Zakzaky: Abin da ya faru da shugaban IMN da mabiyansa cikin shekara hudu

Asalin hoton, AFP
Tarihin arangamar 'yan Shi'a da jami'an tsaro da zanga-zanga da kuma shari'ar da ake yi wa jagoran kungiyar Islamic Movement In Nigeria, Ibraheem Zakzaky.
-
1980s
-
Yuli 25, 2014Rahotanni sun ce an sojojin sun kashe mabiyan El-zakzaky guda 35 lokacin tattakin ranar Qudus a Zariya da ke jihar Kaduna. Uku daga cikin wadanda aka kashe 'ya'yan Zakzaky ne.
-
Disamba 12, 2014Sojoji sun yi zargin daruruwan mabiyan Islamic Movement In Nigeria da tsare wa hafsan sojin kasar, Laftanar Janar Tukur Burutai, hanya a kan titin Sokoto road da ke Zaria, inda sojoji suka yi zargin kungiyar da yunkurin kashe Buratai, duk da kungiyar ta musanta.
-
Disamba 12-13, 2014
-
Disamba 14, 2014
-
Nuwamba 14, 2016
-
Disamba 2, 2016Wata babbar kotu a Najeriya ta ba da umarnci hukumar SSS da ta saki Elzakzaky a cikin kwana 45.
-
Janairu 20, 2017Kotun ta ce idan ba a bi umarninta ba to za ta kama sifeto janar na 'yan sanda na wancan lokaci, Ibrahim Idris da ministan Shari'a, Abubakar Malami da Darakta Janar na SSS, Lawal Daura, da laifin rasahin girmama kotu kuma za su iya fuskantar zaman gidan kaso idan suka ci gaba da yin burus da umarnin na kotu na Disamba 2, 2016.
-
Janairu 7, 2018Jmai'an tsaro sun kashe dalibai guda biyu a lokacin zanga-zangar neman a saki Elzakzaky a Kaduna d ake arewacin Najeriya.Duk da umarnin da babbar kotun ta bayar da a saki Zakzaky, amma yana tsare a hannun SSS a wani boyayyen wuri. Gwamnati ta sha ikrarin cewa ba ta da hurumin sakin Zakzaky saboda shari'ar da ke masa tana hannun kotu a jihar Kaduna. Hakan ne ya sa mabiya IMN suka lashi takobin ci gaba da zanga-zanga har sai an saki jagoran nasu ko da kuwa za su kare baki dayansu.
-
Janairu 13, 2018
-
Afrilu 16, 2018Yan sanda sun yi rikici da 'yan IMN a lokaci wata zanga-zangar neman sakin Zakzaky a dandalin Unity Fountain, Abuja inda aka kashe mutum daya sannan da dama suka jikkata.
-
Afrilu 23, 2018Yan Shi'a sun sake haduwa da fushin 'yan sanda lokacin wani tattaki zuwa hukumar kare hakkin dan adam. An kama 'yan IMN akalla 115.
-
Mayu 15, 2018An gurfanar da Elzakzaky da matarsa Zeenat a gaban mai shari'a, Gideon Kurada na babbar kotu da ke Kaduna bisa tuhume-tuhumen kisan kai da taro ba da izni ba da kuma tayar da zaune tsaye da dai sauransu. Gwamnatin jihar Kaduna ce ta shigar da karar.
-
Yili 11, 2018Kotu ta dage karar zuwa 2 ga Agusta 2018
-
Agusta 2, 2018Kotu ta dage bukatar Elzakzaky ta neman beli zuwa Oktoba 4, 2018
-
Oktoba 4, 2018Alkali ya sake dage sauraron bukatar bayar da belin Zakzaky zuwa Nuwamba 17, 2018.
-
Oktoba 27, 2018
-
Oktoba 29, 2018
-
Oktoba 30, 2018Yan sanda sun kama 'yan Shi'a 400 bisa tuhumar tayar da zaune tsaye a Abuja. Jmai'an tsaro sun zargin 'yan Shi'ar da mallakar bam din da ake yi fetir guda 31 da sauran muggan makamai. Sojoji sun ce mutum uku ne suka mutu amma IMN ta ce gwammai ne.
-
Nuwamba 17, 2018
-
Disamba 7, 2018
-
January 22, 2019Mai shari'a Gideon Kurada ya yanke cewa hukumar DSS ta ci gaba da tsare Zakzaky da mai dakinsa, Zeenat sannan a ba shi damar ganin likitoci.
-
Yuni 29, 2019Mai shari'a Kurada ya dage karar ba tare da sanya wata rana ba saboda zai shiga sahun alkalan kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa da 'yan majalisa a jihar Yobe.
-
Yuli 9, 2019Yan sanda da 'yan Shi'a sun sake taho mu-gama a wajen majalisar dokokin Najeriya. 'Yan sanda sun ce an harbi jami'ansu guda biyu a kafa sannan an jikkata wasu guda shida da duwatsu. 'Yan sanda sun kama 'yan Shi'a 40. Sai dai wani mamban kungiyar Abdullahi Muhammad Musa ya shaida wa Reuters cewa 'yan sanda sun bude musu wuta, inda suka kashe masu zanga-zanga biyu a lokacin da suke kokairn shiga majalisar dokoki cikin ruwan sanyi.
-
Yuli 10, 2019Yan majalisar wakilai sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta saki El-zakzaky kamar yadda kotuna da dama suka yi umarni.
-
Yuli 18, 2019Mai shari'a D.H Khobo ta jagoranci zaman sauraron bukatar neman beli wadda aka dage zuwa 29 ga Yuli 2019. Ta ce "Yana da muhimmanci a fahimci cewa gwamnatin tarayya ba ta da hannu a ci gaba da rike da Zakzaky kasancewar shari'ar da ake yi masa ta koma hannun jiha. Ba kasafai ake bayar da belin mutumin da ake zargi da kisa ba abin da ya sa Elzakzaky da mai dakinsa ke dogara da batun neman lafiya."
-
Yuli 22, 2019
-
Yuli 26, 2019Gwamnati ta samu hukuncin babbar kotu a Abuja na haramta ayyukan 'yan Shi'a mabiya Zakzaky.
-
Yuli 29, 2019
-
Yuli 31, 2019
Tarihi daga Azeezat Olaoluwa da Princess Abumere da Olawale Malomo.
Hakkin Mallaka na hoto: Getty Images.







