Yaya mulkin Paul Biya zai kasance a Kamaru yayin da yake tunkarar shekara 100?

Asalin hoton, Reuters
Bayan samun nasara mai cike da ruɗani domin zarcewa kan wa'adin mulki na takwas, shugaba mafi tsufa a duniya, Paul Biya, mai shekara 92, zai ci gaba da shugabanci wataƙila har gab da cika shekara 100 a duniya - idan har zai iya tukarar rikice-rikicen da ƙasar ke fama da su kenan.
Tuni jam'iyya mai mulki a ƙasar ta yi maraba da wannan nasar, sannan kuma Biya ya yi alƙawarin yin mulki cikin adalci.
Sai dai gabani da kuma ma bayan sanar da sakamakon al'umma sun kasance suna zaman ɗarɗar, bayan da babban abokin hamayyarsa, Issa Tchiroma Bakary ya ayyana cewa shi ne ya yi nasara a zaɓen.
Sai dai sakamakon zaɓen ya nuna cewa Biya ya samu kashi 54%, Tchiroma kuma 35%, lamarin da ya zo wa mutane da dama da mamaki sannan kuma wasu murna ta koma ciki.

Asalin hoton, Reuters
"Yanzu Biya ya samu nasara ce amma mai rauni, ganin cewa da yawa daga cikin al'ummar ƙasar ba su yi amannar cewa shi ne ya lashe zaɓen ba," in ji Murithi Mutiga, daraktan sashen Afirka na Ƙungiyar lura da rikice-rikice ta duniya.
"Muna kira ga Biya da ya gaggauta shirin sasantawa a cikin ƙasa domin daƙile yiwuwar yaɗuwar rikici."
Masanin siyasa da tattalin arziƙi a Jami'ar Oxford, Francois Conradie ya ce: "Muna tunanin rikici zai iya rincaɓewa kasancewar ƴan Kamaru da dama sun yi watsi da sakamakon da hukuma ta fitar, kuma ba ma tunanin cewa gwamnatin Biya za ta yi ƙarko."

Asalin hoton, Reuters
Biya wanda ya yi ƙaurin suna wajen kwashe lokaci mai tsawo a ƙasar Switzerland a otal, da wuya a gan shi a bainar jama'a - rashin ganin sa da aka yi na tsawon wata shida a bara ya sanya aka riƙa raɗe-raɗin cewa ya mutu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
To sai dai ɗan siyasar, wadda ake wa laƙabi da "zakin maza" ba ya nuna aniyar kaucewa daga mulki a yanzu.
Biya wanda wanda aka haifa a yankin kudancin Kamaru, kiristocin mishan na Katolika waɗanda ya samu ilimi a hannunsu sun so a ce ya zama malamin coci ne.
To amma Biya a lokacin da yake matashi ya zaɓi ya karanta fannin shari'a da siyasa a Jami'ar birnin Paris, sannan bayan ya gama ya koma gida ya kama aikin gwamnati.
Mutumin mai ra'ayin sauyi ya riƙe muƙamai da dama, inda ya riƙe manyan muƙamai har ya samu shiga a wurin shugaban ƙasar na wancan lokaci Ahmadou Ahidjo, wanda ya kasance kan mulki tun daga lokacin da ƙasar ta samu ƴanci a shekarar 1960.
Ya kasance firaiminista mai matuƙar biyayya na tsawon shekara bakwai, har zuwa shekara ta 1982 - lokacin da Mista Ahidjo ya ɗauki wani mataki mai ban mamaki, inda ya ajiye aikinsa tare da naɗa Biya a matsayin shugaban ƙasa.
Mista Ahidjo ya ci gaba da zama shugaban jam'iyyar, yana tunanin cewa muƙamin shugaban jam'iyya ya fi ƙarfi a kan na shugaban ƙasa.
To amma a wannan lokaci sai Biya ya yi amfani da ƙarfi, ya kori duk mutanen Ahidjo daga gwamnati tare da tursasa wa Ahidjo tafiya gudun hijira.
Daga nan ya nuna kansa a matsayin jarumi, ta hanyar murƙushe yunƙurin juyin mulki sau biyu, ɗaya a 1983 da kuma wanda ya biyo daga baya.

Asalin hoton, Reuters
Ana ganin cewa ɗaya daga cikin sirrin dadewarsa a kan mulki shi ne matarsa ta biyu, Chantal mai shekara 38, wadda ya aura a 1994.
Wadda ta yi suna da shigarta da kuma launin gashinta, ayyukanta na tallafa wa al'umma sun sanya ta yi suna a kafafen sada zumunta.
Kafafen yaɗa labarun Kamaru na yi mata laƙabi da wadda ta mallake zukatan al'umma, wani abu da ya sa ta cike gurbin rashin jin duriyar shugaban.
Mutanen biyu sun haifi yara biyu, kuma har akwai wasu zakuna da aka sanya wa sunansu a gidan namun daji na Mvog-Betsi da ke Yaounde.
Haka nan sun yi ƙaurin suna kan rayuwar ƙasaita da suke yi a kasar ta Kamaru.

Asalin hoton, Brenda Biya/Instagram
Ƴar Biya, Brenda, mai shekara 27 a duniya, ta bayyana kanta a matsayin ƴar maɗigo a wani hoto da ta wallafa a shafinta na instagram a shekara ta 2024, inda aka gan ta tana sumbatar wata mai tallar kayan ado ƴar ƙasar Brazil Layyon Valeca, inda ta rubuta cewa: "Na haukace a kanki kuma ina son duniya ta sani," ta haɗa da alamar zuciya a matsayin tambarin soyayya.
Ƴar ta Paul Biya wadda mawakiya ce da ke zama a ƙasashen ƙetare, wadda ta yi wa kanta laƙabi da King Nasty, ta ce ida da aminiyar tata sun ziyarci Kamaru sau uku tun bayan haduwarsu, wata takwas gabanin hakan, duk da ba ta faɗa wa iyalinta cewa akwai wata alaƙa ta soyayya a tsakaninsu.
Mutanen da ke alaƙar jinsi ɗaya za su iya fuskantar ɗaurin shekara biyar a Kamaru, lamarin da ɗiyar ta Biya ta bayyana a matsayin "rashin adalci kuma ina tunanin labarina zai sauya batun".

Asalin hoton, Reuters
Tun bayan nasarar da ya samu da ƙayara a zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 1992, Shugaba Biya ya kakkaɓe duk wani ƙalubalen zaɓuka da yake fuskanta, inda ake zargin ya riƙa yin katsalandan a zaɓuka da kuma yin amfani da salon rarraba kawuna ƴan adawa.
Abin yabawa da za a iya alaƙantawa da shuga Biya sun haɗa da faɗaɗa makarantu da jami'o'in gwamnati a zamanin mulkinsa da yadda ya tunkari rikicin yankin Bakassi, inda Najeriya ta miƙa wa Kamaru yankin mai dimbin albarkatun man fetur.
To amma duk da haka nan a ƙarƙashin mulkinsa, Kamaru ta shafe kusan shekara 10 tana fama da matsalar ƴan aware a yankin masu amfani da turancin Ingilishi, yayin da Boko Haram ke ƙaddamar da hare-hare a arewacin ƙasar.
Rashin aikin yi a ƙasar ya kai kashi 40% a tsakanin matasa, hanyoyi da asibitoci sun kasance a lalace yayin da ƴancin faɗin albarkacin baki ya zama tarihi.











