Kalli hotunan yadda aka yi jana'izar Mohammed Morsi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An girke motar 'yan sanda a wajen makabartar da aka binne tsohon shugaban

An binne zababben shugaban kasar Masar na farko, Mohammed Morsi, wanda sojoji suka hambarar da gwamnatinsa a shekarar 2013.

An rufe marigayin a makabartar Al-Wafaa Wa al-Amal da ke gabashin birnin Alkahira ranar Talata.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Makabartar Al-Wafaa Wa al-Amal tana gabashin birnin Alkahira ne

Lauyansa ya shaida wa kamafnin dillancin labarai na AFP cewa an binne shi ne a birnin Alkahira ranar Talata da safe a gaban iyalansa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manyan jami'an gwamnatin Erdogan suna cikin mutanen da suka halarci sallar jana'izar a birnin Ankara

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya yi mutuwar shahada.

Hakazalika an yi wa marigayin sallar jana'iza a birnin Ankara na kasar Turkiyya a ranar Talata.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani masallaci rike da hoton marigayin a masallacin Dergah ranar Talata

Har ila yau an yi masa sallah a masallacin Dergah na birnin Sanlıurfa a kasar ta Turkiyya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda aka yi sallar jana'iza a masallacin Ulu a birnin Diyarbakir a Turkiyya

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Anadolu Agency via Getty

Bayanan hoto, Su ma mazauna birnin Istanbul na Turkiyya sun yi masa sallar jana'iza