Yaƙin Iran: Gaba ake ci ko baya?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duniya ta sa ido tana jiran yadda za a samu mafita game da yakin Iran: ko dai a sasanta ko kuma lamarin ya kazance ganin wa’adin da shugaba Trump ya diba
Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da aka kwashe kimanin kwana 40 ana artabu tsakanin Iran da kuma a Amurka da Isra'ila a ɓangare daya, ana ta ƙoƙarin ganin an warware matsalar ta hanyar tattaunawar diflomasiyya domin daƙile yiwuwar ƙazancewa da faɗaɗarsa.

Akwai batu na tsagaita wuta, sannan kuma akwai batu na kawo ƙarshen yaƙin baki-ɗaya kamar yadda Iran ta dage kai da fata.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wata majiya na cewa Iran da Amurka duk sun karɓi wasu jerin shawarwari na kawo ƙarshen yaƙin, wanda ake sa ran za su kawo maslaha wajen bude mashigar Hormuz.

Majiyar ta ce Pakistan ce ta tsara yarjejeniyar kuma ta miƙa ga ɓangarorin biyu, kuma ta ƙunshi matakai biyu, inda za a fara da tsagaita wuta nan take kafin a cimma yarjejeniyar ƙarshe.

Majiyar ta ce yarjejeniyar ta kunshi cewa Iran za ta yi watsi da shirin samun makaman nukiliya, za a dage mata takunkumi sannan za a sakar mata kadarorinta da aka rike.

Hakan zai sanya a dakatar da yakin nan take kuma za a bude mashigar Hormuz, sannan za a cimma yarjejeniya ta karshe cikin kwanaki 15 zuwa 20.

Shafin kafar yada labarai na Axios da ke Amurka shi ma ya ruwaito cewa ana tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan yiwuwar tsagaita wuta ta kwana 45.

Wadannan labarai na shirin tsagaita wuta na zuwa ne bayan hasashen da aka rika yi na inda yakin zai dumfara bayan shugaban Amirka Donald Trump ya yi gargadi game da wa’adin da ya shata wa Iran, cewa yana karewa.

Masu nazari na ganin cewa abubuwa biyu ne za su iya faruwa bayan karewar wa’adin na Trump: ko dai a samu kazancewar yakin tare da fadadarsa ko kuma cimma yarjejeniyar da za ta kai ga Iran ta mika makamashinta na Uranium ga Amirka da kuma sake bude mashigar Hormuz, sai dai manazarta da dama na ganin cewa akwai yiwuwar yakin zai kara kazancewa ne idan aka yi la’akari da abubuwan da ke faruwa.

Yiwuwar cimma yarjejeniya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Manazarta na ganin duk da cewa ana yin sabuwar tattaunawa, amma akwai yiwuwar yarjejeniyar ta gaza cimma nasara, duk kuwa da cewa bangarori da dama na son ganin an yi nasarar.

Bayanan da aka samu a baya sun nuna cewa an gaza samun nasara a yarjejeniya ta farko da Pakistan ta so kulluwa tsakanin Amurka da Iran kasancewar Iran ta yi watsi da sharuddan da Amurka ta gindaya haka nan ita ma Amurka ta yi watsi da sharuddan Iran.

Kafin fara sabuwar tattaunawar ta baya-bayan man, kafar yada labarai ta Isra’ila ta ruwaito cewa Amurka ta sanar da hukumomin Isra’ila cewa tattaunawar da ake yi tsakaninta da Iran ta wargaje, tare da bayyana cewa lamurra za su iya kazancewa.

A nata bangaren kafar yada labarai ta Axios da ke Amurka ta ruwaito cewa Iran na yin watsi da duk wani batu na tsagaita wuta na wucin-gadi, inda take bukatar a kawo karshen yakin baki daya tare da bayar da tabbacin cewa ba za a sake kai mata hari ba.

A kwanakin baya-bayan nan kasashen yankin sun matsa kaimi wajen ganin an dakatar da yakin tare da dakatar da yiwuwar tsawaitarsa.

An gudanar da tattaunawa ba ta kai-tsaye ba a Islamabad, babban birnin Pakistan kafin daga baya China ta tsoma baki domin ganin an hada gwiwa a kokarin yin sasancin.

Yarjejeniyar da China da Pakistan ke son cimmawa sun kunshi sharudda biyar na dawo da zaman lafiya a yankin Gulf da Gabas ta Tsakiya da kuma dakatar da yakin.

Sharuddan sun kunshi daina kai wa juna hari baki daya, da tattaunawar samar da zaman lafiya ba da jimawa ba da kuma dakatar da kai hari kan fararen hula da wuraren da ba na soji ba.

Yarjejeniyar ta kunshi tabbatar da tsaron hanyoyin ruwa da kuma bude mashigar Hormuz ba tare da bata lokaci ba, sannan yarjejeniyar na neman ganin an cimma yarjejeniyar samun cikakken zaman lafiya bisa tsari da manufofi da kuma dokokin majalisar dinkin duniya.

Sai dai abubuwan da suka faru sun nuna cewa Amurka ba ta amince da tsarin na China ba sannan akwai sabani kan hanyar da China ke nema a bi, da kuma wadda Amurka ke son a bi wajen kawo karshen yakin.

Yayin da China ke neman a bi hanyoyi na diflomasiyya wajen tsagaita wuta, ita kuwa Amurka ta ci gaba ne da aiwatar da shirinta na soji, wanda ke da nufin nakasa karfin sojin Iran.

Yiwuwar kazancewar yaki

Idan aka gaza samun mafita ta hanyar sasantawa da diflomasiyya, manazarta na ganin cewa za a samu mummunan kazancewar yakin idan wa’adin da Amurka ta dibar wa Iran ya kare, inda ita ma Iran za ta mayar da mummunan martani.

Wasu da ke goyon bayan Shugaba Trump a Amurka na ganin cewa hakan zai tursasa shugaban ya yi amfani da mummunan karfin soji domin kawo karshen yakin, tare da cewa yana fargabar kada kimar Amurka ya zube a idon duniya inda za a rika yi mata kallon kyanwar lami bayan duk barazanar da ya yi.

Masana a Amurka na ganin yiwuwar Amurka ta dauki mummunan mataki a wannan karo ya zarce na baya, kasancewar da alama a yanzu Amurka ta kara shiri fiye da baya, bayan da ta yi amfani wa’adin da ta bayar a baya wajen kara yawan dakarunta a Gabas ta Tsakiya ta hanyar kai sojojinta na kundunbala, wanda hakan ya kara karfafa shirinta na kai samame ta kasa a cikin Iran, sai dai idan an cimma yarjejeniya kafin karewar wa’adin.

Ana fargabar cewa Amurka tare da hadin gwiwar Isra’ila za su kai farmaki kan cibiyoyin lantarki da na tace ruwa na Iran da zaran wa’adin da Trump ya diba ya kare, a kokarinsu haifar da rudani a cikin kasar domin tursasa wa hukumomin Iran din su mika wuya.

Sai dai manazartan na ganin cewa hakan ba zai tursasa wa Iran ta mika wuya ko ta ja baya ba, kuma hakan zai haifar da kazancewa da fadadar yakin fiye da yadda kowa ke tsammani, kasancewar ita ma Iran za ta iya kaddamar da hare-hare kan cibiyoyin lantarki da makamashi da kadarorin Isra’ila da kuma na kasashen Larabawa na yankin Gulf.