Darasin da na koya bayan daina shan sukari na tsawon mako shida

Melissa Hogenboom.

Asalin hoton, Getty Images and BBC

Bayanan hoto, Ƴar jarida Melissa Hogenboom ta sauya kalan abincin da take ci don lura da tasirin shan suga a jikinta.
Lokacin karatu: Minti 4

Na'ukan abinci da ke ɗauke da sinadarin sukari na a ko'ina, har ma a wuraren da ba mu yi tsammani ba. Don haka abu ne mai sauki a rage shan sukari, amma wane tasiri hakan zai yi ga lafiyarka?

Duk da cewa na bi tsarin cin abinci mai gina jiki, ina da ɗabi'ar cin kayan zaƙi kuma ina shan cakuleti ɗaya ko biyu a rana.

Wannan ba abin mamaki ba ne: Shan suga mai yawa abu ne da aka saba gani a cikin cimar mu. Ba shi da kyau ga hakorinmu da lafiyarmu, akwai kuma hujjar cewa shan suga mai yawa na janyo wa mutum matsalar rashin fahimta ta tsawon lokaci.

Aiki na ya kunshi mu'amala da batutuwan lafiya da sauransu, kuma na yi matukar damuwa kan yawan kayan zaƙi da nake sha, ga kuma ita suga.

Ɗaya daga cikin kayan zaki da nake sha akai-akai, ya kai fiye da rabin abin da aka ba da shawarar a sha na sukari na yau da kullun.

Daina shan kayan zakin da kuma suga baki ɗaya ba abu ne mai sauki ba, amma na yanke shawarar dakatar da wannan ɗabi'a.

Fafutukar daina shan suga

Na kalubalanci kaina don in guji duk abinci da ke ɗauke da suga a ciki na tsawon mako shida.

Na kuma ƙaurace wa zuma da kayan lemu, sai dai na ci gaba da shan zaƙi daga ƴaƴan itace, da abinci na'uin carbohydrates, wanda jikinmu ke jujjuya shi zuwa sinadarin glucose wanda shi ke samarwa jikin mu da kuma kwakwalwa kuzari.

`Da fari, na fuskanci sauyi na ban mamaki dangane da kuzarina da kuma yanayin jikina.

Zaƙuwar cin abincin rana ta guje sannu a hankali. Sai dai, ina yawan zuwa cikin firiji don duba ɗan abin da zan saka a baki, amma ina ji kamar na rasa wani abu.

Kayan zaƙi

Asalin hoton, Getty Images

Akwai suga a ko'ina

Da farko, yana da muhimmanci a san adadin suga da ke cikin abinci. Na ji mamaki lokacin da gano wahala wajen iya ƙauce wa suga.

Yayin da nake bincike, na gano cewa akwai suga cikin wasu na'uin abincin da ban yi tsammanin za a samu ba. Alal misali, irin biredin nan da ake gasawa a haɗa kuma da wasu sinadarai, yana ɗauke da giram 5.7 na suga a cikinsa.

Yawancin na'uin abincin da ake ƙaryawa da ci yana ɗauke da karin suga, sannan burodin da ake saya a kantuna na ɗauke da giram 1.2 na suga.

Akwai kuma suga sosai a cikin na'uin abincin da aka sarrafa, waɗanda yawanci ake cewa suna da lahani ga jiki kuma suna da ƙarancin sinadarai ba kamar sauran abinci ba, kamar ƴaƴan itace, ganyayyaki da kuma dangin hatsi.

Akwai nau'ukan sukari da yawa a cikin abincin mu. Mai yiwuwa yafi yawa cikin sinadarin Glucose,.

Ana kuma samun sukari a cikin kayan lemu da zuma. Wannan yana cikin manyan abubuwan da ke haifar da illa ga lafiya.

Kayan sha.

Asalin hoton, Getty Images

Tasirin suga a jikin mu

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bincike ya nuna cewa cin abinci masu ɗauke da suga na janyo ƙaruwar suga a cikin jini.

Duk da cewa wannan abu ne da aka saba gani bayan cin abinci, amma idan aka yawaita yin haka zai janyo ƙaruwar suga sosai a cikin jinin, abin da zai iya kai ga barazanar kamuwa da cutar suga mataki na biyu. Har ila yau abinci mai ɗauke da suga sosai zai iya ɓata haƙori, ƙiba har ma da cutar kansa.

"Cutukan da ke da alaƙa da wasu na'ukan abinci, irin su ciwon suga, sun fi kashe mutane fiye da masu shan barasa da wasu kayan maye; kuma takarcen abinci da taba suna sahun gaba wajen hallaka rayuka a duniya," in ji Gearhardt.

Bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa cin abinci mai ɗauke da suga da yawa yana da alaƙa da yawan damuwa da ake fama da shi, ciki har da alamun fargaba da kuma cutar damuwa.

Yayin da hakan zai ƙara zama abin damuwa, shan suga iya adadin da aka kayyade abu ne mai kyau ga lafiya. Sai dai, rage shan suga na da alfanu ga lafiyar miliyoyin mutane waɗanda ke shansa babu adadi.

Ƴaƴan itace.

Asalin hoton, Getty Images

Me zai faru idan muka daina shan suga?

Kwanaki kaɗan bayan daina shan suga, jiki zai fara marmarinsa kaɗan-kadan, kamar yadda Dalia Perelman, wani kwararriya kan abinci mai gina jiki a Jami'ar Stanford ta bayyana min.

Abubuwan ɗanɗano na sun fara daidaita, inda nake ɗandano mai daɗi.

Bayan makonni uku da daina shan suga da na yi, wani abu ya faru: Na ɗaina jin kwaɗayin kayan zaƙi.

Idan na ɗan fara jin kwaɗayi kaɗan da tsakar rana, ina waiwayar abubuwan da suka fi alfanu ga lafiya, irinsu man zaitun da ƴaƴan itace da sauransu.

Ɗaya daga cikin dalilan daina jin kwaɗayi shi ne rage cin abinci mai ɗauke da suga.

Abincin mai ƙarancin sukari yana da alfanu ga lafiya. A wani ƙaramin gwaji, wata tawaga ta buƙaci wasu yara 41 da su daina shan suga na kwanaki 10 kacal.

A karshen wannan gwaji, hawan jini da kuma kitsen jikinsu ya ragu. Sinadarin insulin ɗin su ma ya ragu.

Abinci.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cin abinci mai lafiya yana rage kwaɗayin cin abinci mai ɗauke da suga a tsawon lokaci.

Shin zan koma shan suga?

Bayan makonni shida, zan iya cewa ban ji kwaɗayin cewa in koma cin abinci mai ,dauke da karin suga ba. Watakila kwakwalwata ta fara saba wa da hakan, kamar yadda kwararriya Begdache ta faɗa min.

Ba na jin kwaɗayin cin abinci masu ɗauke da suga a yanzu. Na ma fi jin dadin cin abinci mai ɗauke da ƙarancin suga a cikinsu.

Yanzu da makonni shida na gwajin da na yi sun kare, shin zan koma ɗabi'ata ta cin abubuwa masu suga? Amsar ita ce a'a. Na tsara yin wasu sauye-sauye.

Maimakon daina shan suga baki ɗaya, zan takaitawa kaina shan suga a ranakun mako, inda zan riƙa sha kaɗan kawai a karshen mako.