Tsagaita wuta: Wurare 5 da sharuɗɗan Iran suka ci karo da na Amurka

Asalin hoton, Getty images/Tasnim
A ƙarshen makon nan ne ƙasashen Amurka da Iran ƙarƙashin jagorancin Pakistan za su yi wani zama a Islamabad domin tattauna yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu.
Kwana biyu da suka gabata aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako biyu, domin bayar da damar tattauna cikakkiyar yarjejeniyar dakatar da yaƙin Amurka da Isra'ila da kuma Iran a wani ɓangaren.
Duka ɓangarorin biyu sun gabatar da sharuɗɗan kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe kimanin kwana 40 ana gwabzawa.
To sai dai akwai manyan ɓangarori biyar da ƙasashen biyu suka ci karo da juna a sharuɗɗan da kowanesu ya gindaya.
A matsayinta na mai shiga tsakani, Pakistan za ta yi ƙoƙarin daidaita al'amura tare da shawo kan ɓangarorin biyu wajen sassauta sharuɗɗan nasu domin cimma yarjejeniyar ta dindindin.
Kodayake ba a wallafa cikakkun sharuɗɗan ba, da suka haɗa da na Iran 10 da na Amurka 15, cibiyar nazarin alaƙa tsakanin ƙasashen duniya, ''Council on Foreign Relations'', ta zayyana wasu wurare biyar da ƙasashen biyu suka ci karo da juna a sharuɗɗan nasu, sun haɗa da:
Mashigar Hormuz

Asalin hoton, JOHAN VICTOR VIA REUTERS
Mashigar Hormuz ta kasance ɗaya daga cikin abubuwan da aka fi ambata a tsawon lokacin wannan yaƙi.
Tun bayan fara kai mata hare-hare, Iran ta ɗauki matakin rufe mashigar a matsayin martani ga hare-haren.
Mashigar Hormuz ta kasance hanyar da kashi 20 cikin ɗari na man fetur da iskar gas na duniya ke bi ta wurin.
Galibin man da ke bi ta mashigar na ƙasashen Gabas ta Tsakiya da na yankin gulf ne, ƙasashen da Iran ta zarga da taimaka wa Amurka a hare-haren da take kai mata.
Sharaɗin Iran: Za ta riƙa lura da ilahirin mashigar da zirga-zirgar jigaren da ke bi ta ciki.
Sharaɗin Amurka: Iran ta sake buɗe mashigar ba tare da sanya idanu kan zirga-zirgar jiragen da ke bi ta wurin ba.
Shirin nukiliyar Iran
Wannan na ɗaya daga cikin batutuwan da suka haddasa rashin jituwa tsakanin Iran da Isra'ila da kuma Amurka.
Duka ƙasashen sun saka sharaɗi a kansa dangane da kawo ƙarshen yaƙin.
Sharaɗin Iran: Iran ta buƙaci damar ci gaba da inganta sinadarin yureniyom (uranium) zuwa wani mataki, tare da kawo ƙarshen sharuɗan hukumar sanya ido kan makamashin nukiliya (IAEA) kan shirin nukiliyarta.
Sharaɗin Amurka: Amurka ta buƙaci Iran ta haƙura kacokan da burinta na ci gaba da inganta sinadarin da kuma shirinta na nukiliya.
Ƙungiyoyin da ke goyon bayan Iran
Tun bayan fara yaƙin, ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon ta fara kai hare-hare cikin Isra'ila, yayin da ita ma Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare a birnin Beirut.
Baya ga Hezbollah, wata ƙungiyar da ke samun goyon bayan Iran da ta so shiga yaƙin ita ce ƙungiyar ƴantawayen Houthi da ke Yemen.
Sharaɗin Iran: Iran ta buƙaci Amurka da Isra'ila su daina kai wa waɗannan ƙungiyoyi hare-hare.
Sharaɗin Amurka: Iran da daina ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ta hanyar ba su kuɗaɗe da kayan aiki.
Taƙaita sojoji
Batun takaita yawan soji a yankin na daga cikin abubuwan da ɓangarorin biyu suka ci karo da juna dangane da kawo ƙarshen yaƙin.
Sharaɗin Iran: Iran na son Amurka ta bayar da tabbacin cewa ba za ta ƙara kai mata hari ba, sannan ta janye ilahirin dakarunta daga yankin Gulf da yankin Gabas ta Tsakiya.
Sharaɗin Amurka: Amurka na son Iran ta taƙaita ƙarfin sojinta.
Diyya da takunkumai
Wani abu da sharuɗan ɓangarorin biyu ke cin karo da juna a wannan yarjejeniyar shi ne biyan diyya da batun takunkuman da aka sanya wa Iran.
Ƙasar Iran ta jima tana fuskantar jerin takunkuman tattalin arziƙi a duniya sakamakon shirinta na nukiliya.
Sannan kuma wannan yaƙi ya haifar mata da ɓarna mai yawan gaske.
Sharaɗin Iran: A ɗage mata duka takunkuman da aka sanya mata, sannan a biya ta diyyar ɓarnar da aka yi mata a wannan yaƙi.
Sharaɗin Amurka: Amurka ba ta nuna muradin hakan ba, sai dai Shugaba Trump ya nuna cewa zai iya ɗage wa Iran ɗin takunkuman nata.











