Iran na da tarin sindarin uranium - amma me ya sa ba za ta iya mallakar makamin nukiliya ba?

Asalin hoton, Getty Images/BBC
- Marubuci, Luis Barrucho
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 5
Tarin sinadaran uranium da Iran ke da shi ya ɗauki hankali bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ce Tehran ta amince ta miƙa shi, daga cikin yarjejeniyar da aka cimma domin dakatar da yaƙi.
Sai dai mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh ya musanta wannan iƙirarin, inda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa babu wannan maganar.
Yayin da ake ci gaba da tattaunawar tsakanin bangarorin biyu, ana ganin sinadarin na daga cikin manyan batutuwan da za a maida hankali a kai.
Amma mene ne tataccen sinadarin uranium ɗinnan - kuma me ya sa yake da muhimmanci?
Mene ne sinadarin uranium?
Uranium wani sinadari da ake samu a cikin ƙarƙashin ƙasa.
Mafi yawa yana da nau'i guda biyu ne: U-238 da U-235.
Kusan kashi 99 na uranium samfurin U-238 ba shi da amfani wajen ƙera makamin nukiliya. Bai wuce kashi 0.7 na U-235 ba ne ke da ƙarfin samar da makamin.
Idan har ana son uranium ya yi tasiri, sai an inganta samfurin U-235 zuwa abin da ake kira "wadataccen sinadarin uranium".
Abu na farko dai shi ne, ana sarrafa uranium zuwa gas. Daga nan sai a zuba shi cikin wani inji da zai riƙa markaɗa shi da sauri.
A yayin da ya ke jujjuyawa, samfurin U-238 zai ci gaba da ƙara nauyi da haɗewa, yayin da samfurin U-235 zai ci gaba da rage nauyi yana taruwa tsakiya.
Wannan ya sa samfurin U-235 ke ƙaranci, wanda kuma shi ne ke da amfani - amma sai idan an raba shi da U-238.

To request this and the next graphic:
Complete the translations here: https://tinyurl.com/2haz2w67
Fill-in the commissioning form https://bit.ly/ws_design_form with this title in English:
Uranium enrichment process - 2026042006
Mene ne bambancin uranium ɗin da ake amfani da shi domin makamashin nukiliya da na makami?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bambance-bambancen wadataccen sinadarin uranium ya sa ake iya amfani da shi domin abubuwa da dama.
Idan uranium samfurin U-235 bai wuce kaso 3 zuwa 5 ba, ana amfani da shi domin samar da man da ake amfani da shi a cibiyoyin nukiliya. Wannan zai iya aiki wajen makamashi amma kuma ba abin da zai iya yi wajen makamin nukiliya.
Uranium ɗin da ya kai kashi 20 zuwa sama, za a iya amfani da shi wajen bincike kan makamashi, amma kuma ana buƙatar ya kai kusan kashi 90 domin ƙera makami.
A wannan matakin, ana ganin ya wuce batun makamashi, kuma ya wuce ƙima. Idan aka tattaro waɗannan waje guda, daga nan ne za a fara samun alamun daga sinadarin.
Wannan shi ne bambancin yadda gwamnatin farar hula da ta soji suke amfani da uranium: ana amfani da shi ne domin samar da wadataccen mai na makamashi, kuma ana sanya ido a kai sosai, inda ake sakin shi a tsawon watanni ko kuma shekaru. Idan kuma na bam ne, akwai bambanci: ana sakin shi ne ne a lokaci guda.
A wata yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin manyan ƙasashe shida a shekarar 2015 - China, Faransa, Jamus, Rasha, Amurka da Birtaniya - An dakatar da irin daga mallakar wadataccenn sinadarin uranium ɗin da ya wuce kashi 3.67.
Yarjejeniyar ta kuma ƙayyade abin da za ta iya adanawa kada ya wuce kilo 300, da kuma adadin wanda za ta iya markaɗawa, tare da dakatar da tace shi a masarrafarta ta ƙarƙashin ƙasa ta Fordo.
Sai dai a shekarar 2018 - a wa'adin mulkin Donald Trum na farko - Amurka ta fice daga wannan yarjejeniyar.

Me ya sa ake damuwa da adadin tataccen uranium?
Adadin yawan wadataccen uranium ɗin aka ƙasa ta mallaka, yana nuna matakin da take kai na ƙera makamin nukiliya.
Mallakar kaso 20 na sinadarin uranium, babban mataki ne, saboda duk wasu matakai da ake buƙata wajen ƙera makamin nukiliya ya kammala a wannan lokacin.
Sarrafa uranium zuwa kaso 20 na tataccen sindari yana buƙatar aiki tuƙuri wajen rarraba su, lamarin da zai ɗauki tsawon lokaci.
Idan aka yi la'akari, mallakar tataccen sinadarin uranium daga kaso 20 zuwa 90 abu ne dai zai ɗauki dogon lokaci da matakai daban-daban.
Wannan na nufin yawan adadin uranium ɗin na nuna yadda ƙasa za ta iya ƙera makamin nukiliya da sauri.
Wane adadin uranium Iran ta tara?
A yayin da ake tsaka da tattaunawa ana sa ran ganin me zai faru da sinadarin uranium ɗin da Iran ta mallaka.
A lokacin da aka fara yaƙi, Iran ta mallaka aƙalla kilo 440 na uranium, wanda ya kai kusan kashi 60, kamar yadda wani babban jami'in Amurka ya bayyana. Ana ganin daga wannan matakin za su iya kaiwa zuwa kashi 90 cikin sauƙi da zai ba su damar mallakar makamin nukiliya.
Iran tana kuma da kusan kilo 1,000 na sinadarin uranium da aka tace kusan kashi 20, da kuma kilo 8,500 da aka tace kusan kashi 3.6, waɗanda ake amfani da su wajen makamashi da kuma binciken likitanci.
Ana hasashen Iran ta adana sinadarin uranium ɗin da za ta iya amfani da shi wajen ƙera makaman nukiliya a Isfahan. Wajen na ɗaya daga cikin ma'ajiyar ƙarƙashin ƙasa na nukiliya da Iran take da su, wanda Amurka da Isra'ila suka kai wa hari a shekarar da ta gabata.

Asalin hoton, Google maps/BBC
To request Isfahan nuclear site:
1. Complete the translations here: https://tinyurl.com/4r62679b
2. Fill-in the commissioning form https://bit.ly/ws_design_form with this title in English:
Iran fortifies underground complex near nuclear site - 2026021301
Sai dai babu tabbacin adadin uranium ɗin da ta tara a wasu wuraren na ƙarƙashin ƙasa.
Wasu majiyoyi sun ce Iran ta ƙi amincewa da buƙatar sanya takunkumin shekaru 20 kan mallakar tataccen sinadarin uranium. A madadin haka, ta ce sai dai ta dakata na shekara biyar kawai, kafin a fara rikici.
Ta kuma ƙi amincewa da buƙatar miƙa kilo 440 ɗin da ta mallaka na sinadarin uranium, inda ta nace cewa sai dai ta narkar da kashi 60 ɗin.
The head of the International Atomic Energy Agency (IAEA), Rafael Grossi, told AP in October last year that this amount - if further enriched - would be enough for 10 nuclear bombs.
Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya shaida wa AP a watan Oktobar bara cewa, adadin da Iran ta mallaka, zai iya ba ta damar ƙera makaman nukiliya 10.
Shin Iran na ƙera makamin nukiliya ne?
Iran ta nace cewa cibiyoyin nukiliyarta ba su wata barazana, ita ma IAEA ta ce babu wata alama da ke nuna cewa tana shirin ƙera makamin nukiliyar.
Mallakar sinadarin uranimun ɗin da zai iya ƙera makami, kamar mallakar makamin nukiliya ne. Sai dai akwai buƙatar ƙarin wasu matakan, da suka da haɗa da tsarawa da kuma ƙaddamar da maɗaukan makaman da na'urorin da za su sarrafa su.
"Iran ta fara tsara samfurin maɗaukan makamin nukiliyar a shekarar 2003, inda ta dakatar da shiri," in ji Patricia Lewis, wata ƙwararriya a fannin makamai.
Sai dai ta ƙara da cewa: "Bayan rashin nasara a tattaunawar da aka yi a shekarar 2015 kan makamin nukiliya, da alama za ta yi gaban kanta domin ci gaba da ƙera makamin".
A watan Mayun 2025, wani bincike da hukumar leƙen asiri ta Amurka ta yi, ya bayyana cewa la'akari da adadin uranium ɗin da Iran ta mallaka, za ta iya mallakar makamin a cikin "ƙasa da mako guda".
Sai dai kuma ta ce ba lallai Iran ɗin tana ƙera makamin nukiliya ba ne, duk da yake tana kan matakan yin hakan.
Isra'ila ma ta ce ta samu bayanain sirrin da ke nuna cewa Iran ta kai wani "muhimmin mataki" da ke nuna ta fara ƙera wasu sassa na makamin nukiliya.
Ƙarin rahotanni da tace su daga Nadia Suleman da Mark Shea











