PSG na son Fernandes, Barca na harin Silva da Neto

Mateus Fernandes

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mateus Fernandes
Lokacin karatu: Minti 2

Paris St-Germain ta gana da wakilin ɗan wasan Portugal da West Ham Mateus Fernandes. (Foot Mercato - in French)

Chelsea na ci gaba da shawarar wanda zai maye gurbin Liam Rosenior, yayin da take duba wanda zai maye gurbin sa ciki har da mai horar da yan wasan Bournemouth Andoni Iraola.(RMC Sport - in French)

Chelsea na kuma duba yiwuwar ɗauko ɗan wasan tsakiya Cesc Fabregas, wanda yanzu ya ke horar da ƴan wasan Como da ke Italiya. (Football Insider)

Barcelona na son Marcus Rashford, da ya ci gaba da zama a ƙungiyar a matsayin dan wasan aro a kakar wasanni mai zuwa, maimakon su biya Manchester United fam miliyan 26 a matsayin dan wasan su na din-din din. (Mirror)

Liverpool, da Chelsea, da Tottenham, da Newcastle, da Aston Villa da Newcastle sun nuna sha'awarsu na ɗaukar mai tsaron ragar Manchester City da Ingilan James Trafford. (Goal)

Manchester United ta sanar da Portugal Bruno Fernandes, cewar suna son ya ci gaba da zama a Old Trafford. (Sun)

Sunderland za ta iya korar mai horar da ƴan wasanta Regis Le Bris a ƙarshen kakar nan, idan ya gaza kai ƙungiyar gasar Eroupean. (Talksport)

Bayern Munich ba za su sake tsawaita zaman ɗan wasan Senegal Nicolas Jackson da ke zaman ɗan wasan aro a ƙƙungiyar da ga Chelsea ba a ƙarshen kakar nan ba.

Barcelona na duba yiwuwar siyo ƴan wasa daga Machester City kamar Bernardo Silva, da ɗan wasan gaba na Chelsea Pedro Neto. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Juventus na harin mai tsaron ragar Liverpool Alisson a wannan kaka, wanda ke cikin ƴan wasan da ta ke baiwa fifiko a cefanen da za ta yi a bana. (Fabrizio Romano)

Manchester United na son ɗakar ɗan wasan Bournemouth da Ingila Alex Scott. (Mirror)

United na matuƙar son ɗauko ɗan wasan Benfica Richard Rois, don in ga ta tsakiyar ƙungiyar. (Caught Offside)

Bournemouth ta shiga cikin jerin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar ɗan wasan Amurka da Bayer Leverkusen Malik Tillman. (Teamtalk)

Fulham na duba tsarin su na shirin ko ta kwana, kan tafiyar mai horar da ƴan wasan ƙungiyar da kwantaraginsa za ta ƙare a ƙarshen kakar na. (The i)

Arsenal na sa ido kan ɗan wasan tsakiya na Turkiya Arda Guler, wanda zai iya barin Real Madrid saboda rashin tabbas kan makomar Alvaro Arbeloa. (Caught Offside)