Ko Obi da Kwankwaso za su kawo wa Atiku cikas wajen samun takara?
Asalin hoton, BBC COLLAGE
Yayin da zaben Najeriya ke kara karatowa jam'iyyar adawa ta ADC na ci gaba da tumbatsa.
A baya bayan nan, jam'iyyar ta samu karɓar manyan ƴan siysa kamar su tsohon gwamnan kano, Rabiu Kwankwaso da kuma tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna, baya ga ƴan majalisa da suka koma da kuma manyan yan siyasa da suka daɗe suna a cikin ADC kamasr su Peter Obi da Malam Nasir ElRufai da Rotimi Amaechi da sauran su.
Amma yayin da jam'iyyar ADC ke ƙara samun manyan ƴan siyasa da ke shiga cikin ta gabanin babban zaɓen Najeriya na 2027, wani abu da ke ɗaukar hankalin masana da kuma sauran jama'a shi ne zaƙuwa domin ganin wanda zai yi nasarar samun tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Kawo yanzu dai Peter Obi da Rotimi Amaechi sun riga sun sanar da aniyar su ta yin takarar shugaban ƙasa, yayin da Rabi'u Kwankwaso da Atiku Abubakar ba su bayyana aniyar yin takarar ba.
Daga cikin waɗannan ƴan siyasa, Aiku Abubakar ne ya fi kowa tsayawa takarar shugabancin Najeriya, kuma tuni masu sharhi suka fara hasashen yadda za ta kaya a tsakanin su wajen fitar da ƴan takara.
Atiku Abubakar dai shi ne ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a Najeriya, lokacin da ya yi takara a jam'iyyar PDP. Shi kuma Peter Obi da ya yi takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Labour ya ƙare a masayi na uku, yayin da Rabi'u Kwankwaso da ya yi wa NNPP ya ƙarƙare a matsayi na huɗu.
A yanzu da dukkan su suka koma cikin jam'iyya ɗaya, kallo ya koma sama, domin ganin yadda ADC za ta tsallake matakin fitar da gwani, musamman a tsakanin masu sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Akwai masu ganin cewa dunƙulewar manyan ƴan siyasa a ADC zai iya kawo cikas ga burin Atiku na sake yin takara a 2027.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
To sai dai a zantawar shi da BBC, Atiku Abubakar a yanzu ba lokacin takara bane, don haka abin da suka sa a gaba shi ne gina jam'iyyar ADC ta yadda za ta tsaya da ƙafarta.
''Ba maganar ƴan takara a yanzu, muna maganar gina jam'iyya ne , sai ka gina jam'iiya tukun.'' in ji Atiku.
Da aka tambaye shi ko ya yanke shawarar tsayawa takara a 2027, sai tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce a yanzu dai ''wannan ba zan baka amsa ba.''
Dangane da matakin da hukumar zaɓen Najeriya ta ɗauka kan dambarwar shugabancin ADC kuwa, Atiku Abukar ya ce bai yi mamakin abinda ya faru ba.
Ya ce ADC ta cika duk wani sharaɗi da ya kamata wajen rushe tsohon shugabancin jam'iyyar da kuma kafa sabbi na riƙon ƙwarya, amma duk da haka hukumar zaɓe ta ɗauki matakin da ya saɓa haƙiƙanin abin da ke faruwa.
Saboda haka, tsohon mataimakin shugaban Najeriyan ya ce a matsayin jam'iyya za su ci gaba da gudanar da harkokin su ba tare da jiran kowa ba, kuma suna da yaƙinin cewa a ƙarshe za su yi nasara.
Kwankwanso a siyasar Najeriya
Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FB
Tsohon gwamnan jihar Kanon, Rabi'u Musa Kwankwaso na ɗaya daga cikin ƴan siyasa a arewacin Najeriya da suka daɗe suna tasiri, musamman saboda yadda ya shiga zuciyar matasa.
Ana dai ganin tun bayan Malam Aminu Kano ba a sake samun wani ɗan siyasa ba da ya fito da wani tsari na siyasa a arewa da ya saka wa suna, kuma yake da mabiya na ga-ni-kashe-ni, sai Kwankwason.
Kwankwaso ne jagoran aƙidar siyasa mai suna ɗarikar Kwankwasiyya da mabiyanta ke saka jar hula.
Bayan kammala wa'adinsa ne ya tsayar da mataimakinsa, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ba a daɗe ba, suka samu saɓani aka raba-gari.
Wannan ya sa a lokacin da Ganduje yake neman wa'adi na biyu, Kwankwaso ya tsayar da Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2019, amma Ganduje ya kayar da shi bayan an yi zaɓen cike gurbi a garin Gama.
Har ila yau, Kwankwaso ya tsayar da gwamnan Kano mai-ci, Abba Kabir Yusuf inda ya kayar da ɗantakarar gwamna mai barin gado, Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC mau mulkin jihar a lokacin.
Ba zan zama mataimakin Atiku ba - Peter Obi
Asalin hoton, Peter Obi/X
Ɗan takarar shugabancin Najeriya a 2023 a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya tabbatar da cewa zai yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, inda ya yi watsi da yiwuwar zama mataimakin Atiku Abubakar.
Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talbijin na Channels.
"Zan tsaya takarar shugaban ƙasar jamhuriyar Najeriya, kuma na yi imani ina da cancantar yin hakan." In ji Obi.
"..Babu wanda ya taɓa tattauna batun (kasancewa mataimakin Atiku Abubakar). Mutane suna tsammanin abubuwa da yawa. Babu mutumin da ya taɓa magana da ni akan wannan cewa ko zan zama kaza ko kaza".
Peter Obi ya sha nanata aniyarsa na yin wa'adi ɗaya na shekaru huɗu a matsayin shugaban Najeriya idan aka zaɓe shi a 2027.
A shafinsa na X, Peter Obi ya ce idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasar, wa'adi ɗaya na shekara huɗu kawai zai yi kamar yadda ya yi alƙawari.
"Ko tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln wa'adi ɗaya ya yi na shekara huɗu, sannan John F. Kennedy bai ma ƙarasa wa'adi ɗaya ba, amma ana ci gaba da tunawa da su a matsayin shugabanni masu adalci."
Ya ce ko a Afirka, Nelson Mandela ya zama abin koyi a duniya wajen shugabanci na adalci, "amma wa'adi ɗaya kawai ya yi. Ba daɗewa a ofis ba ne ke alamta nasara, irin ayyukan da shugaba ya yi ne za a riƙa tunawa."
Ya ƙara da cewa ya san ƴan Najeriya ba su cika yarda da maganar ƴan siyasa ba, "amma duk da haka akwai masu cika alƙawari."
Obi ya ce duk da wasu ƴan Najeriya na da hujjar ƙin amincewa da alƙawarin ƴansiyasa amma a cewarsa, yana da tarihi mai kyau wajen cika alƙawari tun daga lokacin da ya fara siyasa a Anambra, inda ya ce wata 48 sun isa duk wani shugaba da ya shirya mulki ya yi abin da ya dace.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai