Man U da Man City na son Anderson, Liverpool za ta sallami 'yan wasan da suka gaza

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Elliot anderson
Lokacin karatu: Minti 2

Kungiyoyin Manchester United da Manchester City na fafatawa domin sayen dan wasan tsakiyar fili na Nottingham Forest, Elliot Anderson mai shekaru 23. Kungiyoyin na son kammala cinikin cikin gaggawa a wannan bazara, ganin irin rawar da zai taka a gasar kofin duniya tare a Ingila zai iya daga darajarsa zuwa sama da fam miliyan 100. (The Sun)

Babu tabbas kan makomar kyaftin din Manchester United, Bruno Fernandes mai shekaru 31, musamman idan kungiyar ta samu tayin kudi mai tsoka daga kungiyoyi irin su Paris Saint-Germain da Bayern Munich a wannan bazara. (CaughtOffside)

Sai dai kuma Manchester United na da niyyar rike Fernandes duk da cewa akwai sharadin sakin sa a kwantiraginsa na fam miliyan 57. (Daily Express)

Kungiyar Liverpool na shirin yin garambawul ga 'yan wasanta da ba sa taka rawar gani ba, inda shugabannin Anfield ke shirin amincewa da manyan sauye-sauye a lokacin bazara. (Daily Star)

Liverpool na iya fuskantar gogayya daga Manchester United da Newcastle United idan tana son dauko dan wasan tsakiya na Juventus, Khephren Thuram mai shekaru 25. (Daily Mirror)

Dan wasan baya na tawagar matasa ta Jamus 'yan kasa da shekara 21, Karim Coulibaly, na shirin barin Werder Bremen a wannan bazara, inda ake cewa Newcastle na daga cikin kungiyoyi biyar da ke nemansa. (Bild/Chronicle)

Dan wasan tsakiya na Ecuador, Moises Caicedo mai shekaru 24, ya ce yana da niyyar ci gaba da zama a Chelsea amma bai cire yiwuwar komawa Real Madrid nan gaba ba. (AS)

Mai tsaron raga na Brighton & Hove Albion kuma dan kasar Netherlands, Bart Verbruggen mai shekaru 23, na iya zama zabin Bayern Munich a wannan bazara, yayin da su ma Tottenham da Newcastle ke zawarcinsa. (Teamtalk)

Dan wasan baya na Colombia, Jhon Lucumi mai shekaru 27, na dab da barin Bologna a bazara, kuma Sunderland na ci gaba da sha'awar daukarsa bayan sun kasa samun sa a watannin baya. (ForzaRoma/Sport Witness)