan jam'iyar Trump sun mara masa baya, bai samu goyon bayan da ya saba ba.
Sanata Lisa Murkowski ta Alaska, wacce ba su jima ɓatawa da shugaban Trump ba, kai tsaye ta wallafa cewa barazanar shugaban "ba abin da za a iya yi mishi uzuri ba ne domin samun damar tattaunawa da Iran".
Me sharuɗɗa 10 suka ƙunsa?
A cikin sabon saƙonsa a shafukan sada zumunta, Trump ya bayyana ranar a matsayin babbar rana ga zaman lafiya a duniya, yana mai cewa yarjejeniyar na iya kai wa ga wani sabon zamani mai armashi a Gabas ta Tsakiya.
Sai dai har yanzu akwai manyan ƙalubale da ke gaban samun dawwamammen zaman lafiya, inda daga cikin buƙatun Iran akwai biyan diyya da kuma ɗage takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba mata.
Kafar yaɗa labaran Iran ta ce: "Trump ya sanar da tsagaita wuta ta tsawon makonni biyu, inda ya amince da sharuɗɗan da Iran ta gindaya na dakatar da yaƙin saboda gudun zubewar ƙimarsa bayan barazanar da ya yi".
- Dakatar da yaƙi kan Iraƙi, Lebanon da Yemen nan take
- Dakatar da yaƙi kan Iran da kai hare-hare gaba ɗaya ba iya na tsawon wani lokaci ba
- Dakatar da yaƙi a yankin baki ɗaya
- Buɗe mashigar Hormuz
- A bai wa Iran cikakken ƴanci da iko da mashigar Hormuz
- Biyan diyyar ɓarnar da aka yi wa Iran a yaƙin
- A ɗage dukkanin takunkuman da aka ƙaƙaba wa Iran
- Amurka ta saki kuɗaɗen Iran da ta riƙe
- Iran za ta amince ba za ta mallaki makamin nukiliya ba
- Tsagaita wuta nan take idan aka amince da dukkan buƙatun da aka gabatar











