Mohammed Morsi: Rayuwar tsohon shugaban Masar cikin hotuna

A ranar Litinin ne kafar talabijin ta kasar Masar ta sanar da mutuwar tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi, wanda aka hambarar da gwamnatinsa a shekarar 2013.

BBC ta tattaro wasu daga cikin hotunan yadda rayuwarsa ta gudana a shekarun baya-bayan nan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan hoton na nuna yadda jagoran kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood, Mohammed Morsi, yake yi wa 'yan jarida bayani a yayin wani taron manema labarai a birnin Alkahira, ranar 6 ga watan Fabrairun 2011. Kusan mako biyu tun kafin a fara bore, dubban masu zanga-zanga ne suka ci gaba da mamayar dandalin Tahrir suna bukatar Shugaba Hosni Mubarak na wancan lokacin ya yi murabus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manyan jagororin kungiyar Muslim Brotherhood a yayin kaddamar da babban ofishinsu a Alkahari a ranar 21 ga watan Mayun 2011. Daga hannun dama Mohammed Morsi ne. Na biyu daga hagu kuma Mahmoud Ezzat ne sabon jagoran kungiyar a wancan lokacin, bayan da kama Mohamed Badie. Na hudu daga hagu kuwa Mahmoud Hussein ne Sakatare Janar na kungiyar Muslim Brotherhood.

Asalin hoton, Daniel Berehulak

Bayanan hoto, A ranar 13 ga watan Yunin 2012 aka dauki wannan hoton na dan takarar shugaban kasar Masar Mohammed Morsi na kungiyar Muslim Brotherhood yayin da ya isa wajen wani taro don gabatar da jawabi. 'Yan takarar shugabancin kasar Mohammed Morsi da Ahmed Shafiq sun yi takara tare a zagaye na biyu na zaben kasar wanda aka yi ranar 16 da 17 ga watan Yuni.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohammed Morsi yana kada kuri'arsa a rumfar zabe a birnin Zagazig, mai nisan kilomita 90 a arewacin Alkahira a yankin gabashin Nile Delta, ranar 16 ga watan Yunin 2012, a lokacin da 'yan Masar suka kada kuri'arsu a zaben da ya raba kan kasar a zagaye na biyu, inda ya samu nasara a kan na hannun damar Hosni Mubarak, Ahmed Shafiq, kwana biyu bayan da kotu ta bayar da izinin rushe majalisar dokoki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar 11 ga watan Yulin 2012 ne Shugaba Mohammed Morsi ya ziyarci birnin Jiddah inda a nan yake magana da manema labarai tare da Yarima mai jiran gado na Saudiyya a wancan lokacin Salman bin Abdulaziz. Ita ce ziyara ta farko da ya kai wata kasar waje bayan hawansa mulki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar 26 ga watan Satumbar 2012 Shugaba Mohammed Morsi ya gabatar da jawabi ga shugabannin duniya a wajen taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York. Fiye da firaministoci 120 ne da shugabannin kasashe da sarakuna suka halarci taron. Taron ya mayar da hankali ne kan rikicin Syria wanda yake barazana ga zaman lafiyar yankin kasashen Larabawa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar 12 ga watan Agustan 2013 magoya bayan Shugaba Morsi suka yi wani zaman dirshan a dandalin Nahda a yankin Giza. Dakarun tsaron Masar sun yi barazanar yin kawanya a sansanonin da masu zanga-zangar ke zaman. A ranar Litinin kuma bangaren shari'a na Masar ya kara wa'adin zaman Morsi a gidan yari har zuwa wasu kwanaki 15 din har sai an kammala bincike kan tuhume-tuhumen da ake masa da suka hada da hada baki da Kungiyar Hamas ta Falasdinawa. Magoya bayan Morsi sun ci gaba da zaman dirshan a Alkahira fiye da wata daya bayan da sojojin Masar suka hambarar da zababben shugaban kasar na farko a ranar 3 ga watan Yuli.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hambararren Shugaba Morsi yayin da ya halarci zaman shari'a da ake masa ranar 26 ga watan Fabrairu