Ƙasashen duniya 10 mafiya ƙarfin soji a 2026

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
Yayin da duniya ta shiga fargabar ɓarkewar yaƙin duniya na uku, ƙasashe na ci gaba da ƙarfafa tsaro da makamansu don nuna ƙarfin da suke da shi a duniya.
A baya-bayan nan yaƙi ya ɓarke tsakanin Amurka da Isra'ila da kuma Iran a gefe guda.
Yaƙin Rasha da Ukraine da ake ci gaba da gwabzawa a ɗaya ɓangaren, ga kuma gwaje-gwajen makamai da Koriya ta Arewa da China ke yawan yi a kai-a kai.
Ƙarfin ƙasashe ta fannin tsaro na buƙatar abubuwa masu yawa fiye da yawan sojoji na kare kai, ciki har da kayan aiki da kuɗin da ƙasa ke kashe wa fannin tsaron ƙasar.
To ko wadannan ƙasashen ne suka fi ƙarfin soji a duniya?
Shafin Global FirePower Index mai nazarin ƙarfin sojojin ƙasashen duniya ta fitar da jerin ƙasashen da suka fi ƙarfin soji a 2026.
Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Shafin Global Fire Power Index ya sanya Amurka matsayi na farko cikin jerin ƙasashen duniya 145 da ya yi nazari kan tsaro da ƙarfin sojinsu.
Amurka mai yawan al'umma miliyan 341,963,408 na da yawan dakarun soji kimanin miliyan 2,132,530, a cewar alƙaluman shafin na GPF.
Daga cikin wannan adadi dakaru miliyan 1,333,030 ne suke kan aiki a yanzu haka, yayin da 799,500 ke jiran ko-ta-kwana.
Shafin na GPF ya ce daga waɗanna dakaru miliyan 1,174,890 na aiki da rundunar sojin ƙasa, yayin da dakaru 708,758 ke matsayin sojojin sama, sai kuma sojojin ruwa kimanin 612,124.
A fannin kasafin tsaro kuwa Amurka ta ware dala biliyan 831.5 a fannin tsaron ƙasar a a shekarar da ta gabata.
Amurka na da sansanonin soji da dakaru masu yawa da ke aiki a ƙasashen duniya daban-daban.
Rasha

Asalin hoton, Reuters
Rasha ce ƙasa ta biyu mafi ƙarfin soji a duniya a 2026 bayan Amurka a cewar shafin GPF.
Ƙasar - wadda ke yankin gabashin Turai - ya da yawan dakarun soji 3,570,000.
Daga ciki 1,320,000 ne ke aiki, yayin da 2,000,000 ke matsayin masu jiran ko-ta-kwana.
Rasha na da yawan sojojin ƙasa kimanin 600,000 yayin da take da na sama kimanin 203,376 da sojojin ruwa 160,000 da saujran jami'an tsaro 250,000, kamar yadda shafin GPF ya bayyana.
Ƙasar ta ware dala biliyan 212 kan fannin tsaron ƙasar a kasafin kuɗin ƙasar na 2026.
Ƙasar Rasha na da sojojin haya da ke aiki a ƙasashen duniya daban-daban da ake kira Wagner.
China

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasa ta uku mafi ƙarfin soji a duniya ita ce China a cewar alƙaluman shafin GPF na 2026.
A cewar alƙaluman Chida - wadda ke yankin Asiya na da yawan sojoji miliyan 3,170,000.
Daga ciki kimanin miliyan 2,545,000 sojojin ƙasa ne, sai na sama 403,000 da sojojin ruwa kimanin 384,000.
China - wadda ke kan gaba afasahar ƙera makamai a duniya- ta ware da fannin tsaron ƙasar dala biliyan 303 a kasafin kuɗin ƙasar na wannan shekara.
Indiya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Indiya - wadda ita me ke yankin Asiya ce- ƙasda ta huɗu cikin jerin ƙasashen da suka fi ƙarfin soji a duniya a cewar alƙaluman GFP na 2026.
Alƙaluman sun nuna cewa ƙasar na da yawan dakarun soji kimanin kusan miliyan biyar.
Daga ciki sojojin ƙasa miliyan 2,148,000 sai na sama 289,000 da na ruwa 184,869.
GFP ya ce a yanzu haka ƙasar na da yawan dakaru miliyan 1,431,000 da ke aiki, sai kuma miliyan ɗaya da ke jiran ko-ta-kwana da wasu jami'an tsaron kimanin miliyan 2.5.
Alkaluman na GFP sun nuna cewa ƙasar ta ware wa fannin tsaron ƙasar dala biliyan 109 a kasafin kuɗin ƙasar.
Koriya ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Koriya ta Kudu wadda ita ma ke yankin Asiya ta jima tana zuba jari a fannin tsaronta.
Ƙasar - wadda ba ta ga-maciji da maƙabciyarta ta arewa - na mayar da hankali wajen ƙarfafa tsaronta.
Koriya ta Kudu na da yawan dakaru da suka kai kimanin miliyan 3,670,000.
Daga cikin wannan adadi 450,000 kaɗai ke aiki a yanzu, yayin da miliyan 3,100,000 ke matsayin masu jiran ko-ta-kwana.
A cewar alƙaluman na GFP Koriya ta Kudu na da sojojin ƙasa kimanin 365,000 da na sama 65,000 da na ruwa 70,000.
Ƙasar ta keɓe wa fannin tsaronta dala biliyan biliyan 44.8 a kasafin kuɗinta.
Faransa

Asalin hoton, Getty Images
Faransa ce ƙasa ta farko mafi ƙafin soji a nahiyar Turai, amma ta shida a duniya, kamar yadda alƙaluman GFP suka nuna.
Ƙasar - wadda ke da yawan dakaru a ƙasashen waje - ta jima tana zuba jari a fannin sojinta.
Faransa na da yawan dakaru 457,444 daga ciki 264,000 ne masu aiki, yayin da 43,444 ke cikin jiran ko-ta-kwana.
Rundunar sojin ƙasa ta Faransa na da yawan dakaru kimanin 141,600, sai na sama 44,120 da sojojin ruwa 47,000.
Ƙasar ta keɓe wa fannin tsaronta kimanin dala biliyan 67.2 a kasafin kuɗinta na wanann shekara.
Japan

Asalin hoton, Getty Images
Japan ce ƙasa ta bakwai cikin jerin ƙasashen duniya mafiya ƙarfin soji a 2026 a cewar shafin GFP.
Ƙasar - wadda ita me ke yankin Asiya na daga cikin ƙasashen da ke kan gaba a harkar ƙera makaman yaƙi.
Japan na da yawan dakarun soji 332,500, daga ciki 251,500 ne ke aiki a halin yanzu, yayin da 56, ke matsayin masu jiran ko-ta-kwana.
Ƙasar ta keɓe wa fannin tsarota kusan dala biliyan 58 a shekarar 2026.
Birtaniya

Asalin hoton, Getty Images
Birtaniya ce ƙasa ta takwas cikin jerin ƙasashen duniya mafiya ƙarfin tattalin arziki, kodayake ita ce ta biyu a nahiyar Turai.
Ƙasar na da daɗaɗɗen tarihin yi wa ƙasashen duniya da dama mulkin mallaka.
A cewar alƙaluman GFP na 2026, Birtaniya da na yawan dakarun soji kimanin 173,270.
Daga cikin wannan adadi 141,330 na aiki a yanzu haka, yayin da kimanin 31,000 ke cikin shirin jiran ko-ta kwana.
Birtaniya na daga cikin manyan ƙasashe masu sansanonin soji a ƙasashen duniya daban-daban.
Haka kuma alƙaluman GFP sun ce ƙasar ta ware kimanin dala biliyan 88.5 ga fannin tsaron ƙasar.
Turkiyya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Turkiyya ce ƙasa Musulmai ta farko a cikin wannan jeri na ƙasashe mafiya ƙarfin soji a duniya.
Turkiyya na da tsohon tarihin yaƙe-yaƙe a zamannan da suka shuɗe, inda take da manyan daulolin da suka yi tasiri a duniya.
A cewar shafin GFP Turkiyya na da yawan sojoji kimanin miliyan 1,011,000, da suka haɗa da 481,000 masu aiki da kuma 380,000 da ke jiran ko-ta-kwana, sai sauran jami'an tsaro 150,000.
Turkiyya na da sojojin ƙasa 401,500 da na sama 52,850 da na ruwa 100,000.
Ƙasar ta ware dala biliyan 51 kan tsaro a akasafin kuɗinta.
Italiya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Italiya ce cikon ƙasa ta 10 cikin jerin ƙasashe mafiya ƙarfin soji a duniya a 2026, a cewar shafin GFP.
Italiya - wadda ke nahiyar Turai - kamar Turkiyya na da daɗaɗɗen tarihin yake-yaƙe tsakanin tsoffin daulolin da suka yi ƙarfi a zamanin baya da ke ƙasar.
GFP ya ce Italiya na da yawan sojoji 288,800, daga ciki 165,000 ne ke aiki, sai kuma masu jiran ko-ta-kwana 18,300 da kuma sauran jami'an tsaro 105,000.
A wannan shekarar ƙasar ta ware dala biliyan 37 don kasafin kuɗin fannin tsaron ƙasar.











