A karon farko cikin shekaru 43, shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya zai sami mataimaki

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Paul Biya, ai shakara 93, ya kasance shugaban Kamaru tun daga watan Nuwamban 1982
    • Marubuci, Paul Njie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, Yaoundé
  • Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Kamaru Paul Biya wanda shi ne shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya, zai samu mataimaki a karon farko cikin shekaru fiye da 40 da ya yi a kan mulki.

Wannan na nufin idan wata ƙaddara ta sami Biya mai shekara 93, to mataimakin nasa zai zamo shugaban ƙasa kuma ya kammala wa'adin mulkin su kafin a sake yin zae.

A 1972 aka soke muƙamin mataimakin shugaban ƙasa a Kamaru, inda a bisa tsarin baya shugaban majalisar dattawa ne zai zamo muƙaddashin shugaban ƙasar idan wani abu ya faru da shugaban, har zuwa lokacin da za a yi sabon zaɓe.

Ƴan adawa sun ce an gaggauta yin sauyin, kuma a cewar su wani mataki ne na ci gaba da riƙe ragamar mulki. A gefe guda kuma wani sanata daga jam'iyyar Biya ma ya ce akwai zargin rashin gaskiya a matakin.

A lokuta da dama, an riƙa yaɗa jita-jita a kan lafiyar Biya, amma an haramta tattaunawa kan batun a bainar jama'a, yayin sau tari yake bayyana a wajen taruka domin musanta jita-jitar mutuwarsa.

Wani zaman haɗin gwiwa tsakanin majalisun ƙasar biyu ne ya zartar da dokar gyaran kundin mulkin ƙasar a ranar Asabar, wadda a yanzu take jiran sanya hannun shugaban ƙasan, bayan ƴan majalisa 200 sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da gyaran, 18 sun yi turjiya kuma wasu huɗu sun ƙauracewa zaɓen.

Masu goyon baya sun ce ƙudirin dokar zai inganta yadda ake tafiyar da gwamnati ta hanyar samar da wakilci mai nagarta a duk lokacin da shugaban ƙasa baya nan. Zai kuma samar da sauƙi ga majalisar dattawa a fannin fama da aikin fitarda wanda zai gaji shugaban ƙasa idan wata ƙaddara ta faru.

A tsarin da ƙasar ke kai a baya dai, shugaban majalisar dattawa ne zai zamo muƙaddashin shugaban ƙasa, idan shugaban ƙasa ya rasu ko kuma ya shiga halin tsananin rashin lafiya, kuma zai riƙe muƙamin har zuwa lokacin da za a yi sabon zaɓe.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amma sabuwar dokar da majalisar ta amince da ita ta yi tanadin cewa mataimakin shugaban ƙasa zai ci gaba da wa'adin mulkin har zuwa ƙarshe, kuma a bisa dokar shugaban ƙasa ne zai naɗa mataimakinsa ba zaɓen shi za a yi ba.

Ƴan adawa sun ce an yi gaggawar gabatar da ƙudirin dokar ba tare da tuntuɓa ba.

Jam'iyyar Social Democratic Front (SDF) mai wakilai shda a majalisar wakilai ta ƙauracewa zaman kaɗa ƙuri'ar. Ta nemi a mayar da tsarin ta yadda za a riƙa zaɓen mataimakin shugaban ƙasa a tare da shugaban kasar, a madadin bai wa shugaba ƙasa shi kadai ikon nadin mataimakinsa.

Jam'iyyar ta kuma nemi a yi tanadi a kundin mulki cewa za a raba muƙamin shugaban ƙasa da na mataimakinsa ne a tsakanin yankuna biyu na ƙasar, wato ɓangaren rainon Ingilishi da kuma na Faransa, kamar dai yadda ƙasar ke gudana kafin 1972.

Haka nan kuma, jagoran ƴan adawa kuma ɗan jam'iyyar Cameroon Renaissance Movement, Maurice Kamto ya zargi jam'iyya mai mulki da yi wa kundin mulkin Kamaru karan-tsaye.

Tsakanin 1961 zuwa 1972, Kamaru tana kan tsari ne na tarayya, kuma akwai tanadin tafiyatare da mutumta juna a tsakanin yankin turawan Ingilishi da kuma Faransa.

A lokacin kundin mulki ya yi tanaadi kan muƙamin mataimakin shugaban ƙasa. Amma bayan wata ƙuri'ar raba gardama a 1972, sai akayi watsi da wannan tsarin.

Asalin hoton, Getty Images/BBC

Go to BBCAfrica.com for more news from the African continent.

Follow us on Twitter @BBCAfrica, on Facebook at BBC Africa or on Instagram at bbcafrica